Mutanen da bai kamata su sha agwaluma ba

Asalin hoton, Getty Images
Agwaluma na daga cikin 'ya'yan itatuwa da suka shahara a yankunan Afirka, musamman a kasuwanni inda ake sayar da ita a lokacin zafi.
Yara da manya kan sha agwaluma saboda ɗanɗano mai tsami da zaƙi da kuma yadda take rage ƙishirwa.
Duk da yawan shansa mutane ke yi, masana lafiya sun ce akwai buƙatar a san ko jiki na iya ɗaukar ta kafin a mayar da ita abin sha na yau da kullum.
Masu nazarin abinci sun bayyana cewa duk wani abu da ake sha yana hulɗa da tsarin ciki da hanji, da sinadaran jiki.
Saboda haka abin da ya dace da wani zai iya cutar da wani.
A wata tattaunawa da ya yi da BBC, ƙwararre a harkar abinci Dr. Awwal Musa ya bayyana cewa akwai mutanen da bai kamata su sha agwaluma ba da suka haɗa da
- Masu ciwon ciki
- Masu gyambon ciki, wato ulcer,
- Wanda ransa ke a ɓace,
- Wanda ke jin yunwa."
A cewarsa, tsamin da ke cikinta na iya ƙara motsa zafin ciki wanda zai iya jawo ƙaiƙayi ga masu irin waɗannan matsaloli.
Likitan ya ƙara da cewa idan mutum yana fama da gyambon ciki ko kumburin hanji, shan agwaluma na iya tsananta wa.
Haka kuma wanda bai ci komai ba ya sha, yana iya jin zafi saboda tsamin na shiga kai tsaye cikin ciki da babu komai a ciki. Saboda haka ya ba da shawarar a rika sha ne bayan an ci abinci, kuma a lura da yadda jiki ke amsawa.
Wasu mutane kuma, musamman masu fama da matsalar zafin ƙirji da ƙwannafi,na iya jin tashin zuciya ko zafi a kirji bayan shan ta.
Irin waɗannan mutane ya kamata su rage ko su daina gaba ɗaya idan sun ji wata alama na mara daɗi.
Mene ne amfanin agwaluma a jikin ɗanadam?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da gargaɗin da ya yi, ƙwararren ya ce agwaluma na ɗauke da sinadaran gina jiki masu muhimmanci.
Ya bayyana cewa tana da wadataccen sinadarin Bitamin C (ascorbic acid) wanda ke ƙarfafa garkuwar jiki kuma yana taimakawa fata ta kasance cikin ƙoshin lafiyayya, kuma yana taimaka wa jiki wajen samar da collagen.
A cewarsa, bincike ya nuna cewa agwaluma na iya ƙunsar sinadarin bitamin C fiye da lemu ko gwaba.
Ya ce "agwaluma na kuma ɗauke da sinadarin fiber irin pectin wanda ke taimakawa wajen narkar da abinci, rage ƙullewar ciki, da kuma taimaka wa jiki wajen daidaita cholesterol."
Wannan fiber na kuma taimaka wa hanji ya yi aiki yadda ya kamata in ji ƙwararren.
ƙwararren ya ƙara da cewa agwaluma na ƙunshe da antioxidants kamar flavonoids da phenols waɗanda ke taimakawa yaƙi da lalacewar ƙwayoyin halitta a jiki.
Wadannan sinadarai na taimaka wa zuciya da jijiyoyin jini su kasance cikin ƙoshin lafiya, tare da rage haɗarin kamuwa da cututtuka masu ɗorewa.
Agwaluma in ji shi "na ɗauke da sinadarin calcium da potassium da iron da zinc.
"Potassium na taimaka wa zuciya da hawan jini, calcium na ƙarfafa ƙashi, yayin da iron ke taimakawa hana ƙarancin jini a jiki, Zinc kuma na tallafa wa garkuwar jiki da gyaran ƙwayoyin halitta." in ji shi.
Ƙwararren ya bayyana cewa agwaluma na ɗauke da sinadaran da ke rage kumburi a jiki, kuma suna taimakawa rage yawan kitse a jini.
Likitan abincin ya jaddada cewa agwaluma na da amfani idan an sha ta daidai gwargwado kuma ya ce ya kamata a sha agwaluma 2 zuwa 3 a rana.











