Hukuncin masu kallon fina-finan batsa a Ramadan

Asalin hoton, getty images
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja
Ana kyautata zaton cewar a watan Ramadan, Musulmi zai kame daga ci da sha da kuma jima'i kamar yadda addinin ya tanada ga mai azumi wato dukkannin gabbai suna azumi.
To sai dai a kan samu yanayin da masu azumi musamman matasa kan kalli fina-finan batsa watakila saboda tunanin hakan zai rage musu tsawon lokaci da dauke hankali daga kishirwa da yunwa ko kuma sakamakon irin yadda aka saba da kallon batsar.
Abin tambaya a nan shi ne shin ko me addinin Musulunci ya ce dangane da masu wannan dabi'a?
Malama Habiba Yahaya Alfadarai, malamar addinin Musulunci a Abuja ta shaida wa BBC cewa kallon fina-finai musamman na batsa ba sa karya azumi a kankansu duk da cewa haramun ne amma kuma suna tauye ladan azumi wanda daga karshe ka iya kai wa ga rasa ladan azumin baki daya.
"Kallon fina-finan banza da na batsa dukaninsu haramun ne a addinin musulunci, Allah ya ce wa Manzan Allah (saw) ya faɗawa muminai cewa Ya haramta alfahasha, abin da ya bayyana daga ciki da kuma abin da ya ɓuya." a cewar malama Habiba.
"Manzan Allah (saw) har ila yau ya ce ayar alƙur'ani ya ce muminai sun rintse idanuwarsu daga kallon fina-finan banza da na batsa sannan su kare al'aurarsu, wannan shi ne zai fi tsarki a garesu kuma Allah yana ganin duk wanda ya aikata akasin haka kuma Ya sani saboda haka kallon fina-finan banza ko ba a Ramadanu ba haramun ne ballantana kuma a Ramadana." A cewar malamar.
Malamar ta ƙara da cewa "Duk wanda yake azumi kuma yake kallon fina-finan banza, idanunsa ba su yi azumi ba, kuma ya kasance idan ana azumi, duka gaɓoɓin mutum ma suna azumi."
Ta ce azumin ido shi ne daina kallon abubuwan da ba su halatta a kallon su da furta su ba ko da ma ba a lokacin azumi ba.
Ta ya ya ake iya tantance fina-finan batsa?
Malamar ta yi bayanin yadda za a tantance fina-finan batsa da cewa su ne fina-finana wadanda ake nuna tsiraici ko kuma furta kalaman banza da suka kunci bayyana al'aura da za su iya tayar da sha'awa.
"Duk wani abu da Allah ya yi umarnin a rufe ko kar a faɗa na tsiraici ko al'aura, kuma aka nuna ko faɗi akasin haka shi ne batsa."
Yanayin da kallon batsa ka iya haddasa yin kaffara
Malama Habiba ta ce hukucin abun da Allah ya haramta kuma mutum ya aikata, yana da zunubi, akwai zunubun da Allah ya tanadarwa mai aikatawa.
Ta ƙara da cewa kallon fina-finan batsa a watan Ramadan ba ya lalata azumi amma kuma yana tauye ladan azumi sosai har ma ta kai ga zagwanyewar ladan baki daya.
"Ba za mu ce kallon fina-finan batsa yana lalata azumi ba, zai iya lalata azumi ne idan kallon ya kai ga mutum har ya fitar da wani abu daga jikinsa kamar maniyi sanadiyar wannan sha'awar sakamakon kallon da ya yi.
Idan hakan ta faru, to gaskiya ya karya azuminsa kuma sai ya yi kaffara wato bayan sallah zai rama azumi 60 sannan ya kawo wannan dayan da ya karye, daidai da hukuncin mutumin da ya karya azuminsa da gangan.
"Amma kuma idan babu wani abu da ya fita daga jikinsa sakamakon kallon batsar ko kuma kalaman batsa to za a iya cewa azumin nasa ya samu babbar nakasu kuma ya yi wa Allah babban laifi." In ji Malama Habiba.
Abubuwan da ake son mai azumi ya lazimta
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Halliru Abdullahi Maraya da ke birnin Kaduna, ya yi bayani kan abubuwan da mai azumi ya kamata ya dinga yi a watan ramadan kuma sun haɗa da:
- Yawaita karatun Al-Kur'ani: Malamin addinin Musuluncin ya ce yawaita karatun Al-Qur'ani mai girma a wannan lokaci na azumi yana haɓaka lada saboda falalarsa.
- Yawaita zikiri: Sheikh Halliru Maraya ya kwaɗaita wa mutane cewa su yawaita yin zikiri kamar istigfari da salatin annabi da hailala da kuma yawan tasbihi.
- Yawaita ciyarwa: Malamin ya kuma ce ciyarwa a wannan lokaci na azumi ba karamin abu ba ne saboda falalar da ke tattare da hakan. Ya ce Manzon Allah (SAW) ya kwaɗaitawa mutane muhimmancin ciyarwa.
- Sallar dare: Sheikh Maraya ya ce wani abu da ke haɓaka lada a watan azumi shi ne yawaitar nafilolin dare musmaman tahajjud da sallar tarawihi saboda falalar yin haka ba ta misaltuwa.
- Kame baki: Malamin ya ce mai azumi ya kasance yana kame baki daga yin karairayi saboda hakan na janyo tawaya ga azumi. Ya ce ko da mutum ba ya azumi karya haramun ce a gare shi.
- Halartar wuraren tafsiri: Sheikh Halliru ya ce mutane su rika bayar da lokacinsu wajen halartar tafsirai da kuma jin sakon Allah, inda ya ce hakan zai bai wa mutum damar sanin abubuwan da Allah yake so da wadanda ba ya so.
Daga karshe malamin ya ja hankali masu azumi da cewa ya kamata duk wani abu da mutum ya san zai iya janyowa azuminsa nakasu to bar shi kasancewar watan Ramadan lokaci ne na tarbiyar jiki da zukata.
Ana dai fatan cewa irin tarbiyya da mai azumi ya samu a watan na Ramadan za ta dore har bayan watan, ma'ana halayyarsa za ta sauya sannan ana kyautata zaton zai dore da ayyaukan da aka lissafa a sama har ma karshen rayuwarsa.











