Greenland: Yadda ƙasashen Turai ke caccakar Trump kan barazanar ƙaƙaba musu haraji

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da Allah wadai da barazanar shugaba Trump na ƙaƙaba haraji ga ƙasashen Turai da ke adawa da shirinsa na karɓe ikon Greenland, wanda ya ce ya zama wajibi domin ƙalubantar barazanar tsaro daga Rasha da China.
Mr Trump ya ce zai lafta harajin kashi 10 ga kayayyakin ƙasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da kuma Denmark a farkon watan Fabrairu, tare da barazanar cewa harajin zai iya ƙaruwa zuwa kashi 25 har sai Amurka ta mallaki tsibirin mallakin Denmark.
Ɗaya daga cikin shugabannin ƙasashe takwas da donald Trump ya ambata zai lafta wa haraji, shugaban Faransa Emmanuel Macron a wata sanarwa a shafinsa na X ya ce ba za su lamunta da barazanar harajin ba, kuma harajin ba ya da wani hurumi kan tattaunawar da ake kan Greenland.
Ya ce " Idan har aka tabbatar da harajin, to ƙasashen Turai za su mayar da martani yadda ya dace domin kare ikon ƴancin Turai."
Faransa kamar sauran ƙasashe bakwai da Trump ya ambata ta tura wata ƙaramar runduna zuwa Greenland a matsayin shirin kotakwana, inda shugaba Macron ya ce magana ce ta tsaron tarayyar Turai.
"Babu wata barazana za ta yi tasiri a kanmu ko a Ukraine ko Greenland da ko ma ina ne" a cewar Mr Macron.
Shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce Denmark da mutanen Greenland na da cikakken goyon bayan Tarayyar Turai.
Ta ce tabbatar da ƴancin ƙasa shi ne tushen dokokin ƙasa da ƙasa.
Ministan harakokin wajen Denmark ya ce ya yi mamakin barazanar Amurka domin atisayen soji da aka tsara yi a Greenland daidai ne domin inganta tsaro.











