Abin da ya sa Amurka ta nemi taimakon Ukraine a yaƙin Iran

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky yayin da yake magana a taron majalisar tsaron ƙasar

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, James Landale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent, in Kyiv
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce Amurka ta buƙaci ƙasarsa ta taimaka wajen kawar da hare-haren da Iran ke kai wa ƙasashe ƙawayenta a yankin Gulf.

Ukraine na ƙera na'urori masu araha kuma masu tasiri sosai wajen kakkaɓo jirage marasa matuƙa na kai har-hare, a ƙoƙarin da take na kare kanta daga ruwan bama-bamai da Russia ke yi mata.

Wannan fasaha da ƙwarewar amfani da ita za su kasance masu amfani sosai ga ƙasashe wajen kare kansu daga hare-haren da Iran ke kaiwa a halin yanzu.

Zelensky ya yi wa ƙawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya tayin musayar na'urorin, inda shi kuma yake so su ba shi wasu daga cikin na'urorinsu na garkuwar hare-hare ta sama, waɗanda Ukraine ke buƙata.

Da aka tambaye shi game da tayin da Ukraine ɗin ta yi, Shugaba Trump ya ce ''zan karɓi kowane tayin taimako daga kowace ƙasa.''

Tun da farko Zelensky ya bayyana ƙarara cewa Ukraine za ta taimaka ne kaɗai bisa sharaɗin ba za a nakasa mata tsaronta ba, kuma idan akwai wata ribar diplomasiyya da Kyiv ɗin za ta samu.

'Ba ni gishiri in ba ka manda'

Shugaban na Ukraine ya ce ƙasarsa za ta so yin musayar na'urorinta na kakkaɓo jirage marasa matuƙa da makaman kare sararin samaniya na Amurka, domin kare kanta daga hare-haren Rasha.

Yaƙin Gaɓas ta Tsakiya ya haifar da fargabar ƙarin wahala ga Ukraine, sakamakon yadda hankalun ƙawayenta ya koma kan yaƙin.

Akwai kuma fargabar samun ƙarancin na'urorin tare makamai masu linzami ga Ukraine, haka kuma ana ganin Rasha za ta amfana sakamakon tashin farashin man fetur, babbar hanyar da take samun kuɗin yaƙin.

Zelensky ya amince da wannan hatsari, amma yana ganin hakan zai taimaka wa Ukraine cimma muradunta.

Ya kuma yi magana da ƙawayenta da ke yankin Gulf, irin su Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Qatar da Bahrain da Kuwait - inda ya alƙawarta abin da ya kira ''cikakkun matakan'' da za su taimaka wajen kare sansanonin soji da cibiyoyin fararen a waɗannan ƙasashe daga hare-haren Iran.

Illar jiragen Iran marasa matuƙa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Abin da suke buƙata daga Ukraine a bayyane yake," kamar yadda Zelensky ya wallafa shafinsa na sada zumunta.

"Duk wanda ya fuskanci hare-haren Iran zai fuskanci mummunan ƙalubale - jirage marasa matuƙa na Shaheds, musamman na da wahalar kakkaɓowa, in ba kana da wadatattun makamai da ƙwarewa ba.''

Ya ci gaba da cewa ''Babban muradinmu shi ne taimaka wa mutane kare kansu da kuma maido da zaman lafiya a muhimman hanyoyin safarar muhimman kayayyaki na duniya''.

"Ƙawayenmu na tuntuɓar Ukraine don taimakon kare kai daga jirage marasa matuƙa na Shaheds - musamman horo da ƙwarewar kakkaɓo su. Haka ma akwai buƙatar taimako daga Amurka."

Ukraine ta jima tana fama da hare-haren Rasha da jirage marasa matuƙa na Shahed, wanda Iran ke ƙerawa.

Batun neman taimakon Ukraine da Amurka ta yi ba asara ba ce ga UKraine, wadda ta jima tana fama da jan ƙafar Trump wajen kare kanta daga mamayar Rasha.

A ƙarƙashin gwamnatin Trump, Amurka ta dakatar da tallafin soji kai-tsaye ga Ukraine, amma ta ci gaba da bai wa ƙasar taimakon bayanan sirri da za su taimaka wa ƙasar don kare kanta daga jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami, da kuma samun damar kai hare-hare cikin Rasha.

Wace riba Ukraine za ta samu?

Bayan kwashe shekaru tana neman taimako, a yanzu da alama Zelensky na son yi amfani da wannan damar wajen amfana da damar ta hanyar samun tallafin diplomasiyya da na soji da kuɗi.

Ukraine na fatan samun taimakon Amurka, idan ta tallafa wa ƙawayen Amurka da ke yankin Gulf, musamman Saudiyya.

Haka kuma tana fatan samun tallafi tsakanin ƙasashen Larabawa, waɗanda wasunsu ma na da alaƙa kai-tsaye da Rasha, kuma suka ƙi ɗaukar ɓangare a yaƙin da ƙasashen biyu ke gwabzawa.

Tuni dai tawagar wakilai daga ƙasashen yankin Gulf suka isa Kyiv domin tattauna batun makaman.

Wata majiya ta ce an shaida wa wasu daga cikinsu cewa su zauna a Ukraine har sai an cimma yarjejeniyar.

An bayyana cewa Birtaniya na duba yiwuwar yadda za ta taimaka wa Qatar.

Zelensky ma zai buƙaci haka, ta hanyar bai wa ƙawayenta da ke yankin Gulf cikakken tsaron sararin samaniyarsu, ya kuma ba su shawarar daina amfani da makamai masu tsada wajen kakkaɓo ƙananan jirage marasa matuƙa.

Ukraine na fama da ƙarancin na'urorin tsaron sararin samaniya, kuma ba za ta so karkatar da tsirarun da take da su ba zuwa Gabas ta Tsakiya.

Za mu bayar amma da sharaɗi - Zelensky

A cewar Shugaba Zelensky, kowane taimako da Ukraine ta bayar zai kasance bisa sharaɗi.

"Tabbas duk taimakon da za mu bayar sai da sharaɗin ba zai kawo nakasu ga tsaron ƙasarmu ba, kuma zai zama tamkar adashi muka zuba a fannin diplomasiyyarmu''.

Shugaban majalisar tsaron Ukraine, Ihor Fedirko, ya shaida wa BBC cewa ƙasar za ta riƙa ƙera na'urorin kakkaɓo jirage marasa matuƙa akalla 10,000 a kowane wata.

Sai dai ya ce fitar da na'urorin zuwa ƙasashen waje na buƙatar amincewar man jagororin Ukraine.

Haka ma ya ce koda ƙasar ta amince da fitar da na'urorin, Fedirko ya yi gargaɗin cewa zuwa gaba samun horo da ƙwarewar aiki da su don tsare sararin samaniyarsu yadda ya kamata zai zame wa ƙasashen babban ƙalubale

"Idan ba su samu horo da ƙwarewar aiki da su ba, za su zame musu kaya ne kawai'', in ji shi.

"Za mu iya aika muku nau'rorin. Amma me za ku iya yi da su? Ta ya za ku yi amfani da su, wa zai koya muku amfani da su?

"A yanzu haka cibiyoyinmu na samun horon amfani da makaman na cike da jami'anmu da ke samun horon amfani da su.''