Golan Chelsea, Sanchez, ya koma Como a matsayin aro

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron ragar Chelsea, Robert Sanchez, ya koma Como a matsayin aro na tsawon kakar wasa guda bayan ya rasa matsayinsa na mai tsaron raga na farko ga Emiliano Martinez.
Sanchez ne ya fara wasan da Chelsea ta doke Fulham da ci 3-2 a wasansu na farko a gasar Premier, amma ya bari ƙwallon da Josh King ya buga ta kuɓuce masa a kusurwar raga.
Damuwa game da yadda dan kasar Spain din ke taka leda ta sa ƙungiyar ta Xabi Alonso ɗauko ɗan ƙasar Argentina, Martinez, daga Aston Villa kan kuɗi £7.5m.
Martinez ne ya fara wasan da Chelsea ta doke Brighton da ci 4-3 a ranar Lahadi — sa'o'i kaɗan bayan ƙungiyar ta sanar da ɗaukarsa — yayin da aka cire Sanchez daga cikin jerin ƴan wasan da za su buga wasan.
Sanchez, wanda ya kasance zaɓin farko a matsayin mai tsaron ragar Chelsea tun bayan komawarsa daga Brighton a shekarar 2023, ya buga wasanni 112 kuma ya lashe gasar Conference League da kuma Club World Cup tare da ƙungiyar ta Stamford Bridge.
BBC Sport ta samu labarin cewa kungiyar Como, wadda tsohon ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Spain, Cesc Fabregas, ke horaswa, tana da damar sayen ɗan wasan mai shekaru 28 bayan ƙarewar wa'adin aron.



















