Rikice-rikice uku da suka sa kashe-kashen Benue suka ƙi ci suka ƙi cinyewa

Asalin hoton, Hyacinth Alia/Facebook
Rikicin jihar Benue na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya, musamman yadda matsalar ke ci gaba da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Jihar Benue - wadda ke tsakiyar Najeriya - ta kasance kan gaba a jihohin da ke fama da matsalar tsaro a ƙasar.
Sau da yawa akan alaƙanata rikicin jihar da addini ko ƙabilanci.
To amma shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya, Mallam Isa Sanusi ya ce rikicin jihar ba shi da alaƙa da addini, kamar yadda ake bayyanawa.
''Ƙungiyarmu ta sha gudanar da bincike masu yawa kan rikicn jihar, kuma abin da muka gano shi ne rikicin ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci ko kaɗan'', in ji shi.
Shugaban na Amnesty ya kuma zayyano wasu abubuwa uku da ke haifar da hare-hare a jihar ta Benue.
Rikicin manoma da makiya

Asalin hoton, Getty Images
Abu na farko da ke yawan haifar da rikice-rikice a jihar Benue shi ne rikicin manoma da makiyaya a cewar Isa Sanusi.
A lokuta da mata manoma da makiyaya kan zargi juna. Makiyaya kan zargi manoma da nome hanyoyin da dabbobinsu ke bi, yayin da ake gefe guda manoma kan zargi makiyaya da ɓarnatar musu da gonaki.
''Wannan rikici ya jima ana fama da shi a jihar Benue,'' in ji shi.
Ƙungiyoyin ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban na Amnesty a Najeriya ya ce rikici na biyu da ke addabar jihar shi ne na ƙungiyoyin ƴanbindiga masu ɗauke da makamai da ke kai wa juna hari.
Isa Sanusi ya ce a 2020 akwai wani riƙaƙƙen ɗandaba, mai suan Gana - da ya amince ya miƙa wuya a yi masa afuwa, amma bayan ya miƙa wuyan sai aka kashe shi.
''To wannan kisan da aka yi masa ya tayar da fitina, wadda har yanzu ake ci gaba da yinta a jihar'', in ji Isa Sanusi.
Rikicin Jukun da Tibi

Asalin hoton, Getty Images
Wannan rikici ne da aka jima ana yi tsakanin manoma ƴan ƙabilar Tibi da ƴanƙabilar Jukun, kamar yadda Isa Sanusi ya yi bayani
Shugaban na Amunesty ya ce galbi an fi samun wannan matsala a kusa da kan iyakar jihar da Taraba.
Kuma wannan mafi jimawa daga cikin abu ukun da ke haddasa rikicin jihar Benue.
''Rikicin ya jima domin kuwa tun shekaru 1990 ake yin wannan rikicin'', in ji shi.
Isa Sanusi ya ce waɗanan dalilai ne ya sa yawan mutanen da ake kashewa suka fi yawa a jihar.
Wane hali ake ciki a jihar?
Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya buƙaci jami'an tsaron ƙasar su gaggauta kawo ƙarshen rikicin.
Tuni dai shugaban ya tura wata tawaga mai ƙarfi domin kwantar da hankula a jihar.
Tawagar - wadda ta ƙunshi babban haftsan taron ƙasar da babban sifeton ƴansandan ƙasar, da sakataren gwamnatin tarayya da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro - ta gana da gwamnan jihar da iyalan wadanda hare-haren suka shafa da nufin haƙurƙurta da su.
Haka kuma an baza ƙarin jami'an tsaro jihar, tare da samar da jiragen sama da ke sintiri ta sama a Makurdi, babban birnin jihar da kuma kewayensa.
Tinubu zai ziyarci jihar ranar Laraba

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Baya ga tawagar da ya aike jihar, shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayyana aniyasa ta jihartar jihar a gobe Laraba.
Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, ta ce shugaban kai ziyarar ne domin duba halin da jihar ke ciki da nufin kawo ƙarshen rikicin.
Sanarwar ta ce a lokacin ziyarar, shugaba Tinubu zai gana da masu ruwa da tsaki na jihar, da suka haɗa da sarakunan gargajiya da ƴansiyasa da jagororin addini da shugabannin al'umma da ƙungiyoyin matasa, da nufin lalubo hanyoyin magance rikicin jihar.
Me ya kamata a yi don magance matsalar?

Asalin hoton, NEMA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban ƙungiyar Amnesty International a Najeriya, Mallam Isa Sanusi ya ce abin da kawai zai kawo ƙarshen wannan rikici shi ne a kamo waɗanda ke aikata laifukan tare da yi musu hukuncin da ya dace.
To amma Dakta Kabiru Adamu, shugaban ƙungiyar Beacon Security mai bincike kan al'amarun tsaro a yankin Sahel, ya ce kawo ƙarshen matsalar jihar Benue na buƙatar amfani da jami'an tsaro da kuma dabaru na tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa ''akwai buƙatar gwamnati ta ƙara girke jami'an tsaro da ƙarfafa tattara bayanan sirri a jihar, sannan a tabbatar sun ci gaba da kasancewa a wurin domin magance duk wata barazana da za ta taso''.
Haka kuma Dakta Kabiru Adamu ya ce akwai buƙatar samar da ƙarin wuraren kiwo ga makiyaya, ta yadda za a kauce wa rikicinsu da manoma.
"Manufar hakan shi ne tabbatar da samar da wadatattun wuraren kiwo da hanyoyin da dabbobin makiyaya za su bi," In ji shi.
A bayan tsohon shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya ɓullo da irin wannan tsari na samar wa makiyaya wuraren kiwo, to sai jihohi da dama musamman na kudancin ƙasar sun yi watsi da shi.











