Ƙananan hukumomin Borno da suka fi hatsari sanadiyyar Boko Haram

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A baya-bayan nan hare-haren Boko Haram da ISWAP sun ci gaba da addabar sassan jihar Borno, lamarin da ke ƙara dagula zaman lafiyar al'umma da kuma ƙoƙarin gwamnatin jihar na dawo da martabar yankunan da rikicin ya ɗaiɗaita.

Ƙananan hukumomi da dama waɗanda a baya suka kasance cike da hada-hada a yanzu sun koma wurare masu hatsari sanadiyyar hare-hare.

Mutanen yankunan da dama sun tsere zuwa wasu yankunan, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

A ranar Lahadi, gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya ce sama da mutum 20,000 sun yi ƙaura daga ƙaramar hukumar Marte bayan da mayaƙan Boko Haram suka tursasa wa ƙauyuka kimanin 300 tserewa.

Gwamnan ya bayyana cewa garin Marte wanda a kimanin shekaru huɗu da suka gabata aka samu nasarar mayar da al'ummarsa wadanda rikicin Boko Haram ya tarwatsa, yanzu ƙungiyar ta sake korar su a cikin kwana uku.

Sai dai ba Marte ne kawai ƙaramar hukumar da hare-haren Boko Haram na baya-bayan nan suka addaba ba.

A dalilin haka ne BBC ta tuntuɓi Dr Kabir Adamu, masani kan lamurran tsaro a yankin Sahel kuma shugaban kamfanin Beacon security and intelligence.

Waɗanne ƙananan hukumomi ne?

BBC ta tattaunada da masu nazari a kan tsaro ciki har da Dr. Kabir Adamu da kuma wani dan jarida, Adamu Aliyu Ngulde wadanda suka lissafo ƙananan hukumomin da suka fi fuskantar hare-haren Boko-Haram a shekarun baya-bayannan:

  • Bama – Dr Kabir ya bayyana Bama a matsayin wuri mafi tsanani da hare-haren Boko Haram suka taɓa a Borno. "Garin ya sha fama da mamaya da kuma ƙone-kone na dogon lokaci.
  • Marte: Wannan ce ƙaramar hukumar da ta ja hankalin al'umma a baya-bayan nan bayan gwamnan jihar Babagana Zuluma ya nuna fargaba kan cewa za ta iya faɗawa hannun Boko Haram. Zulum ya ce mayaƙan Boko Haram sun tayar da sama da ƙauyuka 300 na ƙaramar hukumar.
  • Konduga – "Yana ɗaya daga cikin wuraren da hare-haren Boko Haram suka yi ƙamari musamman a kasuwanni da wuraren ibada." in ji mai sharhin.
  • Gwoza – "Wannan shi ne garin da Boko Haram ta ayyana a matsayin hedkwatarta a shekarar 2014. Duk da ƙokarin sojoji, har yanzu akwai yankuna da ake tsoron shiga saboda matsalolin tsaro."
  • Dikwa – Yanzu haka wannan ƙaramar hukumar ita ce ta zama mafakar 'yan gudun hijira daga Marte da sauran garuruwa, in ji Dr Kabir.
  • Askira Uba – Mai sharhin ya ce wannan yankin tsaunuka na fuskantar matsin lamba daga 'yan Boko Haram da ke amfani da yanayin dazuka wajen kai hari da guduwa.
  • Damboa – Kabir Adamu ya bayyana cewa Damboa na daya daga cikin wuraren da sojoji ke yawan fafatawa da masu tayar da ƙayar baya, musamman a hanyoyin da ke kai wa yankin.
  • Mafa – "Saboda kasancewarta a tsakiyar hanya tsakanin Maiduguri da Dikwa, Mafa na fama da farmaki daga ƴan Boko- Haram ɗin in ji Dr Kabir.
  • Jere – Dr Kabir ya ƙara da cewa "Yana kusa da birnin Maiduguri, Jere na fuskantar barazana daga hare-haren bam da na kwanton-bauna."

Ana kallon hare-haren na Boko Haram da suka dawo a baya-bayan nan a amatsayin koma-baya ga yaƙin da hukumomin Najeriya suka kwashe shekara 10 suna yi da mayaƙanta.