Yaushe za a kammala shari’o'in zaɓen gwamnoni a Najeriya ?

Asalin hoton, SUPREME COURT
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
A ƙarshen makon jiya ne, kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta yanke hukunci kan wasu shari'o'in zaɓen gwamnoni waɗanda a ciki wasunsu suka zo da matuƙar ban mamaki a ƙasar.
Kotun ta soke nasarar gwamnonin jam'iyyun adawa guda uku, ta kuma bai wa jam'iyya mai mulki nasara.
Shari'o'in sun haɗa da na zaɓen gwamnan jihar Kano, inda kotun ta sake tabbatar wa NasiruYusuf Gawuna nasarar da ya samu a kotun farko, tare da soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sai kuma jihar Zamfara inda kotu ta ayyana zaɓen gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammala ba, kuma ta ba da umarnin sake zaɓe a ƙananan hukumomi guda uku - Muradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum.
A jihar Plateau ma, kotu ta bai wa jam'iyya mai mulki ta APC nasara, inda ta soke zaɓen Gwamna Caleb Mutfwang.
Babban abin da ya kawo ka-ce-na-ce shi ne, jihohin duka na 'yan adawa ne, PDP babbar jam'iyyar adawar Najeriya, na da gwamnonin Zamfara da Filato, yayin Kano ke hannun NNPP. Kuma zuwa Litinin 20 ga watan Nuwamba, babu jiha ko ɗaya ta APC da kotun ɗaukaka ƙarar ta soke nasarar zaɓenta, duk da yake tana da sauran shari'o'i a gabanta.
Zuwa yaushe doka ta bayar na kammala shari'a?

Asalin hoton, Facebook/Abba/Lawal
"Abin da doka ta tanada shi ne dole ne a yanke duk wani hukunci da ya shafi maganar zaɓe a cikin kwana 180 daga ranar da aka ayyana sakamko," a cewar Barista Audu Bulama Bukarti, wani lauya ɗan Najeriya mazaunin Birtaniya.
Ya ce "an yi haka ne saboda a baya akan ɗauki shekaru kafin yanke hukunci, har ma mutum ya kusa sauka daga kan mulki. Domin magance hakan ne doka ta tanadi kwana 180.
Ya ce idan aka je ga kotun ƙoli kuwa, tana da kwana 60, wato kimanin wata biyu, daga ranar da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci, na sauraron ƙarar da aka gabatar mata da kuma yanke hukunci.
"Tilas ne a cikin kwana 60 kotun ƙoli ta gama komai a kan ƙara, ta kuma yanke hukunci," in ji Bukarti.
Ya ce doka ta bai wa waɗanda ke son ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli kwana 14 su gabatar da sanarwar ɗaukaka ƙararsu, akwai dokar da ta ce kwana 21, amma ya ce zai fiye musu alheri su gabatar da buƙatar ɗaukaka ƙararsu cikin kwana 14.
"Sakataren kotun ɗaukaka ƙara yana da kwana goma wajen haɗa takardun duk abin da ya faru a kotun, ya tura wa kotun ƙoli, daga nan za a bai wa masu ɗaukaka ƙara tsawon kwana bakwai domin rubuta dalilai da suka sanya suka ɗaukaka ƙara.
"Waɗanda aka yi ƙararsu kuwa suna da kwana biyar domin amsa jawaban masu ɗaukaka ƙara," in ji Bukarti.

Asalin hoton, Bulama Bukarti
Ya ce idan aka je kotun ƙoli kwana ɗaya kawai za a ware, inda duk ɓangarori za su gabatar da jawabansu ga alƙalai, daga nan kawai sai ita kuma ta yanke hukunci.
Ya ce idan aka tafi kan yadda doka ta tsara kwana ɗaya za a zauna kuma a yanke hukunci a kotun ƙoli, inda ya ce idan ba ta yanke hukunci cikin kwana 60 ba, to hukuncinta ya zama "aikin banza", kuma duk abin da kotun ɗaukaka ƙara ta faɗa da shi za a yi aiki.
Abin da kotun ƙoli ke la'akari da shi kafin hukunci
Barista Audu Bulama Bukarti ya ci gaba da cewa kotun ƙoli na la'akari da kundin shari'ar da aka gabatar mata daga kotun ɗaukaka ƙara ne, ganin cewa an fara shari'ar ne daga kotun ƙorafin zaɓe.
Bukarti ya ce shaidun da aka gabatar a kundin da jawaban da alƙalai suka rubuta lokacin da ake shari'a da kuma dailai na ɗaukaka ƙara.
"Abu guda uku masu muhimmanci da kotun ƙoli za ta duba su ne sanarwar ɗaukaka ƙara, da jawaban lauyoyin duka ɓangarori, da kuma kundin shari'ar wato abin da ya faru a kotun ƙasa," in ji Bukarti.
Ya ce idan ba tura ce ta kai bango ba, kotun ƙoli ba ta karɓar sabuwar shaida, ba za a kuma kawo sabuwar takardar da ba a shigar da ita a kotunan ƙasa ba. Ba za ta kuma saurari wani jawabi na daban da babu shi a kotun ƙasa ba.
Me zai faru idan aka samu bambancin ra’ayi tsakanin alƙalai?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bulama Bukarti ya ce ana samun bambacin ra'ayi tsakanin alƙalai a kotun ƙoli.
Ya ce alƙalai biyar ne ko goma ke zama domin yanke hukunci a kotun.
Bukarti ya ce idan aka yi irin wannan zama, doka ta ɗora wa kowanne alƙali nauyin faɗar ra'ayinsa ko fahimtarsa, ko kuma hukuncinsa a kan ƙarar da ke gabansu, wanda ra'ayi zai iya zuwa daban-daban.
"Doka ta tanadi cewa idan alƙalan za su zauna dole su zama biyar ko bakwai ko uku ko ma tara, kuma babu wanda zai ce ba ya nan, don haka kowa zai faɗi ra'ayi, inda ɗaya ɓangare zai rinjayi ɗaya.
"Idan su biyar ne, misali uku suka ce sun bai wa masu ɗaukaka ƙara gaskiya, biyu kuma suka ce sun bai wa wanda aka ɗaukaka ƙara a kansu gaskiya, to waɗanda mutum uku suka goyi bayansu su suka yi nasara," in ji Bukarti.
Ya ce an taɓa samun irin haka a baya, inda alƙali huɗu a kotun ƙoli suka goyi bayan marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar'adua lokacin da Buhari ya kai ƙararsa, sannan uku kuma suka goyi bayan Buhari, inda ya ce hakan ne ya sa marigayi Yar'adua ya samu nasara saboda alƙalai huɗu da suka goya masa baya, ba shi Buhari da uku suka mara wa baya ba.
'Kotun koli ba ta sake duba hukunci'
Har ila yau, Barrister Bukarti ya ce kotun ƙoli ba ta sake duba hukunci idan ta yanke shi, duk da yakea doka ta ba bai wa kotun damar yin hakan idan ta yi tuntuɓen harshe, ko kuma inda hukuncinta ya ci karo da doka.
"A rubuce akwai wannan damar, amma a aikace kotun ƙolin Najeriya, ba ta sake buɗe irin wannan kofa, musamman a harkar siyasa idan aka buɗe kofar duk wanda ya yi rashin nasara, zai iya komawa ya ɓata musu lokaci ya ce yana son a sake ziyartar hukuncin.
"Saboda haka kotun ƙoli ba ta sake buɗe irin wannan kofar," in ji Bukarti.
Ya ce ko da kuskure suka yi wajen yanke hukunci, tun da su ne ƙarshe a tsarin shari'ar Najeriya, sai dai mutum ya ja Allah ya isa, ya bar wa Allah maganar.











