Abubuwan da na nema daga wajen shugabannin tsaro - Gwamnan Zamfara

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Abubuwan da na nema daga wajen shugabannin tsaro - Gwamnan Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara a arewacin Najeeriya, Dauda Lawal, ya ce ya gabatar wa shugabannin tsaron ƙasar sabbin buƙatu da zimmar daƙile hare-haren 'yan fashin daji a jihar tasa.

A ranar Talata ne gwamnan ya je birnin Abuja, inda ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, da Nuhu Ribadu mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

Haka nan, gwamnan ya faɗa wa BBC cewa bincikensu ya gano cewa ana kwashe wasu daga cikin sojojin da ke Zamfara tare da sauya musu wurin aiki, inda ya ce ya nemi a ƙara yawansu a jihar.

'Zamfara na cikin tsaka mai wuya kan hare-haren 'yan fashin daji'

A hirarsa da BBC ya ce su na bakin kokari domin magance matsalar, dalilin da ya sa ya yi takakkiya domin ganawa da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, da shugaban ma'aikatan tsaro Janaral Christoper Musa duk kan halin da Zamfara ke ciki.

''Na koka musu kan kalubalen da muke fuskanta a Jihar Zamfara, kamar yadda aka sa ni gwamnatin tarayya ita ke da sojoji da 'yan sanda, dan haka muk bi ko ta ina domin ganin an kawo sauki kan halin da ake ciki.

Abin da ya ke karkashin iko na shi ne 'yan sa kai da muka dauka domin taimakawa matsalar tsaro.

Abu da ya shafi tsaro ba za ka ce yanzu-yanzu za ka shawo kan matsalar ba amma alamun da muke gani Askarawan Zamfara na bakin kokarinsu,'' in ji Dr Dauda.

Ya kara da cewa a shirye ya ke ya yi duk abin da zai iya domin ganin matsalar tsaro ta kau a jiharsa.

Ya ce a ganawar da ya yi da shugaban ma'aikatan soji ya shaida masa su na bukatar karin sojoji a Zamfara saboda wadanda suke da su ma ana ta kwashe su ana maidawa wasu sassan Najeriya.

''Dauke sojoji daga jihar Zamfara akai su wasu wuraren bai kamata ba, mu na kuma bukatar kayan aiki kamar motocin jami'an tsaro da ya kamata a ce jihar mu an bata da yawa amma babu su, na koka kan hakan.

Na kuma bukaci ganin shugaban Najeriya domin in fada masa dukkan matsalolin da jiharmu ke fuskanta, da kuma fatan zai yi mai yiwu wa domin samun sauki a wannan yankin na mu.''

Ya kuma jajantawa al'ummar Tsafe da sauran wuraren da a baya-bayan nan 'yan bindiga suka kai munanan hare-hare, da tabbacin yana bakin kokari domin magance matsalar, da addu'ar neman talafi daga Ubangiji domin samun zaman lafiya a jihar Zamfara.

A ɗan tsakanin nan jihar Zamfara ta kara fadawa cikin matsalar tsaro, inda 'yan bindiga ke ci gaba d kai munanan hare-hare da sace mutane domin neman kudin fansa, da kashe-kashe da far wa dukiyar mutane.

Har wa yau, matsalar 'yan bindigar ta janyo manoma sun gagara noma a jihar, a wani bangaren kuma baryin na kwashe dan abin da suka tanada na kayan abinci.