Jihohin Najeriya biyar da aka fi kashe mutane bayan hawa mulkin Tinubu

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Bola Tinubu ya cika shekara daya a kan mulki bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin shugaban Najeriya.
Ƙasar da ta kwashe shekaru tana fama da matsalar tsaro a kusan dukkanin yankunanta shidda.
Duk da cewa al'ummar yankunan da aka fi fama da matsalar tsaron sun yi fatan a samun sa’ida bayan karɓar sabuwar gwamnati, amma wasu na ganin cewa matsalar tamkar ƙara muni ta yi.
An ci gaba da fuskantar matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da yi wa mutane kisan gilla a jihohin arewa maso yamma, Boko Haram ta ci gaba da kai hare-haren sari-ka-noke da dasa nakiyoyi a arewa maso gabas, sannan an ci gaba da samun kashe-kashe na ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a kudu maso gabas.
Ko a washegarin ranar da aka rantsar da sabuwar gwamnati, ƴan bindiga sun kashe mutum 25 a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, ciki har da wani jagoran ƴan sa-kai.
Sai dai gwamnati na cewa tana bakin kokarinta.
Ta hanyar nazari kan rahotan kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a Najeriya, mun duba jihohi biyar na ƙasar da aka fi hallaka mutane tun bayan rantsar da gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu:
1- Jihar Borno

Asalin hoton, fb/Babagana Umara Zulum
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Borno na cikin jihohin Najeriya da suka fi cin karo da kalubalen tsaro a tarihin Najeriya sanadiyyar rikicin Boko Haram wanda ya samo asali a shekarar 2009.
Duk da nasarorin da dakarun gwamnati suka samu a tsawon shekarun yaki da kungiyar, har yanzu mayakan Boko Haram na nuna tasirinsu nan da can.
Shi ya sa ma jihar ta Borno ta yi zarra a yawan mutanen da aka kashe tun bayan hawan Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya.
Yawancin hare-hare da suka yi sanadiyyar kashe-kashe a jihar sun faru ne sanadiyyar ayyukan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi kamar ta Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati al Jihad da ISWAP, sai kuma wasu lokuta da dakarun Najeriya suka yi masarar murkushe mayakan na Boko Haram.
A jimilla, rahoton Beacon Consulting ya nuna cewa an kashe fararen hula 2,070 a jihar ta Borno tun daga watan Yunin shekara ta 2023 bayan hawa mulkin shugaba Tinubu.
Wani abin kuma shi ne yadda ƙungiyoyin masu ikirarin jihadin suka riƙa kai wa juna hari, lamarin da ya haifar da salwantar rayuka da dama tare da kara yawan adadin mutanen da aka kashe a jihar.
Misali, akwai harin da Jama’atu Ahlis Sunna lidda’awati wal jihad ta kai a ranar 19 ga watan Oktoba kan mayaƙan ISWAP a ƙaramar hukumar Abadam inda ta kashe mayaƙa 40.
Haka nan a ranar 14 ga watan Afrilun 2024 kungiyar ta Jama'atu Ahlis Sunnah ta kai wa mayaƙan ISWAP hari a ƙaramar hukumar Kukawa, inda ta kashe wasu mutunen 100.
Sai dai wasu daga cikin munanan hare-haren da ƙungiyar ta Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati al Jihad ta ƙaddamar kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba sun haɗa da wanda ta kai ranar 19 ga watan Agusta a yankin Maiduguri inda ta kashe mutum kimanin 100.
A ranar 15 ga watan Yunin na 2023 kuma mayaƙan Boko Haram sun kai hari kan wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Jere, inda suka kashe mutum 15.
Sai dai duk da haka sojoji sun samu nasara sosai a kan mayaƙan Boko Haram, kamar yadda sojin sama na Najeriya suka kashe mayaƙan ƙungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah guda 100 a ƙaramar hukumar Gwoza a ranar 11 ga watan Yunin shekarar 2023.
Ƙananan hukumomin da aka fi kashe mutane tsakanin wannan lokaci a jihar ta Borno su ne Marte inda aka kashe mutum 402, sai kuma Kukawa inda aka kashe mutum 347.
2- Jihar Zamfara

Asalin hoton, fb/Dauda Lawal
Ba abin mamaki ba ne yadda jihar Zamfara ta zamo ta biyu cikin jihohin da aka fi kashe fafaren hula Najeriya tun bayan kama mulkin Shugaba Tinubu.
Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da yadda jihar ta yi kaurin suna wajen fama da hare-haren ƴan bindiga masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa ba.
Za a iya cewa Zamfara ce jihar da ta fi kowace fama da wannan matsala tun bayan hawan Tinubu kan mulki.
‘Yan bindiga sun ci gaba da cin karensu babu babbaka - suna kisa a kauyuka da kan manyan hanyoyi, da kwashe mutane suna korawa daji tare da tarwatsa al’ummu daga matsugunansu.
Lamarin ya ci tura duk da cewa gwamnan jihar Dauda Lawal ya kaddamar da kungiyar ‘yan sa-kai ta Askarawan Zamfara, ga shi kuma karamin ministan tsaro na Najeriya, Bello Matawalle ya fito ne daga jihar.
Alƙaluman kamfanin Beacon Consulting sun nuna cewa an rasa ran fararen hula 761 daga 30 ga watan Yunin 2023 zuwa Mayun 2024.
Tun a cikin watan da aka rantsar da shugaban ƙasar ne aka ci gaba da kashe mutane, inda ƴan bindiga suka halaka mutum 25 a Maru, sannan wasu ƴan bindigan suka ƙara kashe mutum 25 a Maradun tare da sace yara mata sama da 30.
A ranar 20 ga watan Yulin 2023 kuma wasu mahara sun kashe sojoji 7 da wasu fararen hula 28 duk a ƙaramar hukumar ta Maru.
A ranar 11 ga watan Mayun 2024 an kashe mutum 49 a ƙaramar hukumar Anka, lokacin da ƴan bindiga suka kai farmaki a ƙauyukan Yar Sabaya da Farar ƙasa da Duhuwa.
Sannan a baya-bayan nan ranar 11 ga wannan wata na Mayu 2024 rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Anka ya yi sanadin kashe mutum 23.
Ƙananan hukumomi biyu da aka fi kashe mutane a jihar su ne Maru inda aka kashe mutum 329, sai Tsafe inda aka kashe mutum 112.
3- Jihar Filato

Asalin hoton, fb/Caleb Mutfwang
Filato jiha ce da ta yi kaurin suna a tashe-tashen hankula masu nasaba da rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma tsakanin ƙabilu.
An samu ƙaruwar irin waɗannan rikice-rikice gabanin babban zaɓen Najeriya na 2023 sannan hakan ya ci gaba da tasiri har bayan rantsar da sabuwar gwamnati.
Daga ranar da aka rantsar da Bola Tinubu zuwa watan Maris na 2024 an kashe fararen hula 560, kamar yadda alƙaluman kamfanin Beacon Consulting suka nuna.
Hari na farko mafi muni a jihar ta Filato bayan kama mulkin Tinubu shi ne wanda aka kai a ƙaramar hukumar Riyon, inda aka kashe mutum 21.
Haka nan ranar 18 ga watan Yuni an kashe mutum 22 a ƙaramar hukumar Mangu, aka kuma ƙara kashe mutum 15 a ƙaramar hukumar ta Mangu ranar 20 ga watan na Yuni sanadiyyar faɗa tsakanin wasu al’ummu.
Ƙananan hukumomin da aka fi rasa rai a cikinsu a jihar ta Filato cikin wannan lokaci su ne Bokkos inda aka kashe mutum 174, sai mai biye mata ƙaramar hukumar Mangu inda aka kashe mutum 149.
4- Jihar Benue

Asalin hoton, fb/Hyacinth Alia
Ta huɗu a cikin jerin ita ce jihar Benue da ke yankin arewa maso tsakiyar Najeriya inda aka kashe mutum 542.
Rikice-rikice a jihar Benue na kamanceceniya da na jihar Filato, inda ake samun taƙaddama tsakanin manoma da makiyaya ko kuma tsakanin ƙabilu masu hamayya da juna.
Tun kafin Tinubun ya cika mako guda aka ci gaba da kashe-kashe a jihar ta Benue, inda a ranar uku ga watan Yunin 2023 aka kashe mutum 25 a ƙaramar hukumar Katsina-Ala lokacin da wasu mahara suka far wa al'umma.
Haka nan a ranar 8 ga watan Yuli wasu maharan sun kashe mutum 24 a ƙaramar hukumar Ukum.
A baya-bayan nan kuwa wasu maharan sun kashe mutum 10 a ƙaramar hukumar Agatu, ranar 25 ga wannan wata na Mayun 2024.
Ƙananan hukumomin da aka fi asarar rai a jihar Benue a tsakanin wannan lokaci su ne Ukum inda aka kashe mutum 136, sai Agatu mai mutum 58 da kuma Gwer West ita ma mai mutum 58.
5- Jihar Kaduna

Asalin hoton, fb/Uba Sani
Kaduna ita ce jiha ta biyar da aka fi kashe mutane a Najeriya tun bayan kama mulkin Bola Ahmed Tinubu.
Kamar takwararta ta arewa maso yamma - jihar Zamfara, babbar matsalar da ta fi addabar Kaduna ita ce ta ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, sai kuma wasu lokutan da akan samu rikici tsakanin ƙabilu ko kuma manoma da makiyaya a kudancin jihar.
Matsalar garkuwa da mutanen ta hana al’umma sakat a waau yankunan kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Kajuru.
Alƙaluman kamfanin Beacon Consulting sun nuna cewa ana kashe mutum 400 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Mayun 2024.
A ranar ɗaya ga watan Janairu wasu ƴan bindiga suka kai hari a ƙaramar hukumar Birnin Gwari inda suka kashe ƴan sintiri 19, sannan duk a ranar wasu ƴan sa-kai ɗin suka kashe ƴan bindiga 40 a ƙaramar hukumar.
A ranar 18 ga watan Fabarairu kuwa wasu ƴan bindiga suka dirar wa wani ƙauye a ƙaramar hukumar Kajuru, inda suka kashe mutum 12 da ƙona gidaje kimanin 17.
Sannan wani abu da ya ɗauki hankalin duniya shi ne yadda wasu ƴan bindiga suka shiga ƙauyen Kuriga na ƙaramar hukumar Chikun a ranar 7 ga watan Mayun 2024 inda suka sace yara ɗalibai da dama, an ceto su daga baya, sai dai malami ɗaya ya rasa ransa.
A baya-bayan nan wasu mahara sun kashe mutum shida a ƙaramar hukumar Kajuru a ranar 19 ga wannan wata na Mayu.
Birnin Gwari ce ƙaramar hukumar da aka fi kashe mutane a cikinta a cikin shekara ɗaya ta mulkin Tinubu, inda aka kashe mutum 105.
Ƙaramar hukumar da ke biye mata a wannan harka ita ce Kauru mai mutum 46.
Duk da cewa gwamnatin Tinubu ta gaji matsalar tsaro ne daga gwamnatocin baya amma gazawar ta wajen yayyafa wa al’amarin ruwa abu ne da zai iya karya gwiwar al’umma.
Tabbas, ba abu ne mai yiwuwa ba a ce Tinubun ya kawar da ilahirin matsalar tsaron da ya gada cikin shekara daya ba, amma rashin ganin sauki a matsalar zai iya zama tamkar Larabar ba ta nuna cewa Juma’ar za ta yi kyau ba.
Saboda haka akwai bukatar gawamnatin ta shugaba Tinubu ta fito da tsare-tsaren da za su taimaka wajen warware wannan mugun kulli.







