Najeriya ta shiga cikin ƙasashen da ke fama da yunwa a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Wasu hukumomi Majalisar Ɗinkin Duniya biyu, sun bayyana Najeriya cikin jerin ƙasashe 16 da aka fi fama da yunwa a duniya, inda matsalar tsaro ke ƙara jefa mutane cikin halin ƙaƙa-niƙa-yi.
Hukumomin da suka haɗa da Hukumar abinci da noma ta duniya (FAO), da shirin samar da abinci na duniya (WPF), sun yi gargaɗin cewa matsalar na iya yin ƙamari idan har ba a tashi tsaye wajen shawo kan abubuwan da ke haifar da ita ba.
Wani rahoton haɗin gwiwa da hukumomin biyu na majalisar ɗinkin duniya suka fitar, ya lissafa ƙasashen Haiti, da Mali, da Falastin, da Sudan ta Kudu, da Sudan, da Yemen cikin jerin ƙasashen da ke cikin haɗarin bala'in yunwa.
Akwai kuma jerin ƙasashen Afghanistan da, Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kwango, da Myanmar, da Najeriya, da Somaliya da Syria, waɗanda rahoton ya ce suna cikin wani yanayi mai matukar bukatar agajin gaggawa ta fuskar abinci.
Sai kuma jeri na uku na kasashen Burkina Faso da Chadi da Kenya, da sansanonin 'yan gudun hijira na Rohingya da ke Bangladesh a matsayin wuraren da ake samun ƙaruwar damuwa game da matsalar ta yunwa.
Dukkan rukunonin ƙasashen dai sun auka cikin wannan hali ne a sakamakon rikice-rikice da tashe-tashen hankula da suke fama da su, a cewar rahoton.
Masu gudanar da ayyukan bayar agaji a Najeriya irinsu Aliyu Dawobe, na ƙungiyar agaji ta Red Cross, ya shaida wa BBC cewa wannan rahoto babu kuskure a cikinsa.
Ya ce,"Akwai binciken da muka yi a watan Yulin 2025, inda muka fitar da bayanin cewa a arewa maso gabashin Najeriya kawai akwai mutane miliyan uku da dubu dari bakwai da ke cikin yanayi na matukar bukatar abinci, don haka wannan babbar matsala ce saboda da dama daga cikin mutane ba sa samu su ci abinci sau biyu sannan ga iyalai kuma."
" A wuraren da muke aiki muna ganin irin wadannan matsaloli , domin a yankin arewa maso yammacin Najeriya ma mun tarar da, da yawa daga cikin yara da mata masu juna biyu da masu shayarwa na fama da yunwa abin da ke kai su ga samun ciwon tamowa."In ji shi.
Aliyu Dawobe, ya ce "a arewa maso gabashin Najeriya, matsalar tsaro ta jima ta na addabar yankin domin an shafe fiye da shekaru 15 ana fama da rikici musamman na Boko Haram, kuma yawancin mazauna wannan yanki da ma wanda ke zaune a arewa maso yammacin ƙasar manoma ne, to irin wadannan rikici na hanasu noma don haka dole a samu ƙarancin abinci domin irin waɗannan manoman na noma abincin da suke ci da kuma biyan buƙatunsu na yau da kullum ne."
Rahoton hukumomin biyu na Majalisar Ɗinkin Duniya kan abinci dai, ya ce matsalar ta yunwa na iya da da ƙamari, idan har ba a tashi tsaye wajen shawo kan matsalolin da ke haifar da ita ba.











