Ƙurar Hamadar Sahara ta lulluɓe sararin samaniyar Kudancin Amurka

Asalin hoton, AFP
Ƙurar Hamadar Sahara ta lulluɓe sararin samaniyar wasu kasashe na yankin Caribbean na kudancin Amurka.
Ƙurar ta tashi ne daga Hamadar Sahara da ke nahiyar Afrika inda ta bi ta sararin samaniyar Tekun Atlantika.
A ranar Lahadi ta isa kasar Puerto Rico kuma tuni ta lullube kasar Cuba da wasu yankuna na kasar Mexico.
Tsibiran da ke yankin Caribbean kamar Guadeloupe da Martinique sun shafe shekara 10 suna fuskantar kurar hazo mai muni, kuma jami'an lafiya a Cuba sun yi gargadi cewa hakan na iya sawa a samu karin matsloli masu alaka da numfashi.
Kurar tana kuma lullube wasu bangarori na kudancin Florida da suka hada da birnin Miami na Amurka.

'Ƙura mai yawan da ba a saba gani ba'
Sharhi daga mai gabatar da bayanai kan yanayi na BBC, Simon King
Ganin kura da guguwa Dust a wasu bangarori masu dazuzzuka na duniya ba sabon abu ba ne. Iska na kaɗa kusan tan biliyan biyu na kurar duk shekara - inda take bin sararin samaniya ta kuma bi wasu kasashen.

Asalin hoton, Reuters
Kurar tana samar da wani abinci ga dabbobin da suke cikin teku, amma kuma tana shafar yanayi da lafiyar dan adam ta hanyar sanya masa matsalolin numfashi.
Sai dai a makon da ya gabata an ga abin da ba a saba gani ba na yadda kura mai matukar yawa ta turnuke sararin samaniyar Tekun Atlantika sannan abin ya shafi Tsakiyar Amurka da Arewacin Amurka.
Sannan kuma wasu hotunan tauraron dan adam sun nuna wani yanki mai girma da kurar ta taso daga Hamadar Sahahara tana tafiya a saman Tekun Atlantika
An yi hasashen cewa za a ci gaba da samun dusu-dusu da rashin iska mai kyawu a wasu yankuna na Karibiya da Tsakiyar Amurka har nan da mako guda.

A ranar Lahadi, an yi kurar a babban birnin Venezuela wato Caracas, inda hazon kura ya lullube manyan duwatsun da ke zagaye da birnin.

Asalin hoton, EPA
Kura ta addabi masu yawon bude ido a San Juan da ke Puerto Rico fiye da zaton sy a ranar Litinin.

Asalin hoton, AFP
Sannan launin samaniyar birnin Barbados ya zama ruwan dorawa saboda kurar.

Asalin hoton, Reuters
A Cuba, mutane sun yi ta daukar hotunan yadda launin garin ya sauya a ranar Laraba.

Asalin hoton, Reuters
Jami'an lafiya na Cuba sun gargadi mazauna kasar da ke fama da cutar asma da sauran cutuka masu alaka da numfashi cewa watakila yanayin lafiyarsu ya ta'azzara.
Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.












