Ƙananan hukumomin da suka yi sulhu da ƴanbindiga a Najeriya

Tsaro

Asalin hoton, @DanKatsina50

Lokacin karatu: Minti 4

Matsalar ƴanbindiga, wadda ta daɗe tana addabar wasu jihohin arewacin Najeriya na ci gaba da zama barazana ga rayukan al'umma, a daidai lokacin da masana suke ta tafka muhawara kan ko sasanci da masu tayar da ƙayar bayan ne zai kawo ƙarshen matsalar.

Tuni dai wasu ƙananan hukumomi suka shiga yarjejeniya tare da ayyana sasanci da ƴanbindiga da ke addabar yankunan su, lamarin da ya zo a daidai lokacin da wasu jihohi ke ƙara dagewa kai da fata cewa babu batun sulhu da ƴanbindiga da sauran masu aikata laifi.

A kwanakin baya ne dai sabuwar cacar-baki ta kunno kai tsakanin Nasir El-Rufa'i da gwamnatin tarayya bayan tsohon gwamnan ya caccaki gwamnatin tare da zargin ta da ta'azzara matsalolin tsaro ta hanyar "ƙarfafa ƴanbindiga" maimakon ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya a sassan ƙasar, inda ya yi zargin cewa gwamnatin na taimakon ƴanbindigar ta hanyar ba su maƙudan kuɗaɗe ta bayan fage.

Katsina na cikin jihohin da matsalar ta daɗe barazana da ƴan jihar, tare da maƙwabciyarta ta Zamfara da Sokoto da Kaduna da Neja, kuma ƙananan hukumomi da dama na jihar sun shiga sasanci da ƴanbindigar.

Sai dai har yanzu wasu na ganin sasancin ganganci ne, duk da cewa mazauna yankunan da aka yi sasanci suna bayyana farin cikin su kan zaman lafiya da suka ce sun fara samu.

Ƙananan hukumomi da aka yi sasanci a Najeriya

Domin jin ƙananan hukumomin Najeriya da suka shiga yarjejeniyar sasanci da ƴanbindiga a Najeriya, BBC ta tuntuɓi Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting, inda ya ce akwai ƙananan hukumomi guda tara - ɗaya a Kaduna sai guda takwas a jihar Katsina da suka daddale a hukumance cewa sun shiga sasancin kamar haka

  • Birnin Gwari - Jihar Kaduna
  • Jibiya - Jihar Katsina
  • Ɓatsari - Jihar Katsina
  • Safana - Jihar Katsina
  • Kurfi - Jihar Katsina
  • Faskari - Jihar Katsina
  • Ɗanmusa - Jihar Katsina
  • Musawa - Jihar Katsina
  • Ƙankara - Jihar Katsina

Masanin tsaron ya ƙara da cewa akwai wasu ƙananan hukumomin da ma wasu garuruwan da suka shiga sasanci, waɗanda a cewarsa ba a tabbatar da hakan a hukumance ba.

Sasancin na aiki?

A game da shin ko ana samun nasara a dalilin sasancin ko akasin haka, shugaban na kamfanin Beacon ya ce ana samun sauƙi, amma a cewarsa, "na wani ɗan lokaci ne kuma akwai sauran rina a kaba."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Idan ka duba ƙaramar hukumar Birnin Gwari, kusan shekara ɗaya ke nan ba mu ga masatalar ba kamar yadda muke gani a baya. A da ko da rakiyar jami'an tsaro ana kai hari, amma yanzu ana iya bin hanyar zuwa Birnin Gwari, kuma an buɗe kasuwanni ana cinikayya, sannan manoma sun koma gonaki, don haka idan dai don biyan buƙata ne na wani ɗan wani lokaci, lallai za a iya ce an samu."

Sai dai ya ce inda matsalar take ita ce, "mu masana muna tunanin abin da zai biyo baya ne, matakan da ya kamata a ɗauka na rage aibin da ke tattare da wannan sasanci, gaskiya ba mu ga an ɗauka ba. Yana iya yiwuwa a samu sauƙi na ɗan lokaci, amma matsala ta dawo a gaba."

Dr Kabiru ya ce yawaitar sasanci na iya halasta aikata laifuka, domin a cewarsa, "wasu za su ga cewa idan ba makami suka ɗauka ba, ba za a saurare su ba, wannan kuma hatsari ne ga ƙasa. Na biyu kuma ganin cewa masu laifi ne ake wa alfarma, wanda aka yi wa laifin kuma ba sa samun alfarma," in ji shi, wanda ya ce hakan matsala ce.

Inganta sasancin

A game da yadda sasancin ke ci gaba, Dr Kabiru ya ce abu ne mai kyau, amma dole sai an yi abubuwan da suka dace.

"Sasanci da masu tayar da ƙayar baya abu ne da ke da ƙa'ida, kuma dole a bi ƙa'idar domin samun nasara. A ciki akwai tabbatar da cewa an yi sasancin ne na dindidin. To matsalar yanbindiga ita ce ba a dunƙule suke ba, musamman wajen shugabanci. Babu shugaba ɗaya wanda iyan ya yi magana kowa zai bi."

"Na biyu wane mataki za a ɗauka wajen tabbatar da cewa an yi wajen ladabtar da waɗanda suka yi laifuka a cikin su""

Ya ce idan ba haka aka yi ba, "zai zama an halasta laifi, kuma dole ne a nuna cewa duk wanda ya aikata laifi, ya yi wa ƙasa laifi ne kuma dole za a hukunta shi.

Ya ƙara da cewa dole ne a tabbatar da cewa ƙungiyoyin baki ɗaya ne za a yi sasancin da su, "sannan a duk faɗin ƙasar. Kuma idan ana so a yi haka, dole a fitar da tsarin da muke kira 'framework' na hana laifuka na ƴanbindiga, idan ba haka ba, kowace jiha ko ƙaramar hukuma za ta yi abin da take so ne, amma kuma za su iya komawa wasu wuraren su cigaba da aikata laifi."