'Allah ba zai karɓi ciyarwa da dukiyar haram ba'

Bayanan bidiyo, Allah ba zai karɓi ciyarwa da dukiyar haram ba - Sheikh Tukur Al-Manar
'Allah ba zai karɓi ciyarwa da dukiyar haram ba'

A daidai lokacin da Musulmi ke ta rige-rigen ciyarwa da kyautata wa marasa shi a watan Ramadan, malaman addinin Musulunci na tunatar da jama’a da su yi amfani da dukiyar halas wajen ayyukan alheri.

Sheikh Tukur Al-Manar, malamin addinin Musulunci a Kaduna, ya ce idan mutum ba shi da abin da zai ciyar ko taimaka wa dan uwansa sai ta hanyar haram, to gwara ya yi amfani da wanda ke hannunsa na halal komai kankantarsa.

Shehin malamin ya ja kunnen mutanen da Allah ya hore wa amma kuma ba su son ciyarwa ko kuma taimakon al’umma da shi.