Kalaman da Putin ya yi kan Annabi Muhammadu sun tayar da ƙura a ƙasar India

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Prashant Sharma
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, World Service Disinformation Team
An sake yada wani tsohon kalami da shugaban Rasha Vladmir Putin ya yi kan Annabi Muhammad (SAW), a daidai lokacin da ake tsaka da danbarwa kan kyamar Musulunci a kasar Indiya.
Bai kamata a yi zagi ko batanci ga Annabi ba "domin hakan ba 'yancin yin addini ba ne kuma ya saba wa muradun Musulmai," a cewar Putin lokacin wani taron manema labarai da ya gudanar ranar 23 ga watan Disambar 2021, a cewar kamfanin TASS.
Sai dai ma'abota shafukan sada zumunta da mambobin jam'iyyar adawa ta Congress a Indiya, sun sake yada wannan sanarwar da Putin ya yi. Suna kuma ikirarin a yanzu ne ya yi tsokacin, a matsayin sukar matakin jam'iyyar BJP mai mulki.
An kuma sake wallafa tsokacin mara tushe bare makama a shafin Tuwita, wanda shugaban jam'iyar Congress a yankin Tamil Nadu da ke kudancin Indiya ya wallafa da kuma wani dan gidan sarautar Hadaddiyar Daular Larabawa, an kuma yada shi sama da 7000. Shafuka daban-daban na sada zumunta da ba a tantance su ba sun yada wannan batu.
Tsokaci na baya-bayan nan da wasu jiga-jigan jam'iyyar BJP mai mulki suka yi kan Annabi Muhammad (SAW) ya fusata Musulmin Indiya marasa rinjaye, lamarin da ya janyo zanga-zanga a wasu titunan kasar da tsamin huldar diflomasiyya tsakanin Indiya da gwamman kasashen Musulmai a yankin Asiya da Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Tsokacin na shugabannin jam'iyyar BJP, ya haskaka yadda ake samun karuwar tashin hankali mai alaka da addini a Indiya. Kalaman kiyayya ga mabiya addinin Musulunci sun karu a kasar tun bayan hawan jam'iyyar BJP mulki a shekarar 2014.
Shugaba Putin bai fitar da wata sanarwar mayar da martani kan tsokacin da BJP ta yi ga Annabi Muhammad (SAW) ba, kuma ba shi da alaka da tsokacin da aka yi a shekarar 2021, sannan ba shi da wata alaka da danbarwar da ke faruwa a halin yanzu, duk kuwa da ikirarin da ma'abota shafukan sada zumunta na kasashen Indiya da Gabas ta Tsakiya ke yi.
Putin ya yi kalaman na shekarar 2021 ne a wani bangare na taron manema labarai na shekara-shekara. Ya ce kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) na janyo karuwar tsattsauran ra'ayi da daukar fansa, inda ya yi kwatance da abin da mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta yi da abin da ya biyo baya.
Amma labaran karyar da aka yada sun hada da hoton Putin da Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud suka dauka tare, aka kuma wallafa bayanan da Putin ya yi a shekarar 2021 a kasan hoton da suka dauka. Amma binciken da BBC ta yi na gano ingancin hoton, ya nuna an dauke shi ne a shekarar 2019, lokacin da shugaban Rasha ya kai ziyara Saudiyya. Wannan hoton sam ba shi da wata alaka da kalaman Putin kan batancin da aka yi wa Annabi.

Asalin hoton, Alexander Zemlianichenko/POOL/AFP
Danbarwa
Tsohuwar kakakin jam'iyyar BJP, Nupur Sharma, ta yi wani tsokaci mai cike da ce-ce-ku-ce a kan Annabi Muhammad (SAW) a lokacin muhawarar da aka yi a gidan talbijin din Indiya makwanni biyu da suka gabata.
Wannan ya kara rura wutar rikici tsakanin Musulmai da mabiya addinin Hindu a kasar da kasashen ketare kamar Hadaddiyar Daular Larabawa, Iraki, Maldives, Jordan, Libya, da Bahrain.
Yayin da kasashen Kuwait, Iran da Qatar su kai kira ga jakadunsu kar su amince da hakan su dauki matakin rubuta korafi ga gwamnati, yayin da Saudiyya ta mayar da kakkausan martani kan hakan.
Jami'an Diflomasiyyar Indiya sun ce kalaman ba su da alaka da gwamnati.
A kuma ranar Lahadi, jam'iyyar BJP mai mulki ta dakatar da Ms Sharma daga cikinsu. Shi ma shugaban jam'iyyar reshen birnin Delhi, Naveen Kumar Jindal, an dakatar da shi daga bakin aiki sakamakon sake yada kalaman batancin da Ms Sharma ta yi a Tuwita.
Bayan dakatar da ita daga bakin aiki, Ms Sharma ta rubuta wata wasika a ciki ta fadi janye kalaman da ta yi, amma ta yi kokarin kare kanta, ta hanyar ikirarin mayar da martani ne kan yadda ake samun karuwar cin zarafi, da rashin girmamawa ga abin bautar mabiya addinin Hindu wato Lord Shiva.











