Korona za ta jawo yunwa ta kashe mutum 12,000 kullum a karshen 2020 - Oxfam

yunwa a afrika

Asalin hoton, EPA

Kungiyar agaji ta OXFAM ta yi hasashen cewa mutum 12,000 za su mutu a kowace rana daga karshen shekarar da muke ciki a kasashen duniya sakamakon tangardar da annobar korona ta janyo a fannin walwala da tattalin arziki.

Oxfam ta ce adadin ya zarce yawan mace-macen mutane a kowace rana sanadin cutar korona inda an rika samun mutum 10,000 da suka rika mutuwa tun daga watan Afrilun da ya gabata.

Matakan dakile bazuwar cutar da aka sanya a kasashen Afrika da sauran kasashen duniya sun sa mutane da dama sun rasa ayyukansu, kuma sun sa ba a yi noma domin samar da abinci ballantana mutane su saya ba.

Kungiyar ta Oxfam ta ce matsalar za ta yi kamari a kasashe irin su Sudan Ta Kudu da Sudan da Habasha da Jamhuriyar Dimokaridiyyar Kongo da kuma kasashen yammacin Afrika da ke yankin Sahel.

Al'ummomin wadannan kasashe na fuskantar yunwa sakamakon sauyin yanayi da rikice-rikice da kuma farin dango da suka afka wa gonaki a yankin Gabashin Afrika

Sai dai Oxfam ta ce annobar korona za ta kara jefa rayuwarsu cikin halin ni 'yasu.

Kungiyar ta ce Afrika Ta Kudu wadda ita ce take da yawan masu cutar korona a nahiyar Afrika kuma ita ce ta farko da ta sanya dokar kulle za ta samu karuwa a yawan masu yunwa a kasar sakamako karuwa a yawan mutanen da suka rasa ayyukansu.

Wani bincike ya gano cewa tun bayan da aka sanya matakan dakile bazuwar cutar korona a cikin mutum uku daya daga ciki ya ce yana barci ba tare da ya ci abinci ba.