Me ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci kisan gilla ke nufi?

Asalin hoton, EPA
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa zai saka Najeriya cikin jerin ƙasashe "da ake da damuwa a kansu" saboda zargin yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na dandalin Truth Social, Trump ya ce "shi ne mataki mafi ƙanƙanta da ya dauka" zuwa yanzu.
"Kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya," in ji shi. "Ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar. Saboda haka na ayyana Najeriya ƙasar da ake da damuwa a kanta".
Bugu da ƙari, Trump ya ce ya bai wa 'yanmajalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa.
Tun a farkon watan nan wani sanata a Amurkan ya yi zargin ana yi wa Kiristoci kisan gilla, wanda gwamnatin Najeriya ta musanta.
Amma lamarin ya ci gaba da jawo muhawara a Najeriya game da sahihancin iƙirarin.
Najeriya ce ƙasa mafi fitar da ɗanyen man fetur a Afirka, kuma mafi yawan jama'a.
Me hakan ke nufi?
Bayani daga ma'aikatar harkokin waje ta Amurka sun nuna cewa sakataren harkokin waje na Amurka ne ke ayyana kasa "a matsayin wadda ake da damuwa a kanta" idan aka samu cewa kasar na mummunar take hakkin mutane wajen gudanar da addini, a karkashin Dokar 'Yancin Addini ta kasa da kasa (IRFA), ta shekara ta 1998.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Amurka ta yi amannar cewa nauyi ne da ya rataya a kanta ta bayar da bayani game da halin da ake ciki kan yancin yin addini a fadin duniya ta yadda kasashen duniya za su iya ganowa da aiwatar da maslahar magance matsalolin tauye hakkin addini," kamar yadda yake kunshe a shafin intanet na ma'aikatar tsaron Amurka.
Idan Amurka ta ayyana ƙasa a matsayin wadda ake da damuwa a kanta, hakan na nufin za a iya ƙaƙaba wa ƙasar wasu sharuɗɗa ta ɓangaren tattalin arziƙi, a cewar ma'aikatar harkokin waje ta Amurka.
A tattaunawarsa da BBC, masanin tsaro a Afirka Bulama Bukarti ya ce akwai manyan illoli uku da Najeriya za ta ci karo da su idan Amurka ta ayyana ta a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta.
Ya zayyano illolin kamar haka:
Amurka za ta daina sayar wa Najeriya makamai
Bulama Bukarti ya ce "idan har wannan batu ya tabbata to Amurka da ƙawayenta za su daina sayar wa Najeriya makamai".
Wannan sun haɗa da jirage da kayan yaƙi da Najeriyar ke amfani da su wajen yaƙi da matsalolin tsaro da ke addabar ta.
Takunkumin tattalin arziƙi
Masanin tsaron ya ce wata illar da ayyana Najeriya cikin ƙasashen da ake da damuwa a kansu ita ce daina hulɗa da ƙasar a fannin tattalin arziƙi.
Ya ce "za a daina sayen man fetur daga Najeriya kuma za a daina sayar wa Najeriya kaya."
Najeriya dai ƙasa ce da ke dogaro da kuɗaɗen da take samu ta hanyar sayar da ɗanyen man fetur a ƙsashen duniya, haka nan ta dogara sosai wajen shigar da kayan masarufi daga wasu ƙasashen.
Bukarti ya ce sanya takunkumin tattalin arziƙi zai iya haifar da ƙarancin abinci a Najeriyar da kuma lalata darajar kuɗin ƙasar.
Haɗa rigimar addini
Masanin tsaron ya ce idan har Amurka ta amince da iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a ƙasar har ta ɗauki matakan hukunta ta, to hakan zai iya faɗaɗa rarrabuwar kawuna da ke tsakanin al'ummar kasar mabiya addinai da ƙabilu daban-daban.
A shekarar 2021 ne gwamnatin Amurka ta cire sunan Najeriya daga cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa a kansu bayan saka ta a cikin jerin a karon farko.
Sai dai sabbin kiraye-kiraye na baya-bayan nan sun sanya hukumomi da al'umma da dama suka riƙa hasashen cewa shugaba Donald Trump na iya sake mayar da sunan Najeriya cikin jerin.
Me gwamnati ta ce game da zargin kisan ƙare-dangi?
Tun a watan Satumban 2025 gwamnatin Najeriya ta musanta zargin da ake yi na cewa ana yi wa mabiya addinin kirista kisan ƙare-dangi a ƙasar.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na ƙasar Mohammed Idris ya ce iƙirarin da wasu kafafen yaɗa labarai da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta ke yi kan cewa ana kisan ƙare-dangi ba gaskiya ba ne, duk kuwa da cewa ƙasar tana fama da matsalar tsaro.
"Gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai, sannan ta yi watsi da iƙirari na baya-bayan nan da ake yi kan cewa ƴan ta'adda a Najeriya na kitsawa da aiwatar da kisan ƙare-dangi a kan mabiya addinin kirista."
Ya ce ba za a bayyana matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita a matsayin wani rikici da ke shafar wani ɓangaren al'umma guda ɗaya ba.
"Ayyukan ƙungiyoyin ƴan ta'adda bai taƙaita a kan mabiya wani addini ko ƙabila ɗaya kawai ba."
Najeriya ta shafe sama da shekara 15 tana fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, lamarin da ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da tarwatsa al'umma da kuma haifar da matsalar jin-ƙai.
Ƙungiyar Boko Haram ta fara ne da da'awar ƙaurace wa karatun boko, inda ta riƙa kai hare-hare kan jami'an tsaro da kuma hukumomin gwamnati.
Sai dai ƙungiyar ta kuma riƙa kai hare-hare kan fararen hula a kasuwanni da kuma wuraren ibada, kamar masallatai da majami'u.
Haka nan mayaƙan ƙungiyar sun riƙa kai hare-hare a makarantu sun garkuwa da ɗalibai, ɗaya daga cikin shi ne sace ɗaliban makarantar sakandaren mata da ke Cibok a jihar Borno a ranar 14 ga watan Afrilun 2024.
Sai dai baya ga Boko Haram, akwai matsalar rashin tsaro tsakanon manoma da makiyaya a yankin tsakiyar Najeriya.
Manoma a jihohin Filato da Benue, waɗanda akasarinsu mabiya addinin kirista ne, na yin artabu da makiyaya waɗanda ke neman wa dabbobinsu abinci.
Hare-hare da kuma hare-haren ramuwar gayya sun yawaita a yankin, inda hakn ke haifar da asarar rayuka da dukiya.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce tana bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta samar da zaman lafiya a yankin.
Matsalolin tsaro da suka raba hankulan jami'an tsaron Najeriyar sun sanya ana ci gaba da samun irin waɗannan hare-hare a kusan dukkanin yankunan ƙasar.
Ƴanfashin daji masu ɗauke da makamai na kai hare-hare a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, inda suke kashe mutane tare da garkuwa da wasu domin neman kuɗin fansa.
Haka nan ƙasar na fama da rikicin ƴan awaren Biafra a kudu maso yammcin ƙasar.











