Yadda sabon rikici a Filato ya janyo saka dokar hana fita a Mangu

Gwamnatin Filato

Asalin hoton, @CalebMutfwang

Gwamnatin Filato da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita a ƙaramar hukumar Mangu bayan ɓarkewar sabon rikici a yankin.

Gwamnan jihar Caleb Mutfwang ne ya ayyana dokar hana fita ta sa'o'i 24 a faɗin Mangu a ranar Talata.

Ana tunanin rikicin ƙabilanci ne ya ɓarke a Mangu inda aka yi ƙone-ƙone ciki har da gidaje.

Rikici ya sake kunno kai ne a ƙaramar hukumar tun a shekarar da ta gabata wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi na miliyoyin naira.

Ana fargabar rikicin na yanzu yana neman rikiɗewa ya koma na addini, duk da cewa hukumomi ba su bayyana ɓangaren da ya fara kai hari ba.

Filato, jiha ce da ta yi ƙaurin suna wajen rikice-rikice masu alaƙa da ƙabilanci da addini da kuma hare-haren ‘yanfashin daji, inda ko a watan jiya wasu hare-hare suka yi sanadin mutuwar kimanin mutum 200.

Me ke faruwa a Mangu?

Daraktan yaɗa labarun gwamnan jihar Filato, Gyang Bere ya shaida wa BBC cewa a ranar Talata ne wani sabon rikici ya kaure a ƙaramar hukumar.

Ya bayyana cewa an kai hari a ɓangarori daban-daban na ƙaramar hukumar.

Jim kaɗan bayan ɓullar labarin rikicin a ƙaramar hukumar ta Mangu, an ga hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta, waɗanda BBC ba ta tabbatar da sahihancinsu ba, suna nuna yadda mutane ke gudu yayin da hayaƙi ke fitowa daga wasu gine-gine.

A yanzu haka dai hukumomi sun ce babu tabbas ko an samu rasa rayuka sanadiyyar rikicin ko kuma a'a.

Sai dai daraktan yaɗa labarun na gwamnan jihar ya tabbatar da cewa an yi ƙone-ƙone a ƙauyuka daban-daban.

Me gwamnatin Filato ta ce?

A sanarwar da gwamnatin Filato ta fitar ta bayyana damuwar cewa wasu mutane har yanzu na son haddasa rikici a jihar duk da ƙoƙarin gwamnatoci na kawo ƙarshen ayyukan waɗanda gwamnatin ta kira "‘yan ta’adda."

Gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya ce ya ɗauki matakin sanya dokar hana fita ne a Mangu bayan tuntubar hukumomin tsaro, sannan kuma an ɗauki matakin ne saboda dalilai na taɓarɓarewar tsaro a yankin.

Ya ce matakin zai fara aiki ne nan take, kamar yadda sanarwar da Gyang Bere, daraktan yada labarai da harkokin al’umma na jihar Filato ta bayyana.

Sai dai matakin bai shafi mutanen da ke aiki na musamman ba, kamar jami’an lafiya da ƴanjarida da jami’an tsaro waɗanda aka amince su yi zirga-zirga a yankin na Mangu.

Gwamnatin ta yi gargaɗi da dukkanin mazauna karamar hukumar Mangu su kiyaye bin doka da oda tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kan da ya dace musamman wajen bayar da bayanai domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Rikicin 'yan majalisa a Filato

Rikicin Mangu na zuwa, yayin da a Jos, babban birnin jihar ta Filato, aka samu hatsaniya a majalisar jihar inda 'yan jam'iyyar PDP da kotu ta kora suka mamaye harabar majalisar da magoya bayansu.

'ƴansanda sun harba wa tsofaffin yan majalisar su 16 hayaki mai sa hawaye bayan da suka yi yunƙurin komawa zaman majalisar.

'Yansanda da sauran jami'an tsaro sun mamaye harabar majalisar jihar da Fadar gwamnati tare da hana 'yan majalisar shiga.

Tsofaffin 'yan majalisar karkashin jam'iyyar PDP da kotun daukaka kara ta kora a watan Nuwamba sun yanke shawarar komawa zauren domin ci gaba da gudanar da zama bayan hukuncin kotun koli da ya tabbatar da gwamna Mutfwang a matsayin gwamnan jihar.