Coronavirus: 'Yan Afirka ba za su iya jure wa yunwa a dokar kullen kwana 14 ba

Asalin hoton, EPA
Fiye da kashi biyu cikin uku na mutanen da aka ji ra'ayoyinsu cikin kasa 20 na Afirka sun ce abinci da ruwan shansu za su ƙare idan suka shafe kwana 14 suna zaman gida.
Sama da rabin mutanen sun ce kudadensu za su kare idan suka yi zaman kwana goma sha hudu a gida.
Binciken da cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afirka ta gudanar tare da taimakon gwamnatoci ya fitar da tsare-tsaren da za a yi amfani da su nan gaba wajen daƙile cutar korona.
Binciken ya yi gargaɗin cewa za a samu tarzoma da tashe-tashen hankula idan ba a yi amfani da matakan biya wa mutane bukatu ba.
Rahoton mai suna, Using Data to Find a Balance, ya nuna tsaka-mai-wuyar da ake ciki a Afirka wajen ci gaba da aiwatar da dokokin kulle.
An gudanar da binciken ne tsakanin karshen watan Maris zuwa tsakiyar watan Afrilu a birane guda 28 da ke cikin kasa 20 domin gano tasirin cutar korona da kuma irin halayyar da mutane suke nunawa game da kullen da aka yi musu.
Ƙasashen Afirka da dama wadanda suka dauki matakan nan da nan a kan cutar korona yanzu sun sassauta kullen da suka ƙaƙaba.
"Yawan zanga-zangar lumana inda ake buƙatar gwamnatoci su bayar da kayan tallafi wata shaida ce da ke nuna mawuyacin halin da wasu mutane ke ciki, da kuma giɓin da ake da shi wajen ɗaukar matakan daƙile cutar," a cewar rahoton.
Sai dai rahoton ya gano cewa an samu goyon baya daga kusan dukkan al'umma kan matakin da gwamnatoti suka ɗauka na sanya dokar kulle.


Mutane sun fi yin ƙorafi kan matakai kamar su rufe wuraren aiki da kasuwanni.
A cewar rahoton, ana sa ran abinci da kuɗin magidantan da suka fi ƙarancin kudi za su kare a ƙasa da mako guda.
A Najeriya da Kenya, masu amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana halin yunwa da ake ciki a yankunan karkara abin da ya sa mutane suke karya dokar kulle, a cewar rahoton.
Rahoton ya zo daidai lokacin da wani labari ya karaɗe kasar Kenya inda wata mata ke dafa wa 'ya'yanta duwatsu don ta hilace su har su yi barci, a cewarta "babu yadda na iya."
Masu binciken sun bai wa gwamnatoci shawarwarin yi wa 'yan kasashensu gamsassun bayanai game da dalilan daukar matakan kullen.
"Darasin da muka koya game da Ebola da wasu annobobi shi ne, kashe suna bukatar yi wa jama'a a matakin yankunan karkara bayanai gamsassu.
Sannan a kara musu kayan aiki da za su yi amfani da su wajen riga-kafin cutuka," a cewar Matshidiso Moeti, daraktar Afirka a Hukumar Lafiya ta duniya, wadda ta kaddamar da binciken.
Gwamnatocin kasashen Afirka sun shiga halin tsaka-mai-wuya lokacin da suke kokarin samo hanyar da za su tunkari annobar korona.
Miliyoyin mutane ne ba sa iya ɗora tukunya idan ba su fita neman abinci ba a kullum.
"Yanzu ya zama wajibi kasashe su samu matsakaiciyar hanya da za ta ba su damar dakile yaduwar cutar yayin da a gefe guda kuma suke kokarin rage raɗaɗin tabarbarewar tattalin arziki da ke addabarsu," in ji rahoton.
Zuwa yanzu kusan mutum 50,000 suka kamu da cutar korona, yayin da kimanin 2,000 suka mutu sanadin cutar.
Rahoton ya bayar da shawara cewa ko da yake yawan masu cutar a nahiyar Afirka ba su da yawa idan aka kwatanta da wasu nahiyoyin, akwai bukatar kasashe su "samar da cibiyoyin lafiya masu kayan aikin yin gwaji da ganowa tare da kula' da masu korona a matsayin wani mataki na sake gina al'umma.











