Sanya dogon wando, da sauran abin da ya kamata mace ta yi domin zuwa sallar asham

Shugabar mata ta hukumar Hisbah a jihar Kano, Malama Khadija Sagir
Bayanan hoto, Shugabar mata ta hukumar Hisbah a jihar Kano, Malama Khadija Sagir
Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da watan Ramadan ke ƙara nisa, al'ummar Musulmi na ci gaba da zage damtse wajen ibada domin cin gajiyar watan.

Ramadana wata ne da Musulmai kan dage wajen gudanar da ibada, inda baya ga ƙaurace wa ci da sha da sauran abubuwan da aka hana, mutane kan yi ƙoƙari wajen yin sallolin nafila da kuma sadaka.

Wasu daga cikin sallolin nafila da aka fi yi a cikin watan su ne sallar asham ko tarawi, da kuma wadda ake yi cikin tsakiyar dare a masallatai.

A irin wannan yanayi akan ga mata na tururuwan zuwa masallatai domin cin gajiyar alfanun da za su samu daga sallolin, kamar yadda addini ya tanada.

Malama Khadija Sagir, wadda ita ce shugabar mata ta hukumar Hisbah a jihar Kano da ke Najeriya ta ce: "Abu ne mai kyau mace ta fita ta yi sallar tahajjud a irin wannan lokaci mai tsada da kuma daraja".

Sai dai ta ce a bisa koyarwar addinin Musulunci yin sallah a gida shi ne abin da ya fi dacewa ga mace.

"Manzon Allah ya ce mace ta zauna ta yi salati a cikin gidanta ko a tsakiyar ɗakinta ya fi mata alheri a kan zuwa masallaci."

Sai dai malamar ta ce ba laifi ba ne mace ta je masallaci domin yin waɗannan nafiloli "idan ta ga cewa ta fi samun natsuwa lokacin da ta je masallacin ta bi liman".

Sai dai malamar ta bayar da shawarwari ga macen da ke son zuwa masallacin domin irin wannan sallah:

xxx

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shiga ta Mutunci:

Malamar ta ce "idan za ki fita ya kamata ki sa dogon wando, domin har addu'a manzon Allah ya yi wa mace mai saka wando, saboda wata baiwar Allah da ciwo ya same ta, da ta faɗi ba a ga tsiraicinta ba, sai ya yi addu'a ga macen da take yin wannan dabarar".

Ta ce idan mace ta saka wando da riga a ciki sai ta ɗora wata rigar a sama, wadda za ta bai wa mace damar yin gudu ko da an samu matsala.

Haka nan malamar ta shawarci mace ta sanya takalmi maras tudu "saboda kada a ji sautin takawar ki, sannan kuma ba zai harɗe ki ba idan abin gudu ko sauri ya kama," in ji Malama Khadija.

Zuwa babu nauyi:

Malamar ta kuma shawarci mata da su guje wa ɗaukan kaya da yawa domin zuwa wurin sallolin dare da su. "Ki kiyayi fita da kayan abinci da kwamin shayi."

Zuwa da ƙaramar waya:

A cerwar malamar idan har ta kama mace na son ta je wurin sallolin dare da waya saboda gudun wani abu da zai taso na gaggawa "to ki je da ƙaramar waya kuma ki kashe ƙaran (sailens)".

Fita da ɗan rakiya:

"Idan za ki fita ki tabbatar kin samu sahhalewar mijinki, ƙila ma ya zama shi ne zai kama hannun ki ku tafi, ko kuma ku tafi tare da wani yayanki ko babanki ko kuma babban ɗanki wanda zai zama miki kariya," a cewar malamar.

Sai dai ta ƙara da cewa mace za ta kuma iya tafiya tare da abokan zamanta (kishiya) ko facala, "matuƙar za ku kame kanku daga barin ciye-ciye a hanya ko hira ko kuma fesa turare."

Sauran abubuwan da malamar ta buƙaci mata su yi su ne:

  • Rufe gida da sakata
  • Kada yara su buɗe gida idan an yi sallama