Ina ne 'Timbuktu Triangle' kuma me ya sa ya zama maɓoyar Boko Haram?

Asalin hoton, Getty Images
Kashe sojojin Najeriya sama da 22 da mayaƙan Boko Haram suka yi a ƙarshen mako a dajin Timbuktu Triangle ya ɗaga hankalin mutane, ganin yadda aka yi asarar sojoji masu yawa a lokaci guda.
Tun a ƙarshe-ƙarshen shekarar da ta gabata ne hare-haren mayaƙan Boko Haram suka fara komawa a yankin arewa maso gabas, wanda ya daɗe yana fama da matsalar tsaro, musamman rikicin Boko Haram.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran shalkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar ranar Lahadi, ya ce, an kashe sojojin ne a lokacin da suka suka ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin mayaƙan ƙungiyar da ke yankin na Timbuktu.
Sai dai ya ƙara da cewa sojojin sun samu nasarar kashe mayaƙan ƙungiyar 70, ciki har da wasu manyan kwamandojinsu guda uku.
Wannan kashe sojojin ya sa sunan yankin na Timbuktu ya yi amo a bakunan mutane, inda wasu ke tambayar ina ne, kuma me ya sa ƴan Boko Haram suke ɓuya a ciki?
A baya dai an fi ambaton dajin Sambisa a matsayin maɓoyar ƴan Boko Haram, inda ba a cika maganar Timbuktu Triangle ba.
Wannan ya sa BBC ta yi nazari kan ina ne wannan wuri, kuma mene ne ya sa ya zama maɓoyar mayaƙan?
A ina Timbuktu Triangle yake?
Tun farkon yaƙin Boko Haram, wuraren da Boko Haram suka fi ɓuya sun haɗa da Timbuktu Triangle da Sambisa da tsaunin Mandara da tafkin Chadi.
Timbuktu Triangle ya ratsa ƙananan hukumomin Damboa, da Jere, da Kaga, da Konduga a jihar Borno da ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Game da asalin wurin, Baritsa Audu Bulama Bukarti, mai bincike kan harkokin tsaro a yankin Sahel, ya ce mayaƙan Boko Haram ne suka sanya wa dajin suna Timbuktu.
"Kuma wataƙila sanya sunan na da alaƙa da tarihin asalin Timbuktu na ƙasar Mali wanda aka sani a tarihi a matsayin cibiyar karatun addinin musulunci, kuma manyan malamai sun zauna musamman ƙarƙashin daular Songhai."
Bukarti ya ce sojojin ne da suka lura dajin yana da kusurwa uku, sai suka ƙara 'triangle', sai sunan ya koma 'Timbuktu Triangle'.
Me ya sa ya zama maɓoyar Boko Haram?
A game da dalilin da ya sa ƴan Boko Haram suke samun mafaka a dajin, Barista Bulama ya ce dajin ya tattara dukkan abin da ake buƙata domin yaƙin sunƙuru da ma rayuwa.
"Bayan ƙananan hukumomin da dajin ya bi, ba shi da nisa da garin Biu da Damaturu da Gujiba da Gwoza da wasu manyan garuruwan. Ke nan duk wanda ya kama dajin, zai samu sauƙin isa ko samun iko da waɗannan wuraren," in ji shi.
Ya ce muhimmancin wurin ne ya sa suka ɓullo da dabarun hana sojoji fatattakarsu.
"Dabarun sun haɗa da toshe duk hanyoyin da za a shiga dajin. Kuma a cikin dajin akwai gidajensu da kasuwa da wurin samun horo da ma kotu da sauran abubuwan da suke buƙata."
Ya ƙara da cewa daji ne da yake da duhu, ga dogayen ciyayi ga ruwa ga kuma fili mai faɗi tamkar sahara, "wato duk yanayin da ake buƙata akwai.
"Shi ya sa ake ɗauki ba daɗi tsakanin sojoji da mayaƙan Boko Haram tsawon shekaru saboda kowa na son yin iko da dajin."
Me ya hana a kori Boko Haram daga dajin?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanin harkokin tsaron ya ce tun daga wuraren 2011 ne ƴan Boko Haram suka yi sansani a dajin, inda ya ƙara da cewa an dai fi sanin dajin Sambisa ne.
"An fi sanin Sambisa ne, wataƙila saboda ya fi suna da girma, kuma sun taɓa komawa kusan suka tare a Sambisa, amma shi ma Timbuktu yana da muhimmanci. Amma an taɓa taɓa fatattakarsu, daga baya da sojoji suka ja baya, sai suka koma.
Bukarti ya ce lokacin da Boko Haram ta rabu biyu, ɓangaren Shekaru ne ke dajin Timbuktu, "amma kimanin shekara 5 da suka wuce bayan ya mutu, sai ya zama tsagin ISWAP ne ke riƙe da dajin," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa sojoji suna ƙoƙari sosai domin ƙwace iko da dajin.
Sai dai ya ce ya na da wahala sojoji su mamaye wurin domin ya na da girma da zai buƙaci dubban sojoji, "sannan idan ka mamaye gurin za su iya komawa dutsen Mandara ko Sambisa ko Tumbus, kuma sojojin ba su da yawa sosai, kuma ana buƙatar aikinsu a wasu wuraren."
Ya ce dajin ya fita daga ɓangaren da sojojin haɗakar ƙasa da ƙasa suke aiki, domin a cewarsa, sun fi mayar da hankali a kan bakin iyakoki, "shi kuma dajin Timbuktu ya fi nausawa cikin Maiduguri. Don haka sojojin Najeriya ne suke aiki a yankin."
Ya ce kamata ya yi idan sojoji sun ƙwace wuri, a kawo ƴansanda su mamaye yankin, sannan ya ƙara da cewa, "mafita ɗaya ita ce idan aka shiga dajin, kada a tsaya, sannan a musu ƙawanya ta dukkan mashigogin dajin."










