Bayani kan iyalan da ke riƙe da rigar Annabi Muhammad a Turkiyya

Asalin hoton, AFP
Ɗaruruwan Musulmai ne ke taruwa a gaban wani daɗaɗɗen masallaci mai shekara 160, a kowanne watan Ramadan domin ganin abu mafi daraja ga Musulman duniya.
Wannan abu mai daraja shi ne, rigar Annabi Muhammad (SAW).
Ana kiran rigar da Hirka-i Sharif, wato riga mai tsarki. Kuma an adana wannan riga ce a masallaci mai tarihi da ke lardin Fatih na birnin Istanbul.
An kai rigar birnin Istanbul ne a ƙarni na 17, lokacin mulkin daular Usmaniyya, masarautar da ta mulki mafi akasarin ƙasashen Musulmai da suka haɗa da Saudiyya.
Mutane fiye da miliyan ɗaya ne ke ziyartar masallacin duke wata domin ganin wannan riga mai tsarki ta Annabi (SAW).
Iyalan da Annabi (SAW) ya bai wa rigar

Asalin hoton, AA
Wani labarin mai ban ta'ajibi da ke kama da na wannan masallaci, shi ne na zuri'ar da ke kula da wannan riga mai daraja, wato waɗanda ke da alhakin kula da rigar da kuma ba ta kariya.
Mutum na 59 a jerin zuri'ar gidan Aweys Qarni, shi ne ke wannan aikin a yanzu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Aweys Qarni wani babban malami ne, da ya yi rayuwa tare da Manzon Allah (SAW).
Zuri'ar gidan ta 13 ce ke riƙe da wannan matsayi, an kuma faro daga farko har zuwa kansu.
"Tun ina ɗan shekara uku zuwa huɗu, nake wannan masallaci.
"Na fahimci yadda danginmu ke alfahari da wannan masallaci kuma suke da ra'ayin barin masu ziyara zuwa cikinsa," In ji Baris Samir, mutum na 59 da ya gaji Aweys Qarni.
Mutumin, mai shekara 45, wanda ya yi karatu a fannin injiniya, ya shaida wa wakilin gidan talbijin na Turkiyya TRT cewa ya yi amannar ba kowanne dangi ba ne suke da tarihin tsatsonsu tun daga farko har zuwa zuri'a ta 59.
Annabi Muhammad (SAW) ya ba da kyautar wannan riga ce ga shehin malamin wanda ya yi yunƙurin zuwa ganin Manzon Allah (SAW) daga garinsu zuwa Madina a ƙarni na baƙwai.
Sai dai bai samu damar ƙarasawa ba, saboda daidai lokacin da ya kai Yemen, sai ya samu labarin mahaifiyarsa ba ta da lafiya.
Lamarin da ya tilasta masa koma wa garinsu, ba tare da ya yi ido biyu da Annabin Rahama (SAW) ba.
A lokacin da Manzon Allah (SAW) ya samu labarin yadda wannan shehin malami mai tsananin biyayya ga mahaifiyarsa ya koma gida, ba tare da ya haɗu da shi ba, sai ya ba da saƙon rigarsa mai launin zinare ta hannun sahabinsa Sayyidina Umar da Aliyu (RTA), don a kai masa kyauta.
Tun wannan lokaci ne, zuri'ar gidan Aweys Qarni ke riƙe da wannan riga mai launin zinare da daraja wadda Annabi Muhammad ya sanya a lokacin rayuwarsa.
Mufti Hasan Kamil Yilmaz ya ce Shiekh Al-Qarni bai haihu ba, saboda haka ƴan uwansa ne suka gaje shi.
Shin ta yaya rigar Manzon Allah ta je Istanbul?

Asalin hoton, AFP
A shekarar 1611, Sarkin Turkawa zamanin mulkin daular Usmaniyya, Ahmed 1, ya yi tunanin bin hanyoyin da zai ƙwace ikon mallakar rigar daga hannun zuri'ar Aweys Qarni, sai dai masu ba shi shawara da malamai sun faɗa masa cewa yin hakan ya saɓa wa ra'ayi da koyarwar Annabi (SAW).
Sai dai daga bisani ya yanke shawarar gayyatar iyalan domin komawa birnin Istanbul da zama.
Saboda haka an kai rigar mai tsarki da daraja Istanbul a zamanin sarki Ahmed na ɗaya daga Kusadasi da ke yankin Yammacin Turkiyya, kuma ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar zuri'ar Aweys Qarni.
"Tun daga lokacin ne rigar mai tsarki take birnin Istanbul," kamar yadda Yilmaz ya shaida wa AFP.
Daga ƙarshe a ƙarni na 18, shugaban Daular Usmaniyya, Abdulhamid na Daya ya yanke shawarar gina wannan babban masallaci mai alfarma, aka kuma sanya masa sunan da ake kiran rigar, a lardin Fatih.
Da farko ana ajiye rigar a wani ƙaramin ɗaki da aka keɓe.
"Wurin da ake adana rigar sai ya zama ba ya isar masu kai ziyara. A wannan lokaci ne, Sarki Abdulhamid ya ba da umarnin gina masallaci da kuma samar da ma'ajiyar rigar Hirka-i sharif mai tsarki a kusa da masallacin.
An kuma ci gaba da adana rigar a nan har cikin 1851," in ji Samir.
"Akwai makullin ɗakin da rigar take guda biyu, ɗaya yana hannun kwamitin masallacin, yayin da ɗayan yake wajen iyalan Aweys Qarni, in ji Muftin Istanbul.
Rigar ta ratsa zuri'a mai yawa, ma'ana ta kwashe shekaru a hannun iyalan da suka gaje ta, inda a yanzu haka Baris Samir ke shugabantar kula da rigar, kuma shi ne mutum na 59 da ya gaji wannan aiki.
"Aiki ne mai daraja.
"Muna tsananin farin ciki da muka samu kanmu cikin masu yin sa," Cewar Samir a zantawarsa da kamfanin dillacin labarai na AFP. "Aiki ne mai matukar buƙatar jajircewa a ɗabi'ance da kuma abin da ya shafi kuɗi."
Labari daga sashen BBC Somali.









