Dalilan jam'iyyun siyasar Najeriya na barazanar ƙaurace wa zaɓen 2027

Asalin hoton, @ipacnigeria1
Shugabancin kungiyar jam'iyyun siyasa a Najeriya IPAC ya bayyana dalilan da ya sa jam'iyyun suka yi barazanar ƙaurace wa zaɓen 2027.
Jam'iyyun sun yi gargaɗin cewa za su iya kaurace wa babban zaben 2027 idan har ba a yi gaggawar gyara wasu tanade-tanaden da ke cikin sabuwar dokar zabe ta 2026 ba da aka amince.
Shugaban kungiyar tuntuɓa tsakanin jam'iyyun siyasar na Najeriya Yusuf Dantalle ya shaida wa BBC cewa idan har ba a yi gyara ga ɓangarorin dokar zaɓen ba da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya riga ya sanya wa hannu, za su ƙaurace wa zaɓen 2027.
Batun tsarin zaɓen fitar da ƴantakara ne babban korafin jam'iyyun siyasar inda sabuwar dokar zaɓen ta yi watsi da tsarin wakilai da ake kira deliget.
IPAC na adawa ne musamman sashe na 84(2) na dokar zaɓen, wanda ya soke tsarin fitar da gwani a jam'iyyun siyasa ta hanyar wakilai.
Sabuwar dokar ta amince da tsarin zaɓe na ƙato bayan ƙato ko kuma ta hanyar sasanci tsakanin ƴantakara.
Jam'iyyun siyasar sun ce wannan ya saɓa ƴancin da kundin tsarin mulki ya ba jam'iyyun siyasa na tafiyar da harakokinsu na cikin gida.
"Idan ba a yi abin da muka ja hankalinsu ba za mu iya ƙaurace wa zaɓen 2027," in ji Dantalle.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ƙara da cewa ƙungiyarsu za ta haɗa kan jam'iyyun siyasa a sassan Najeriya idan har majalisar tarayya ba ta sake yin gyara ga sashen dokar da ya hana amfani da deliget ba wajen zaɓen yantakara a jam'iyyun siyasar.
Kungiyar jam'iyyun ta ce nan gaba za ta kafa wani kwamitin da zai mika korafe-korafen ga masu ruwa da tsaki.
IPAC ta kuma yi caccaki matakin aika sakamakon zaɓe ba ta hanyar amfani da laturoni, wanda ta ce rashin haka zai shafi sahihancin zaɓen 2027. Don haka jam'iyyun siyasar sun buƙaci majalisar tarayya ta sake yin gyara domin amincewa da aika sakamako ta hanyar intanet.
Tun a watan Fabrairu shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu kan dokar zaɓen da aka yi wa gyara bayan shafe makwanni ana cecekuce a Najeriya kafin majalisa ta amince.
Bayan amincewa da dokar ne kuma hukumar zaɓen Najeriya Inec ta fitar da jadawalin zaben 2027.
Duk da barazanar jam'iyyun siyasar na ƙauracewa zaɓen, Inec ta bayyana cewa za ta tabbatar da an gudanar da babban zaben kasar cikin adalci ga kowa.











