Tinubu ya yi tir da harin Filato wanda aka kashe 'fiye da mutum 140'

President Bola Tinubu

Bayanai na ci gaba da fitowa fili kan girman hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai tun daga ranar jajiberen Kirsimeti kan garuruwan jihar Filato 20, inda ƙungiyar Amnesty ta ce zuwa yanzu an tabbatar da kashe fiye da mutum 140.

Akwai kuma ƙarin ɗaruruwan mutane ne da aka ji wa raunuka. An kwantar da wasu daga ciki a babban asibitin gwamnati na Barikin Ladi da kuma Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jos, inda suke jinya.

Daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Mista Gyang Bere ya ce har yanzu ba su iya tabbatar da haƙiƙanin alƙaluman mutanen da aka kashe ba tukunna.

A cewarsa, ko cikin daren Litinin, an sake gano gawawwakin wasu mutane da aka kashe.

Tuni dai jami'an tsaro da 'yan bijilante na yankin da kuma maharba suka bazama cikin dazukan kusa don neman mutanen da suka ɓata a cewar hukumomi.

An sa wawa kan gidaje da gonaki, wasu kuma an ƙone su yayin farmakin na cikin dare, kamar yadda shaidu sun faɗa wa wakilin BBC.

Hukumomi sun ce 'yan fashin daji ne suka kai hare-haren.

Hare-haren sun faru ne a cikin daren Lahadi da kuma washe gari ranar Kirsimeti a ƙauyukan da ke ƙananan hukumomin Mangu da Bokkos da kuma Barikin Ladi.

Caleb Mutfwang

Asalin hoton, Governor Plateau state/Facebook

Bayanan hoto, Gwamnatin jihar Filato ta ce har yanzu ba ta iya tantance haƙiƙanin yawan mutanen da aka kashe ba

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya yi alla-wadai da hare-haren sannan ya ci alwashin shawo kan irin wannan farmaki da jihar ke fama da su.

Filato, jiha mai yawan ƙabilu da addinai daban-daban a tsakiyar Najeriya, ta tagayyara sakamakon rikice-rikicen ƙabilanci da addini da kuma na manoma da makiyaya tsawon shekaru.

Wakilin BBC ya ce faɗin ƙasar Filato da ƙarancin tashoshin jami'an tsaro musannan a yankunan karkara na nufin mahara irin na jajiberen Kirsimeti za su iya arcewa kafin isar dakarun tsaro.

Hare-hare a yankin tsakiyar Najeriya sun ɗan ragu a wannan shekara idan an kwatanta da bara, cewar wata gidauniya mai tattara alƙaluman hare-hare wadda da Ingilishi ake kira Armed Conflict Location and Event Data (Acled) Project.

Sai dai yanzu ana fargabar cewa wannan hari na baya-bayan nan yana iya sake haddasa zaman ɗar-ɗar da hare-haren ramuwar gayya.

Plateau attack scene

Asalin hoton, Amnesty International

Rikici yana ƙara ruruwa ne sanadin tashe-tashen hankulan siyasa da batutuwan addini da gaba a tsakanin juna da yaɗa labaran ƙarya da gwagwarmayar samun 'yanci da iko a kan albarkatun ƙasa da kuma al'amuran sarauta.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi alla-wadai da "miyagun hare-haren na Filato, kuma ya ba da umarnin a gaggauta kamo masu hannu".

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman Ajuri Ngelale ya fitar ta ce Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta kutsawa ko'ina a yankin don kamo masu hannu a hari.

Shugaban ya kuma ba da umarnin a gaggauta kai kayan agaji don mutanen da suka kuɓuta daga hare-haren tare da yi wa waɗanda suka jikkata magani.

Da yake miƙa alhini ga gwamnati da al'ummar jihar Filato, Shugaba Tinubu ya bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa waɗanda suka kai harin ba za su tsira ba.