Yadda ake amfani da sojojin haya na Amurka wurin kashe-kashe a Yemen

Asalin hoton, Jack Garland/BBC
- Marubuci, Nawal al-Maghafi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic Investigations
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta ɗauki nauyin kisan mutane da ke da alaƙa da siyasa a Yemen, kamar yadda wani binciken da BBC ta yi ya gano.
Lamarin da ya ƙara dagula rikici tsakanin gwamnatin Yemen da masu adawa da ita, rikicin da ya ja hankalin duniya a yankin Bahar Maliya.
Horon yaƙi da ta'addancin da sojojin hayan Amurka suka bai wa jami'an Daular Larabawar a Yemen, ana amfani da shi wajen horar da wasu ƴan ƙasar ta Yemen waɗanda za su iya aiki da shi ba tare da sun tayar da ƙura ba - abun da ya ƙara yawan kashe-kashen siyasa matuƙa, kamar yadda wani mai kwarmata bayanan sirri ya shaida wa binciken da sashen Arabic na BBC.
Haka kuma BBC ta gano cewa duk da cewa sojin hayan na Amurka sun ce manufar ita ce kakkaɓe masu iƙirarin jihadi da mayaƙan al-Qaeda (IS) da ke kudancin Yemen, sai dai UAE ta ɗauki tsoffin mayaƙan al-Qaeda a matsayin jami'an tsaro da ta ajiye a Yemen don yaƙi da mayaƙan Houthi da sauran masu ɗauke da makamai.
Gwamnatin haɗaɗɗiyar Daular Larabawar ta musanta duka zargi da ke ƙunshe a binciken na BBC, na cewa ta sa an kashe waɗanda ba su da alaƙa da ta'addanci - tana cewa zargin "ba shi da tushe bare makama."
Kashe-kashen da aka yi a Yemen - mutum fiye da 100 da aka kashe a cikin shekara uku - abu ɗaya ne cikin mummunan rikicin da ke gara kan ƙasashen ƙetare masu ƙarfin faɗa a ji a ƙasar da ta fi kowacce talauci a yankin Gabas Ta Tsakiya.
Mummunan yanayin da ake ciki ya sa an gaza mayar da gwamnatin dindindin da ƙasashen wajen suka amince da ita a Yemen.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lamarin da za a iya cewa ya taimaka wajen ƙara wa ƙungiyar Houthi da ke samun goyon bayan Iran ƙwarin guiwa - wadda a yanzu ake bayar da rahotannin kai hare-harenta kan jiragen ruwa a Bahar Maliya.
A baya-bayan nan, Amurka ta ce za ta sanya ƙungiyar cikin "ƴan ta'adda na duniya."
Tun a 2014 wakiliyar BBC ke aiko da rahotanni kan yaƙin Yemen.
Yaƙin ya janyo gwamnatin ta rasa iko da arewacin ƙasar wanda ya faɗa hannun ƴan Houthi - ƙungiyar da a cikin shekaru ta ƙara ƙwarewa da samun kayan aiki.
A shekarar 2015, Amurka da Burtaniya sun tallafa wa dakarun hadin guiwar da Saudiyya ke jagoranta, rundunar da mafiya yawanta ƙasashen larabawa ne, Kuma UAE wata ƙusa ce a tafiyar.
Rundunar ta abka wa Yemen da zummar mayar da gwamnatin da aka tilasta wa gudun hijra kan mulki kuma ta yaƙi ta'addanci.
An bai wa UAE kula da batun tsaro a kudancin ƙasar kuma ta kasance wata babbar ƙawar Amurka wajen yaƙi da ta'addanci a yankin da tuni al-Qaeda ta daɗe a kudancin kuma tana ƙara faɗaɗa wuraren da ke ƙarƙashin ikonta.
Rikicin Yemen
- A shekarar 2014, ƴan tawayen Houthi, wani reshen mabiya ɗariƙar Shi'a marasa rinjaye suka ƙwace iko da babban birnin ƙasar, Sanaa
- Shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi ya kafa babban birni na wucin-gadi a birnin Aden da ke kudanci, bayan ya tsere wa ɗaurin talalar da aka yi masa a Sanaa a watan Fabairun 2015
- Saudiyya da wasu ƙasashe takwas, waɗanda galibinsu ƴan sunni ne suka fara kai hari ta sama kan ƴan Houthi, waɗanda suka yi ikirarin cewa abokiyar gabarsu, ƙasar Iran na taimaka musu da makamai. Rundunar ta samu tallafin kayan aiki daga Amurka da Burtaniya da kuma Faransa
- An dinga samun fafatawa a tsakanin waɗanda ma suke ganin suna ɓangare guda. A shekarar 2019 faɗa ya ɓarke tsakanin dakarun gwamnati da Saudiyya ke goya wa baya da ƙungiyar ƴan’aware ta (STC) da ke kudanci, waɗanda suke zargin shugaba Hadi da aikata ba daidai ba da kuma alaƙa da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin musulunci.
- Mayaƙan ƙungiyar al-Qaeda a yankin Larabawa (AQAP) da kuma ƙungiya mai alaƙa da abokiyar gabarta ta (IS) sun ribaci yanayin da aka shiga, inda suka kwace yankuna a kudancin Yemen, kuma suke kai munanan hare-hare, musamman kan Aden.
- Houthi ta ƙara faɗaɗa tasirinta - a watan Nuwamban 2023 ta fara kai hare-hare kan jiragen ruwa na ƙasashen duniya da ke bi ta Bahar Maliya.
Sai dai maimakon mayar da zaman lafiya da kuma faɗaɗa hakan, a lokacin da wakiliyar BBC ke bayar da rahotanni ta lura da kashe-kashen da ake yi na ɗaiɗaikun mutane a yankin kudancin ƙasar da ke ƙarƙashin ikon gwamnati, kisan mutanen da ba su da wata alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci.
A ƙarƙashin dokar ƙasa-da-ƙasa kisan farar hula ba tare da bin hanyoyin da doka ta amince da su ba, ana ɗaukar sa a matsayin kisan gilla.
Mafiya yawan waɗanda aka kashen ƴan ƙungiyar Islah ne - wani reshe na ƙungiyar Muslim Brotherhood a Yemen.
Ƙungiya ce ta ƴan Sunni da aka sani a duniya, kuma Amurka ba ta taɓa sanya ta cikin ƙungiyoyin ƴan ta'adda ba, amma Ƙasashen larabawa da dama sun haramta ta - ciki har da haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, inda gidan sarautar ƙasar ke kallon ayyukan siyasarsu a ƙasar a matsayin wata barazana ga mulkinsu.
Wani hoton jirgi marar matuƙi da aka kwarmata na kisan da farko da aka fara yi shi ya kai ga fara wannan binciken kisan da ba a san dalilin yin sa ba.
Yana ɗauke da kwanan watan Disamba 2015 kuma an bi diddiginsa, inda ya samo asali daga wani kamfanin tsaron Amurka mai suna Spear Operations Group.
Daga ƙarshe BBC ta samu ganawa da daya daga cikin mutanen da suka yi aikin da ke cikin hoton a wani gidan cin abinci a birnin London a 2020.
Isaac Gilmore, wani tsohon sojin ruwan Amurka ne wanda daga bisani ya zama shugaban ɓangaren aikace-aikace na Spear, wanda kuma ya ce yana daga cikin Amurkawa da dama da UAE ta yi haya su aikata kisan a Yemen.

Asalin hoton, Jack Garland/BBC
Ya ƙi yarda ya yi magana kan waɗanda ke cikin jerin sunayen mutanen da UAE ta bai wa kamfanin na Spear don a kashe su - sai mutum na farko da suka fara kashewa: Ansaf Mayo, wani ɗan majalisa a Yemen kuma shugaban ƙungiyar Islah da ke birnin Aden a kudancin ƙasar, kuma babban birnin ƙasar na wucin-gadi tun shekarar 2015.
Na ƙalubalanci Mista Gilmore kan cewa amma hukumomin Amurka ba su taɓa sanya Islah cikin ƙungiyoyin ƴan ta'adda ba.
"Yaƙe-yaƙe na zamani suna da wuyar sha'ani," In ji shi. "Mun ga haka a Yemen - Mutum ya zamo shugaba ne na farar hula kuma malami, amma ga wani shugaban ta'addanci ne."
Mista Gilmore, da wani ma'aikacin Spear a Yemen a wancan lokaci - Dale Comstock - ya shaida wa BBC cewa ayyukan da suka yi sun kawo ƙarshe a shekarar 2016.
Amma an ci gaba da kashe-kashen a kudancinYemen.
Hasali ma sun ƙara yawaita ne a cewar ƙungiyar kare haƙƙin bil-Adama.
Ƙungiyar ta yi bincike a kan kisa 160 da aka yi a Yemen daga 2015 zuwa 2018.
Ta ce mafiya yawansu an yi su ne daga shekarar 2016 kuma 23 daga cikin mutane 160 da aka kashe ke da alaƙa da ta'addanci.
Kuma dukkanin kashe-kashen an yi su ne ta irin hanyar da Spear ta bi - tayar da abubuwa masu fashewa don ɗauke hankali, kafin harbin wanda aka yi nufi.
Kisan da ke da alaƙa da siyasan da aka yi na baya-bayan nan a Yemen, a cewar lauyar kare haƙƙin bil-Adama a ƙasar, Huda al-Sarari, ya faru ne a watan jiya - an kashe wani limami a Lahj ta irin wannan hanyar.
Mista Gilmore da Mista Comstock da wasu sojoji biyu na kamfanin Spear da suka nemi a ɓoye sunayensu, sun ce kamfanin ya horar da jami'an tsaron UAE da ke Aden.
Wani ɗan jarida da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya ga hoton irin wannan horon.
Sojin hayan sun ƙi bayar da bayani kan abun da horon ya ƙunsa, amma wani babban sojin Yemen daga Aden, wanda ya yi aiki kai tsaye tare da UAE ya yi ƙarin haske.

A matsayinsu na sojin haya an san su sosai a Aden, kuma hakan za su iya kasancewa cikin hadari idan aka gan su, sai aka sauya abun da za su yi, ya koma horar da jami'an tsaron Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, su kuma sai su dinga horar da ƴan ƙasar ta Yemen "don su aikata kisan waɗanda ake so su kashe," a cewar jami'in sojin na Yemen.
A yayin wannan bincike wakiliyar BBC ta kuma zanta da wasu gwamman majiyoyi a ƙasar Yemen waɗanda suka ƙara jaddada faruwar hakan.
Ciki har da wasu mutane biyu waɗanda suka ce sun kashe wasu mutane da ba su da alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci, bayan sun samu horo daga sojojin UAE.
Sannan da wani mutum wanda ya ce an sako shi daga kurkukun UAE a madadin ya kashe wani babban ɗan siyasa a Yemen, tayin da ya ce bai amince ba.
Neman mutanen Yemen su aikata kisan na nufin zai yi wuya a alaƙanta kisan da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan.
A shekarar 2017, UAE ta taimaka wajen kafa wata rundunar tsaro, wadda ɓangare ce ta ƙungiyar (STC), da ke samun kuɗaɗe daga UAE, rundunar da ke aiki da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a fadin kudancin Yemen.
Rundunar tana zaman kanta kuma ba ta ɗaukar umarni daga kowa sai daga UAE. Ba kawai an horar da mayanƙanta a fagen yaƙi ba ne, tana da wani sashe na, the elite Counter Terrorism Unit, wanda aka horar da su don aikata kisan kai, mai kwarmaton ya shaida wa BBC.
Mai kwarmaton ya aiko da wata takarda mai ɗauke da sunayen tsoffin mayaƙan al-Qaeda 11, kuma a yanzu suna aiki da STC, BBC ta tabbatar da wasu daga cikinsu.
Haka kuma a yayin wannan bincike, an yi karo da sunan Nasser al-Shiba. Wani wanda ya taɓa zama babban ƙusa a al-Qaeda, an ɗaure shi kan ta'addanci, amma daga bisani aka sake shi.
Wani minista a gwamnatin Yemen wanda ya shaida wa BBC cewa al-Shiba sanannen wanda ake zargi ne da kai hari kan jirgin ƴakin Amurka USS Cole, lamarin da ya kai ga mutuwar sojojin ruwan Amurka 17 a watan Oktobar 2000.
Majiyoyi da dama sun gaya wa BBC cewa a yanzu shi ne kwamandan wasu sassan sojin ƙungiyar ta STC.
Lauya Huda al-Sarari tana bincike kan keta haƙƙin bil-Adama da sojojin da ke samun goyon bayan UAE suka aikata a Yemen. Ta sha samun barazanar kisa saboda aikinta, amma ɗanta mai shekara 18 ne ya rasa ransa a kan hakan.
An harbe shi a ƙirji a watan Maris 2019 a lokacin yana kan hanyar zuwa wani gidan mai, kuma ya mutu wata guda bayan hakan ta faru. Lokacin da Huda ta koma bakin aiki ta ce ta samu saƙonnin da ke gargaɗinta da ta daina. "Ɗa guda ɗaya bai ishe ki ba, kina son mu kashe sauran?" Suka ce mata.
Wani binciken da mai gabatar da ƙara na Aden ya yi daga baya, ya gano cewa wani ɗan ƙungiyar da ke samun goyon bayan UAE ne ya kashe Mohsen, sai dai ba a taɓa kama kowa da laifi ba.
Wasu jami'an ofishin ma su gabatar da ƙara - waɗanda ba za su iya ambata ba sun shaida muna cewa yawaitar kashe-kashen sun samar da wani yanani na ban-tsoro wanda ya kai su kansu suna tsoron gabatar da ƙara kan laifukan da suka shafi dakarun da ke samun goyon bayan UAE.
Mun tambayi wanda ya samar da Spear, Abraham Golan, kan ko sojojin hayarsa ya horar da ƴan UAE dubarun kisa, amma bai ce komi ba.
Mun taƙaita zarge-zargenmu ga gwamnatin Daular Larabawa.
Ta ce ba gaskiya ba ne cewa tana kama waɗanda ba su da alaƙa da ta'addanci. Kuma tana goyon bayan goyon baya ga gwamnatin Yemen.
"UAE ta kiyaye dokokin kasa da kasa a lokacin ayyukanta," a cewarta.
Mun tambayi ma'aikatar tsaron Amurka da ma'aikatar harakokin waje su yi magana game da ayyukan Spear amma ba su ce komi ba. Hukumar leƙen asirin Amurka a cikin wata sanarwa ta ce: Batun cewa CIA na da hannu ba gaskiya ba ne."







