Ƴan bindiga sun kori mutanen ƙauyuka 50 a Zamfara

Asalin hoton, Tsafe
Ƙauyuka aƙalla 50 ne hare-haren ƴan bindiga suka suka tilastawa jama'ar su yin ƙaura a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Wannan lamari ya tilastawa jama'ar waɗannan ƙauyuka neman mafaka a wurare daban-daban, lamarin da ya ƙara jefa su ckin mummmunan hali na rashin tabbacin yadda rayuwa za ta kasance.
A hirar sa da BBC, ɗan majalisar mai wakiltar Zurmi da Shinkafi a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Bello Hassan Shinkafi ya ce yanzu haka akwai mutane aƙalla 500 da ƴan bindigar suka yi garkuwa dasu daga ƙauyukan yankin.
Ɗan majalisar ya ce ƴan bindigar suna kai hari ƙauyukan mazaɓar tasa a kowanne lokaci, inda suke afkawa mutanen gari, su kashe na kashewa su kuma yi garkuwa da wasu.
Ya ce wannan lamarin ya tilastawa mutanen yin ƙaura daga mafi yawan ƙauyukan, yayin da waɗanda suka zaɓi ci gaba da zama ke fuskantar cin zarafi kala-kala daga maharan dake afkawa mutanen kodai da rana ko kuma da dare.
Ya ce ''Ba garin Gora kaɗai ba, Ƙaramar hukumar Zurmi ba ta zaune lafiya saboda waɗannan hare-hare, kuma duk lokacin da aka kai hari sai kaji an kashe mutane, kuma an tafi da wasu, ga kuma waɗanda aka jikkata.
ko a Knawa sun kashe mutum uku kuma sun ɗauki kusan mutum talatin da wani abu, a Nasararwa, ranar Litinin akwai wani gari da ake cewa Gidan Shaho, an kashe ƴan sanda biyu kuma da rana ba wani abu ba, kuma an jikka wasu mutane da dama. Yanzu haka ana neman a ƙididdige yawan mutanen da aka ɗauka ne.''
Hon. Bello Shinkafi ya ce duk da irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da sauran jami'an tsaro domin magance wannan matsala, akwai buƙatar ɗaukar ƙwararan matakan gyara kan wasu tsare-tsare da ake amfani da su wajen yaƙi da ƴan bindigar a jihar Zamfara.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce: ''Maganar gaskiya jami'an tsaron da ake dasu a wannan yanki ba su isa ba. Matsalar ma da ake ciki yanzu akwai sojojin da sun kai shekara takwas, tara har goma sha wani abu a cikin Zamfara waɗanda ya kamata ace an canza su.
An ɗauke su daga jihar nan an kawo wasu domin kada su saba da abin da ke faruwa a wannan jihar Zamfara, mun riga mun kai rahoto mun fada wa waɗanda ya kamata amma har yanzu shiru.''
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar tana nata ƙoƙarin wajen ceto mutanen da ƴan bindigar suka yi garkuwa dasu, inda ko a ƴan kwanakin nan an karɓo kusan mutum 200 daga hannun masu garkuwar, kuma ana fatan ci gaba da karɓo wasu.
Hon. Bello Shinkafi ya ce yanzu haka akwai ƙudirin da ya gabatar a zauren majalisar wakilai, inda ya nemi a tura ƙarin jami'an tsaro na soji da ƴan sanda zuwa mazabar tasa domin gudanar da aikin tabbatar da tsaro da kuma ƙwato mutanen da ƴan bindigar ke tsare da su.
Jihar zamfara na daga cikin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya dake fama da rashin tsaro sabboda ayyukan mahara masu ɗauke da makamai, waɗanda ke kai farmaki ƙauyuka da garuruwa su yi garkuwa da mutane, kuma a lokuta da dama suna kashe wasu, su kuma jikkata wasu.
Gwamnatin jihar ta ce tana bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalar, yayin da itama gwamnatin tarayya ke cewa tana nata ƙoƙarin amma duk da haka ana ci gaba da samun hare-haren ƴan bindigar.










