Wane zaɓi ya rage wa mataimakin gwamnan Kano bayan yunƙurin tsige shi?

Asalin hoton, Comr Aminu Abdussalam Gwarzo/FB
Majalisar dokokin jihar Kano ta sanar da aike wa mataimakin gwamnan jihar, Comdr. Aminu Abdulsalam Gwarzo takardar aniyar majalisar ta tsige shi bayan zarginsa da aikata wasu laifuka.
A ranar Alhamis ne Majalisar dokokin jihar ta Kano, ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, bisa wasu zarge-zarge da aka gabatar a kansa a gaban majalisar, ranar Alhamis.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini ne ya gabatar da ƙudurin kan zarge-zarge da ya ce sun haɗa da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin da ya shugabanci wasu hukumomin gwamnati.
Kan haka ne majalisar ta ce ta gabatar da ƙudirin tsige shi daga muƙamin nasa.
A watan Janairu ne dai gwamnan jihar Abba Kabir tare da wasu mambobin majalisar dokokin jihar, ciki har da kakakin majalisar suka fice daga NNPP zuwa APC.
To sai mataimakin gwamnan bai yi shiga cikin masu sauya sheƙar ba, inda ya ci gaba da zamansa a NNPP, lamarin da ya sa wasu ke ganin yunƙurin tsige shi tamkar bi-ta-da-ƙullin siyasa ne.
Wane zaɓi yake da shi?

Asalin hoton, Comr Aminu Abdussalam Gwarzo/FB
Kawo yanzu dai mataimakin gwamnan bai yi wani martani a hukumance ga yunƙurin majalisar dokokin ba.
Barista Abba Hikima Fagge wani lauya mai zaman kansa a kano, kuma masanin kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce akwai zaɓi guda biyu da suka rage wa mataimakin gwamnan a daidai wannan lokaci.
Zaɓi na farko
Zaɓi na farko ne idan aka ba shi takardar gayyata, aka buƙaci ya je gaban kwamitin da za a kafa domin bayar da bahasi kan tuhume-tuhumen da ake yi masa, ya amsa gayyatar domin kare kansa.
''Sashe na 188, (ƙaramin sashe na 2 ko na 3)na kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa idan aka tuhumi mutum da irin wannan wannan, zai iya zuwa ya kare kansa shi da kansa ko kuma ta hanyar lauyoyinsa'', in ji shi.
Sai dai Abba hikima ya ce a gyaran da ka yi wa kundin dokar a shekarar 2013, da ya ce irin wannan tuhuma ta neman tsige mutum, idan aka yi wa mutum, kuma aka same shi da laifi har aka tsige shi, to kotu ba ta da hurumin saurarin ƙorafin tsigewar.
''To amma idan ba a kammala ba, ko aka samu wata lam'a a matakan tsigewar kotu za ta iya shiga ciki'', in ji masanain dokokin Najeriyar.
Zaɓi na biyu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani zaɓin da mataimakin gwamnan shi ne zuwa kotu domin neman ta dakatar da majalisar daga wannan yunƙuri, a cewar Abba Hikima, sai dai ya ce a nan ba dakatar da majalisar za a yi ba.
''A irin wannan kuma sai dai ya ƙalubalanci hanyar da majalisar ta biyo, idan akwai kuskure, ya ƙalubalanci wannan kuskure'', in ji shi.
Ya ce a irin wannan yanayi kuma kotun ba ta da hurumin hana majalsiar yunƙurin, sai dai ta ce an saɓa wata doka, a koma a gyara.
''Idan ya zama an fara abin ba da hanyar da ta dace ba, ko an saɓa wa wata doka wajen fara binciken tsigewar, to zai iya zuwa kotu domin tanemi majalisar ta gyara abin da yake saɓa wa doka'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ƙara da cewa a ƙa'idar kotu ba ta hana yin bincike, sai dai ta bayar da gyara kan hanyar da ya kamata a bi domin gyara hanyar da take ganin ta saɓa.
''Yawanci ba binciken kotu ke hanawa ba, sai dai ta ce a gyara hanyar da take ganin an saɓa idan akwai wajen gudanar da binciken'', in ji ƙwararren lauyan.
Laifukan da ake tuhumar Aminu Abdulsalam

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/FB
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Hon. Lawan Hussaini Dala ya bayyana laifukan da suke zargin mataimakin gwamnan da aikatawa da suka haɗa da:
- Tsakanin shekara ta Yuni 2023 zuwa Janairu 2024 ya karɓi kuɗi daga ƴan kwangila har naira miliyan 1.5 daga kowace ƙaramar hukuma, wato miliyan 66 a kowane wata, har na tsawon wata bakwai. Wanda hakan ne nufin ya karbi naira miliyan 462, wadanda ya yi amfani da su kan abubuwa na ƙashin kansa.
- Tsakanin watan Janairun zuwa Yulin 2024 ya karɓi wasu kudade da sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman, waɗanda suka kai miliyan 3,250 daga kowace ƙaramar hukuma 142.2 na tsawon wata shida, wanda jimilla ya kai naira miliyan 726.
- Cin amanar ofis, ta hanyar yin amfani da ofishinsa wajen sanya ƙananan hukumomi su bai wa kantin sayar da magani na Novomed kuɗi har naira miliyan 440.











