Ladubban da suka kamata mai azumi ya lazimta lokacin Ramadan

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Ladubban da suka kamata mai azumi ya lazimta lokacin Ramadan

Yayin da al'ummar musulmin duniya suka wayi gari da azumin watan Ramadan a yau Asabar, malamai sun fara fadakarwa game da laduban da suka kamata mai azumi ya kiyaye da su a lokacin wannan ibada.

Sheikh Idris Yunus, wani malamin addinin musulunci ne a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce abin da ake so mai azumi ya yawaita yi shi ne lazumtar masallaci.

''Komai ƙanƙantar damar da mutum ya samu to ya je masallaci'', in ji shi.

Na biyu mutum ya kauce wa aikata zunubi ko abubuwan da Allah ya haramta.

Ana so mutum ya shiga azumin Ramadan da kyakkyawar zuciya, tsaftatacciya, ba tare da gillin wani a zuciyarsa ba.