Abun mamaki bakwai da suka faru lokacin haihuwar Annabi Muhammad (SAW)

Asalin hoton, Getty Images
A rana irin ta yau ta 12 ga watan Rabi'ul Awwal a duk shekara ne miliyoyin Musulmi a faɗin duniya ke bikin murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Bisa maganganu mafi rinjaye, an haifi Annabin Muhammad (SAW) ne ranar Litinin a shekarar 570 a birnin Makka da ke Saudiyya.
Annabi Muhammad (SAW) ya kasance ɗa ga, Aminatu bint Wahb da Abdullahi bin Al-Mutallib, tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su.
Mahaifin Manzon Allah, Abdullahi ya rasu tun kafin a haifi manzon tsira.
Ita ma Aminatu ta rasu a shekarar 675, shekaru biyar bayan haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).
Albarkacin zagowar ranar Mauludi, BBC ta tuntuɓi Malam Nazifi Alƙarmawi da Malam Bashir Sheikh Tijjani Zangon Barebari dangane da abubuwan al'ajabi da suka faru a lokacin haihuwar fiyayyen halitta.
1) Tsagewar katangar Kisra
Malam Nazifi ya ce yana ɗaya daga cikin abubuwan al'ajabi da aka gani tun annabi yana cikin mahaifiyarsa.
"Lokacin da yana ciki a kwai abubuwa da dama da suka faru. Misali katangar masarautar Kisra da ba a taɓa tunanin wani abu zai rusa shi ba idan ba tashin alƙiyama ba amma sai ga shi ginin duk ya daddare sakamakon ɗaukar cikin fiyayyen halitta." In ji Malam Zangon Barebari.
2) Aminatu (SA) ba ta yi naƙuda ba
Sheikh Nazifi Al-ƙarmawi ya ce yana daga cikin mu'ujizar haihuwar fiyayyen halitta rashin naƙudar da Aminatu ta yi wanda ya bai wa al'umma mamaki kasancewa duk wata wahala da mace mai juna biyu ke fuskanta.
3) Haske ya bayyana
Sheikh Nazifi ya ce mahaifiyar annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ta ce lokacin da ta haihu ta ga wani haske da ya haska mata duk wani lungu da saƙo na wurin da take.
"Hasken nan ya haska mata har ta hango wasu biranen duniya da suka haɗa da Basra da Sham, yayin da ita kuma take a birnin Makka saboda ƙarfin abin da ya fito da shi na haske."
4) Halartar annabawa da mala'iku
"Yana ɗaya daga cikin mu'ujuzozin haihuwar annabo Muhammad (SAW) yadda mala'iku da annabawa da matan aljanna suka hallara domin karɓar haihuwar fiyayyen halitta.
Domin kafin haihuwar, Nana Aminatu ta ga wasu mata guda uku sun zo wurinta sai ta tambaye su ku kuma su wane ne sai suka ce mata mun zo tarbar fiyayyen halitta da za ki haifa ne. Sai ta ƙara tambayar su ku su wane ne? Sai suka ce ni ce Asiya matar Fir'auna da Maryam uwar annabi Isa. Waɗannan kuma matan aljanna ne." In ji Sheikh Nazifi.
5) Annabi ya yi sujjada
Sheikh Nazifi ya ƙara da cewa wani abun mamaki dangane da haihuwar annabin tsira shi ne yadda daga zuwansa duniya, sai ya sa goshinsa a ƙasa domin yin sujjada.
"Yana fitowa duniya kawai sai aka ga ya sa goshinsa a ƙasa yana sujjada. Sai da ya yi sujjada guda biyu yana faɗin Allahu Akbar sai ya yi sallama. Sayyada Amina ta ce ya ɗaga hannayensa yana magana a hankali amma ta ce ba ta san me yake faɗi ba. Daga nan kuma sai ya yi atishawa. Daga nan ne kuma sai ya kwanta ya yi kuka irin na jarirai."
6) An haifi annabi da askinsa
Sheikh Nazifi ya ƙara da cewa saɓanin yadda aka saba karɓar haihuwar jarirai, unguwar zomar ta tabbatar da cewa an haifi annabi a wanke.
"An haife shi a wanke kuma a shayance ba tare da wani wanzami ya ga tsiraicinsa ba. Sannan cibiyarsa ita ma a yanke"
7) Ya miƙe kafin ranar suna
Sheikh Al-Ƙarmawi ya ce tun kafin cikarsa kwana bakwai, fiyayyen halitta ya miƙe ya fara rarrafawa saɓanin abin da aka saba gani.
"Kan a ce ranar suna ta zo kamar yadda aka saba bisa al'ada, manzon tsira ya riga ya zauna ya fara rarrafawa ya kuma miƙe."
Yaushe aka fara Mauludi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sheikh Halliru Maraya wani malamin addinin Musulunci a Kaduna ya ce an fara maulidi ne tun hijira na da shekara 604, wanda ya fara yin sa shi ne Sarkin Erbil na wancan lokaci wato Mozaffar ad-Din.
Erbil a yau tana cikin Iraƙi, kuma babu a inda aka ambata a Ƙur'ani ko Hadisi ko kuma malamai su yi ijma'i a ce sai Annabi ya yi kaza ne abin ya zama halal.
Malamin ya ce, babban abin da za a yi la'akari da shi, shi ne Allah ya hana? Ko Annabi ya hana?
Sheikh Halliru Maraya, ya ce ƙur'ani ya ce abin da Manzon Allah ya kawo muku ku riƙa, haka abin da ya haneku ku guje masa.
Al'ummar Musulmai dai kan yi hidima a wannan lokaci, inda a kamar a Najeriya musamman a jihohin arewacin ƙasar, makarantun allo ko na Islamiyya kan shirya mauludi ta hanyar ƙayata waje a gayyaci manyan baƙi a zo a bai wa ɗalibai karatu da waƙoƙi na yabon Annabi su zo su rinƙa yi.
Wata al'ada kuma za ka ga a wannan rana a kan dafa abinci da nama musamman kaji a raba gida-gida na maƙwabta kamar ranar sallah.
A wani lokaci ma har ɗinki ake yi wa yara don su sanya sabon kaya kamar sallah.
Ga wasu mutanen kuma a kan shirya taron lakca inda za a gayyato malamai su yi wa'azi.










