Me ya sa kashe-kashen ta'addanci ke ƙaruwa a Najeriya da Nijar?

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya ce ta shida yayin da Jamhuriyar Nijar ta zo a matsayi na biyar cikin jerin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta'addanaci a duniya, kamar yadda rahoton ayyukan ta'addanci na duniya na shekarar 2025 ya nuna.
Rahoton ya yi nazari ne kan ƙsashe 136, bisa la'akari da abubuwa kamar yawan hare-haren da ka kai, da waɗanda hare-haren suka rutsa da su da kuma mutanen da aka yi garkuwa da su.
Rahoton, wanda cibiyar zaman lafiya da tattalin arziƙi ta duniya ta fitar a ranar 5 ga watan Mayu ya nuna cewa Najeriya ta samu ci baya daga matsayi na takwas da take a rahoton da aka fitar cikin shekarun 2024 da 2023.
Najeriya ta zo ta shida ne bayan Jamhuriyar Nijar da ake a matsayi na biyar, Mali a matsayi na huɗu, Syria a matsayi na uku, Pakistan a matsayi na biyu, sai Burkina Faso a matsayi na ɗaya.
Rahoton na wannan karo ya nuna cewa a Najeriya an samu kashe-kashe masu alaƙa da ta'addanci guda 565 a shekarar 2024, wanda hakan ya zarce na shekaru biyu da suka gabata.
Wannan na zuwa ne duk kuwa da cewa rahoton ya nuna cewa an samu raguwar kashe-kashen ta'addanci a duniya cikin shekarar ta 2024.
Najeriya ta daɗe tana fama da hare-hare na ta'addanci, musamman daga mayaƙan ƙungiyar Boko Haram, wadda ta shafe sama da shekara 10 tana gudanar da ayyukanta a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Duk da cewa an raunana ƙungiyar sosai, amma a shekarar da ta gabata an ga farfaɗowar hare-harenta a yankunan jihar Borno, inda ta kai harin ƙunar baƙin wake a garin Gwoza, wanda ya yi ɓarnar da aka daɗe ba a gani ba.
Haka nan mayaƙan ƙungiyar sun kai farmaki da dama a kan sojoji da kuma kashe manoma da masunta a ƙauyuka, lamarin da ya haifar da tsoro a zukatan al'umma.
Abin da rahoton ya ce kan yankin Sahel

Asalin hoton, Boko Haram
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rahoton ya nuna cewa a karo na biyu, Sahel ne yankin da ya fi kowane a duniya fama da hare-haren ta'addanci.
Yankin ne ya samu fiye da rabi na adadin mutanen da aka kashe ta hanyar hare-haren ta'addanci a faɗin duniya, kamar yadda rahoton ta bayyana.
Rahoton ya nuna cewa biyar da cikin ƙasashe 10 da ta'addanci ya fi yi wa katutu a duniya suna a Sahel ne - makekekn yanki mai rairaiyi wanda ya tashi daga tekun Atlantika a yammacin Afirka zuwa Tekun Maliya da ke gabashin nahiyar.
Ƙasashen Burkin Faso, wadda ta zo ta ɗaya a jerin, da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar su ne waɗanda suka fi shan wahala.
Rikicin masu tayar da ƙayar baya da ya ɓarke a Mali, shekaru 10 da suka gabata ya yadu zuwa Burkin Faso da Jamhuriyar Nijar masu maƙwaftaka.
Manyan ƙungiyo biyu da ake ɗora wa laifin kai hare-haren su ne IS da kuma wata ƙungiya mai alaƙa da Alqaeda a ƙasar Mali.
Rahoton ya nuna cewa cibiyar hare-haren ta'addanci ta tashi daga Gabas ta tsakiya zuwa yankin Sahel na nahiyar Afirka.
Duk da cewa yawan mutanen da aka kashe sanadiyyar hare-haren ta'addanci ya ƙaru a Najeriya a 2024, amma ƙasar na daga cikin waɗanda aka fi samun raguwar irin waɗannan kashe-kashe a tsawon shekaru.
A 2014 ne aka samu irin waɗannan kashe-kashe mafi yawa a ƙasar, inda aka kashe mutum 2,101 sanadiyyar hare-haren ta'addanci, inda kuma yawan ya yi ƙasa sosai zuwa kashe-kashe 392 a 2022, wanda shi ne mafi ƙaranci tun daga 2011.
Sai dai irin waɗannan kashe-kashe sun ƙaru da kashi 34 cikin ɗari a 2023, inda aka kashe mutum 533, sai kuma ya ƙaru zuwa 565 a 2024.
Ƙasashe 10 da ta'addanci ya fi yi wa illa
Burkina Faso ce ta zamo ta farko a jerin cikin shekara biyu a jere:
1 - Burkina Faso
2 - Pakistan
3 - Syria
4 - Mali
5 - Jamhuriyar Nijar
6 - Najeriya
7 - Somaliya
8 - Isra'ila
9 - Afghanistan
10 - Kamaru
Rahoton na ƙasashen da ta'addanci ya fi shafa ya ce ƙasashen da aka fi samun ƙaruwar kashe-kashe masu alaƙa da ta'addanci tun daga 2007 su ne Pakistan da Syria da kuma Mali.
Iraqi kuma ita ce ƙasar da aka fi samun raguwar irin waɗannan kashe-kashe, inda ya ragu da kashi 99 cikin ɗari daga shekarar 2007, inda aka samu kisan mutane 6,249 zuwa 59 a 2024.
Ƙasashen Afghanistan da kuma Thailand na cikin jerin ƙasashen waɗanda suka samu raguwar kashe-kashe sanadiyyar ta'addanci.











