Coronavirus: Wacce ƙasa ce a Afirka aka fi yin gwajin cutar?

Nigerian woman receiving swab test in Abuja

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Christopher Giles da Peter Mwai
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
  • Lokacin karatu: Minti 4

Gwaji na taka muhimmiyar rawa a yaƙi da cutar korona, yana taimakawa wajen fahimtar girman yaɗuwar cutar.

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Afirka da ke jagorantar lamurran annobar a sassan nahiyar, ta ce akwai bambanci sosai kan batun gwaji a tsakanin ƙasashe.

Waɗanne ƙasashe ne kan gaba, kuma waɗanne ne a baya?

A ina aka fi yin gwaji, da rashinsa?

Wasu ƙananan ƙasashe sun samu ci gaba inda suka zarta sauran maƙwabtansu manyan ƙasashe ta fuskar gwaji.

Mauritius and Djibouti, misali dukkaninsu sun cimma adadin da ya kamata na gwaji.

Haka ma ana yabon Ghana kan batun gwaji, inda gwamnatin ƙasar ta ce zai taimaka waje daƙile bazuwar cutar idan an ɗage dokar kulle.

Afirka ta Kudu ita ma ta ɗauki matakai sosai kan inganta gwaji, kuma zuwa yanzu an gudanar da gwaji sama da 200,000. Amma wannan bai kai alƙalumman kasashe kamar Koriya ta Kudu da Italiya da Jamus ba.

Ana bayyana damuwa cewa Najeriya mai yawan jama'a a Afirka, gwajin da ta ke bai kai mizani ba - ko da yake gwamnati ta jaddada cewa ta mayar da hankali ne kan daga rukunin waɗanda suka kamu da cutar.

Nesa nesa da juna a Uganda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nesa nesa da juna a Uganda

Wakiliyar BBC a Najeriya Chi Chi Izundu ta ce hukumomi yanzu na faɗaɗa gwaji.

"Manufar shi ne ya kai 5,000 a rana - amma har yanzu ba su kai 1,000."

Yana da kyau a fahimci cewa akwai wasu ƙasashe a nahiyar da babu ma wasu bayanai game da gwaji. kamar su Eritrea da Algeria.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Wasunsu ba su da kayan gwajin, yayin da wasu kuma saboda wasu dalilai na daban ba za su bayar da bayanan ba.

Misali, Shugaba Magafuli na Tanzania ya faɗi cewa fitar da irin waɗannan bayanai na haifar da tsoro da fargaba. Ƙasarsa na fitar da bayanai ne kawai lokaci-lokaci, wani lokaci bayanan waɗanda suka warke kawai kae fitar da bayanansu.

Waɗanne abubuwa ne ke hana inganta gwaji?

Samun wadatatattun sinadarun da ake buƙata wajen aiwatar da gwajin na iya zama da wahala, domin wasu ƙasashen Afirka ba su samar da nasu kuma suna dogaro ne da waɗanda ake samarwa a duniya da yanzu ake da ƙarancinsu.

John Nkengasong na cibiyar hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ya ce "rashin samun haɗin kai samun goyon bayan kasashen duniya ya tsame Afirka daga kan batun girman gwajin cutar."

Ya ce ƙasashen Afirka suna iya kasancewa suna da kudi, amma "ƙasashe 70 da suka kafa dokar hana fitar da kayayyakin da suka shafi asibiti," zai yi wahala a iya sayen kayayyakin da ake buƙata.

Nigeria coronavirus outbreak

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matakan da ya kamata mutane su dauka

Akwai kuma wasu abubuwa da ke kawo tarnaƙi ga inganta gwaji, waɗanda suka hada da dokar kulle, wanda zai yi wahala ga mutane su fito domin yin gwaji.

Amma, Ngozi Erondu, ta cibiyar lafiya ta Chatham House, ta ce babban al'amari shi ne kayan aiki.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Presentational white space

Hukumar yaki da cutuka masu yaɗuwa Najeriya a yanzu tana da ɗakunan gwaji 18 waɗanda za su iya tabbatar da idan mutum na ɗauke da cutar. Amma ta gabatar da buƙatar kayayyakin gwaji.

Kenya ma ta ce tana fuskantar ƙalubale na kayan gwaji, kuma adadin gwajin da ta ke yi ya ragu.

Gwamnatin larduna a Kenya ta ce a baya-bayan nan kayayyakin gwaji 5,000 kawai ake da su a ƙasar, kuma suna tsammanin samun ƙarin 24,000.

Taron masu ruwa da tsaki a Najeriya domin dakile cutar korona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Taron masu ruwa da tsaki a Najeriya domin dakile cutar korona

Akwai kuma wasu dalilai na zamantakewa da siyasa waɗanda za su iya haifar da cikas ga faɗaɗa gwaji.

"A wasu al'umomin akwai batun nuna kyama idan aka tabbatar da mutum yana ɗauke da cutar korona." in ji Ngozi Erondu. Sannan shugabannin al'umma na iya adawa da gwajin don manufarsu ta cin zabe."

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta kaddamar da wani shiri na haɗin guiwa domin inganta gwaji, Partnership to Accelerate COVID-19 Testing (PACT) wanda za a mayar da hankali kan bibiya gwaji da kuma ganowa.

Manufar shirin shi ne cimma burin yin gwaji miliyan ɗaya cikin mako huɗu a dukkanin sassan nahiyar

The initiative aims to roll out about one million tests in four weeks across the whole continent.

Ɓarkewar cutar korona a yankin Asiya da Turai ya ba kasashen Afirka lokaci da damar ɗaukar matakai, kuma yadda suka yi yaƙi da Ebola ya taimaka masu.

Amma samun kayan gwaji a kasuwar duniya, da gudanar da gwajin a inda ya kamata da samar da ɗakunan gwaji ba ƙaramin ƙalubale ne musamman da raunin tattalin arziki da tsarin kiwon lafiya

Reality Check branding
Presentational grey line