Najeriya ce kasar da yara suka fi tsunburewa a Afirka — UNICEF

Yarinya na fama da rashin abinci mai gina jiki

Wani rahoton Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce yara 'yan ƙasa da shekara biyu ba sa samun abinci ko sinadaran gina jiki da suke buƙata don samun ƙoshin lafiya da girman da ya dace.

Lamarin da hakan kan janyo cutarwa ga bunƙasar yaran irin wadda ba za a iya maye ta ba, in ji rahoton.

Rahoton ya ce a nazarin da aka yi cikin ƙasashe guda casa'in da daya har da Najeriya, an gano cewa rabin ƙananan yara daga wata shida zuwa wata ashirin da uku, ba a ciyar da su mafi ƙarancin adadi na abincin da ake ba da shawara a kullum.

UNICEF ya ce a Najeriya, duk ɗaya cikin uku na yaran ƙasar a tsumbure suke , sakamakon haka, kusan yara miliyan 17 a Najeriya a tsumbure suke ko kuma suna ramewa abin da ya sa Najeriya ta zama ƙasa mafi yawan matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a Afirka kuma ta biyu a duniya.

Rahoton ya ce Najeriya ta sauka daga kan hanyar cimma Muradan Ci gaban Ƙarni na biyu wato Kakkaɓe yunwa nan da shekara ta 2030.

Rahoton na Asusun UNICEF mai taken Ciyarwa don su Gaza? Matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ga ƙananan yara a farkon rayuwarsu - an fitar da shi ne kafin Babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan harkokin samar da abinci a wannan mako.

Rahoton ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar talauci da rashin daidaito da rikice-rikice da annoba iri daban-daban da ke da alaƙa da sauyin yanayi da cutukan da ke buƙatar kulawar gaggawa kamar annobar korona, na taka rawa wajen samun matsalar ƙarancin abinci mai gina jikin da ake ci gaba da fuskanta a tsakanin ƙananan yara a duniya.

A cikin wata sanarwa, mataimakiyar babban jami'in UNICEF a Najeriya, Rushnan Murtaza ta ce abubuwan da rahoton ya gano a fayyace suke ƙarara: ba a ciyar da miliyoyin ƙananan yara da isasshen abinci mai gina jiki ta yadda za su girma, su bunƙasa.

A cewarta, rarraunan cin abinci mai gina jiki a shekara biyun farko na rayuwa, na iya cutar da girman jiki da ƙwaƙwalwar yara cikin sauri, lamarin da kuma ka iya yin tasiri a rayuwarsu ta gaba.

Rahoton ya ce kashi biyu cikin uku na ƙananan yara ba sa samun mafi ƙarancin adadi na rukunnan abincin da suke buƙata don su girma.

A cewar safiyo kan harkokin lafiya da rabe-raben jama'ar Najeriya na 2018, a cikin ƙananan yara 'yan wata shida zuwa wata 23, kashi 23 cikin 100 ne kawai ke samun mafi ƙarancin nau'o'in sinadaran gina jiki da suka wajaba, kuma kashi 42 cikin 100 ne kawai ke samun mafi ƙarancin isasshen abinci.

A cewar rahoton idan ana son sauya wannan lamari, a yanzu lokaci bai ƙure ba na sake tunani ba kawai a kan harkokin samar da abinci ba har ma da batun kula da lafiya da kuma harkokin tallafawa rayuwar masu ƙaramin ƙarfi..