Yadda rikice-rikice suka jefa yara miliyan biyar cikin uƙubar yunwa a Najeriya

Abincin

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross a Najeriya ta ce fiye da yara miliyan 5.4 ne suka faɗa ƙangin yunwa sakamakon matsalolin rashin tsaro a jihohin arewacin ƙasar tara.

Babban daraktan sashen kula da lafiya na ƙungiyar, Dakta Aminu Abdullahi ne ya bayyana haka ranar Talata a Kano, lokacin ƙaddamar da shirin bayar da kulawar gaggawa kan yaran da ba sa samun abinci mai gina jiki a shiyyar arewa maso yammacin ƙasar.

Ya ce jihohin da matsalar ta yi ƙamari su ne Borno da Adamawa da Yobe da Sokoto da Katsina da Zamfara da Neja da Benue da kuma Kano.

Ƙungiyar ta ce cikin wannan adadi yara miliyan 1.8 na fama da matsananciyar matsalar.

Red Cross Nigeria ta kuma alaƙanta matsalar da rashin tsaro da ake fama da shi a wasu yankunan waɗannan jihohi.

Matsalar tsaro dai ta tilasta wa mutane da dama tserewa daga gidajensu da gonakinsu tare da zama ƴangudun hijira a wasu yankunan ƙasar.

Wasu yara

Asalin hoton, Getty Images

Mece ce cutar tamowa

Dakta Fatima Nasir Faskari, ƙwararriyar likitar yara da ke aiki a Babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina ta ce tamowa lalura ce da ke kama yara musammana sakamakon rashin wasu sinadarai da jikin ƙananan yara ke buƙata.

Ta ƙara da cewa matsala ce da ke addabar ƙananan yara sakamakon rashin sinadaran abinci da ke jiki ke buƙata.

''Ba rashin abinci mai gina ciki ne kawai ke haifar da ciwon yunwa ba, akwai sauran nau'ukan abinci da jiki ke buƙata''.

Dakta Faskari ta ce alƙaluman da Red Cross Nigeria ta fitar ba su zo da mamaki ba, saboda yadda suke samun yaran da ke fama da matsalar a asibitin da take aiki.

''Babu abin mamaki a waɗanann alƙaluma, saboda dama a daidai wannan yanayi mun fi ganin yara masu irin waɗannan matsaloli, saboda abinci ya yi ƙaranci'', in ji ƙwarariyar likitar.

Ƙananan yara

Asalin hoton, Getty Images

Mece ce illar tamowa?

Shugaban ƙungiyar Red Cross na Najeriya, Prince Oluyemisi Adetayo Adeaga, ya bayyana cutar yunwa a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke haddasa mutuwar mutane.

Ya kuma yi kiran ɗaukar matakan gaggawa domin magance matsalar.

"Rashin abinci mai gina jiki kan haifar da matsaloli a jikin ɗan'adam da za su sa a yi saurin kamuwa cututtuka, saboda rashin wasu sinadarai a jiki,'' in ji shugaban na Red Cross Nigeria.

Shugaban ƙungiyar reshen jihar Kano, Barrister Salisu Sallama, ya ce duk da matsalar Kano ba ta tsananta ba, amma akwai damuwa game da sauran jihohin, a daidai lokacin da ake ƙara fuskantar yunwa.

Me ke janyo tamowa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rashin abinci: Wannan shi ne ginshiƙi wajen samar da cutar yunwa, kamar yadda Dakta Fatima Faskari ta bayyana.

''Dama cutar yunwa ce ke janyo ta, to ga ka babban abinda ke janyo yuwan shi ne rashin abinci'', in ji ta.

Ƙwararriyar likitar yaran ta ce galibi a wasu yankunan arewacin Najeriya abinci kan yi ƙaranci a daidai wannan lokaci na damina, don haka ne ma aka fi samun cutar a lokacin daminar.

Rashin ilimi: Rashin sanin wane nau'in abinci yaro yake buƙata na taimakawa wajen haifar da cutar yunwa.

''Wasu iyaye matan ba su san nau'in abincin da yaransu ke buƙata ba, kawai su da zarar yaro ya fara cin shinkafa ko taliya da tuwo to shikenan, ba sa mayar da hankali wajen ba shi wasu nau'ikan abincin'', in ji ta.

Talauci: Wannan abin da ke haifar da cutar yunwa shi ne talauci kamar yadda Dakta Fatima Faskari ta yi ƙarin haske.

''Ai sai da wadata sannan za a saya wa yara wasu nau'ikan abincin da jikinsu ke buƙata''.

Rashin zaman lafiya: Ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta bayar da dalili na rashin zaman lafiya a matsayin abin da ya haifar da matsalar.

Dakta Fatima Faskari ta ce ''ai sai da zaman lafiya sannan za a yi noma har abinci ya wadata, a samu biyan buƙata''.

Mece ce makomar yaran?

  • Mutuwar yaran

Dakta Fatima Faskari ta ce akwai matsaloli masu yawan gaske da cutar yunwa kan haifar wa yara.

Ƙwararriyar likitar ta ce babbar matsalar da hakan zai haifar shi ne mutuwa.

''Idan cutar ta yi tsanani za ta iyar haifar da rasa ran yaron da ke ɗauke da ita ba tae da ɓata lokaci ba''.

  • Rashin ƙwarin jiki

Likitar ta ce wata matsalar da wannan cuta kan haifar wa yara ita rashin ƙwarin jiki ta yadda wasu cutukan za su kama yaran cikin sauƙi, kasancewar jikinsu ba shi ƙwarin da zai iya yaƙi da wasu ƙwayoyin cuta.

Dakta Faskari ta ce akwai kuma matsalar rashin ƙwarin jiki

  • Tasiri a rayuwarsu bayan warkewa

Dakta Fatima Faskari ta ce akwai matsaloli masu yawa da cutar kan haifar wa yaran da suka taɓa fukantar cutar a rayuwarsu ta gaba.

''Yaran da suka taɓa fuskantar cutar yunwa za su iya fuskantar matsalolin mantuwa da rashin fahimta da rashin kaifin tunani ko kuma su riƙa ware kansu daga cikin jama'a'', in ji ta.

''Koda kuwa a baya suna da ƙwaƙwalwar fahimtar karatu da zai iya yin wani abu da zai amfani al'ummar a rayuwarsu, cutar kan haifar masa da rashin kaifin ƙwaƙwalwa da zai hana su kasa karatu'', in ji Likitar yaran.