Ba mu da alƙaluman mutanen da aka kashe a Mangu - Gwamnatin Filato

Asalin hoton, PLATEAU STATE GOVERNEMNT
Ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a yankin ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Filato, bayan wani hari da ake zargin cewa ya haifar da asarar rayuka sama da goma.
Lamarin ya haifar da ƙaƙaba dokar hana zirga-zirga a ƙaramar hukumar, karo na biyu a cikin wata uku.
Jihar Filato ta daɗe tana fama da rikice-rikice masu alaƙa da ƙabilanci da kuma addini.
Ko a watan Mayu, rahotanni sun bayyana cewa rikicin da aka samu a yankin na Mangu ya yi sanadiyyar gwamman rayuka.
A wata tattaunawa da BBC, mai magana da yawun gwamnan jihar Filato Gyan Bere, ya ce har yanzu gwamnati ba ta samu rahoton yawan mutanen da aka kashe a rikicin na baya-bayan nan ba.
“Abin da na sani shi ne mutanen Mangu na cikin hali maras kyau.”
Tun farko dai shugabannin ƙungiyar Fulani makiyaya sun yi iƙirarin cewar sun ƙirga gawar mutum 15 da aka kashe, sannan an ƙona gidaje 78.
Amma a tattaunawar tasa da BBC, Mista Berre ya bayyana cewa gwamnati ba za ta iya tantance gakiyar adadin waɗanda aka kashe da ƙungiyoyi ke iƙirari ba.
A cewarsa "Ba zan iya cewa abin da shugabannin Fulani ke cewa gaskiya ne ko ƙarya ba domin ba mu da wannan tabbacin."
“Ni na san da cewa ana kashe-kashe a Mangu, ana yi wa mutanen kwantar bauna ana kashe su.”

Gwamnati ta tura ƙarin jami’an tsaro

Asalin hoton, Getty Images
Mai magana da yawun gwamnan ya ce a yanzu gwamnati ta tura ƙarin dakarun tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Ya ƙara da cewa “muna roƙon al’ummar yankin da su rungumi zaman lafiya”, kuma yunƙurin da gwamnati ke yi ke nan na ganin an samu zaman lafiya.
Wannan ne karo na biyu da gwamnati ke ayyana dokar hana zirga-zirga a yankin na ƙaramar hukumar Mangu a cikin wata biyu.
NYSC ta ɗauke sansanin horas da matasa daga Mangu
Hukumar kula da shirin matasa masu yi wa ƙasa hidima ta Najeriya ta sanar da sauya wa sansanin horas da ƴan yi wa ƙasa hidima daga ƙaramar hukumar ta Mangu zuwa Jos ta kudu.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa ta shafinta na facebook, NYSC ta ce "Ana sanar da matasa masu shirin hidimar ƙasa na Kashi na B, Tawaga ta ɗaya, cewar an sauya inda za a yi musu horo daga sansanin horas da matasa na Mangu, zuwa gidauniyar Waye, da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu."
Sanarwar ta buƙaci matasan da su hallara a sabon adirenshi da aka bayar domin samun horo a kwanakin da aka ware.

Asalin hoton, other
A cikin watan Mayu ma gwamnatin Filato ta ƙaƙaba dokar hana fita a yankin na Mangu, bayan wasu hare-hare na ƴan bindiga.
Mutane da dama sun tsere bayan wani hari da aka kai kan al'ummar yankin da ya haddasa mutuwar gommai sannan aka binne wasu a wani wawakeken kabari.
Mazauna Mwaghavul, al'ummar da ta yi fice a harkar noma a ƙaramar hukumar Mangu sun shaida wa BBC cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyukansu inda suka buɗe wuta kan mutane tare da cinna wa gine-gine wuta.
Shugaban al'ummar Fulani a yankin, Adamu Usman shi ma ya faɗa wa BBC cewa mutum 30 cikin al'ummar yankinsa aka kashe.
Jesse Jwanle, wani rabaran a wani coci da ke ƙauyen Gaude ya ce an kashe ɗaya daga cikin mambobin majami'arsa, an ƙona gidansa da cocin.







