Coronavirus: Taswirar da ke nuna yawan wadanda suka kamu a duniya
Ga wata taswira da ke nuna yaduwar annobar cutar korona a duniya, da ke nuna adadin mutanen da suka kamu da cutar da yawan wadanda suka mutu a kasashen duniya.
Kwayoyin cuta na 'virus' na sauya fasali ko yaushe, amma sauye-sauyen da ke faruwa ga asalin kwayoyin halittarsu ba shi da yawa.
Ana sa rai kwayoyin cuta su sauya su rage karfi nan gaba, amma babu tabbacin haka.
Fargabar ita ce idan coronavirus ta sauya, garkuwar jiki ba za ta gane ta ba kuma riga-kafinta ba zai kare mutane daga kamuwa da ita ba.


An fara wallafawa a ranar 22 ga watan Afrilun 2020.







