Me ya kamata mu ci, me ya kamata mu ƙaurace wa a watan Ramadan?

Asalin hoton, Getty Images
Miliyoyin Musulmai a faɗin duniya na ci gaba da azumin watan Ramadana ɗaya daga cikin watanni masu tsarki a addinin Musulunci.
A watan ne aka saukar wa Annabi Muhammad SAW littafin al Qur'ani mai girma.
Ana yin azumi ne a watan baki ɗaya kuma ɗaya ne daga cikin rukunan addinin Musulunci, wasu rukunai da aka wajabta wa Musulmai su yi riƙo da su iya ikonsu.
A lokacin Ramadan Musulmai na cin abinci ne kafin asubahi, abin da ake kira Sahur.
Ba sa ci ko shan komai a rana ko da wata har sai lokacin shan ruwa bayan rana ta faɗi abin da ake kira Iftar.
Lafiyayyun mutane kamar yadda addini ya zayyana ake sa ran su yi azumin cikakke - waɗanda ba su da lafiya da yara da wadanda ba su balaga ba da mata masu ciki da masu shayarwa da masu jinin haila da matafiya duk azumi na sauka a kansu.
Wasu azumi baya ba su wuya wasu kuma suna shan wuya, kuma yunwa kan damunsu yayin aikin da suke yi na yau da gobe.
To wanne irin nau'in abinci ya kamata mu ci kuma ya rage mana jin ƙishiruwa a yi azumin watan ƙalau?
Me ya kamata mu ci da sahur?
Sahur dai wani bangare ne na shirin azumin ranar, kuma yana da muhimmanci ko a addinance, a gefe ɗaya yana rage yunwa da kwaɗayi na tsawon ranar.
"A yayin Ramadan idan kana son ka yini da kwarinka da lafiya shi ne a ci abin mai gina jiki, da sauransu, kuma dole ka sha ruwa sosai," in ji wani ƙwararre kan harkokin abinci, Ismet Tamer.
Ya kuma ba da shawarar a ci abinci mara nauyi mai lafiya yayin shan ruwa.

Asalin hoton, Getty Images
Kwararriya kan harkokin abinci Bridget Belam ta ce yana da kyau a ci abinci mai nauyi lokacin sahur, ko kuma nau'ukan abincin da suke tsaba, saboda da a hankali suke narkewa, za su riƙa bai wa mutum kwarin jiki a duka yinin.
"Kamar haka dai tsaba biredi da sauran abubuwa yayin sahur," in ji ta.
Bincike ya nuna cewa na'in abinci irin su wake da sauransu za su iya ƙarawa mutum kwarin gwiwa da kashi 30.
"Yana da kyau a sha ruwa isasshe sai ka ga a duka yinin ba ka ji ƙishi ba," in ji Benelam wadda ta nuna a kiyayi sahur da abubuwa masu gishiri.
"Abinci mai gishiri yana sa ƙishi, kuma kamata ya yi ya zama abu na ƙarshe da mutum zai ci. Doguwar rana ce da za ka dade kana jin ƙishi a cikinta."
Me ya kamata a ci lokacin shan ruwa?
Abu ne sananne lokacin shan ruwa an fi so a yi buɗa baki da dabino kamar yadda yake a addinance, sannan a bi shi da abubuwa masu ruwa da sikari, kuma wannan ce hanyar da Fiyayyen Halitta ke shan ruwa da ita.

Asalin hoton, Getty Images
"Hanya ce mai kyau buɗe baki da dabino da kuma ruwa, sannan su buɗe maka hanyar cin abinci," in ji Bridget Benelam. "Za su ƙara maka kwarin jiki su hana ka jin ƙishi."
"Bayan kwashe yini ba tare da cin komi ba, bai kamata mutum ya yi buɗa baki ba da abu mai nauyi, nan da nan za su sanya ka ji ka gaji, ka ji kasala da kuma rashin lafiya a wasu lokutan.
Abun da ake ci bayan wannan ya sha banban da al'ada da kuma al'uma, ko wa da irin abin da yake ci a nahiyarsa, amma kan wannan ba wata ƙa'ida.
Wasu kwararru kan abinci na bayar da shawara kan cewa ka da a ci abincin buɗa baki da yawa lokaci guda, kamata yayi a raba shi gida biyu, wannan zai taimaka wajen narkewar abincin da aka ci cikin gaggawa.
Ko kun san azumi na da alfanu ga lafiyarku?
Babu shakka azumi na da tasiri kan lafiyar ɗan adam, yayin da azumi ya a huta gobe ya zama wata fitattciyar hanyar rage ƙiba a ko ina.
Maimakon mayar da hankali kan abin da za a ci, shi wannan azumin da ake yi na yau azumi gobe hutu zai taimaka maka wajen cin abinci. Wanda hakan ke nufin rashin cin abinci na wasu awanni a rana.
Manufar ita ce, idan jikinka ya saba da rashin sikari, zai riƙa ƙona kitsen da yake jiki, sai kuma ƙiba ta fara raguwa.
Bincike ya nuna daga cikin fa'idar da ake samu daga azumi akwai daidaita jini da kona kitse da bunƙasa sinadaren jiki da kariya daga ciwon siga.

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike da wata cibiyar kwararru ta fitar kan abinci a Amurka ya nuna Azumin Ramadana na taimaka wa masu fama da haɗarin cutuka masu dama na jiki.
Ka zalika ya nuna azumin Ramadana yana kare mata daga kamuwa daga cutar sankarar mama.











