Ana bincike kan 'likitan' da ake zargi da cire wa marasa lafiya ƙoda a Jos

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
An shiga ruɗani da tashin hankali a birnin Jos, na tsakiyar Najeriya, bayan kama wani 'likita' da 'yan sanda suka yi, bisa zargin cire wa marasa lafiyansa ƙoda a lokacin da suka je asibitinsa don yi musu aiki.
Mai magana da yawun rundunar jihar ya tabbatar da cewa sun kama Noah Kekere tare da wasu likitoci guda biyu da ake zargin sun yi aiki tare da shi.
"Mun kama likitan da ake zargi da cire ƙodar, muna ci gaba da bincike a kansa kuma da zarar mun kammala za mu kira ku, domin ku shaida," kamar yadda DSP Alfred Alabo ya faɗa wa manema labarai.
Sai dai, daga bisani 'yan sanda sun ce sun kai wanda ake zargin asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa domin a duba lafiyarsa.
Mutumin ya riƙa aiki ne a asibitinsa mai suna Murna Hospital and Clinic da ke kan titin 'Yan Shanu zuwa Nasarawa Gwon a birnin Jos.
Noah Kekere, a cewar rahotanni, ya fara nuna "alamun hauka" bayan ya shiga hannun 'yan sanda a birnin Jos ranar Laraba.
Kwamishinan Lafiya na Filato, Dr Cletus Shurkuk ya tabbatar da BBC cewa, suna sane da wannan al'amari da ake zargin Noah Kekere.
Ya ce sun kuma samun cewa an kai 'likitan' zuwa sashen kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa na asibitin koyarwa na Jami'ar Jos, inda yake ƙarƙashin kulawar 'yan sanda.
A gefe guda kuma, ƙarin wasu mutanen sun fara fitowa suna zargin Mista Kekere da cire musu ƙoda, kamar yadda Kamaru Busari - mijin Kehinde Busari, wadda ta zargi likitan da cire mata ƙoda ya faɗa wa BBC.
Kamaru Busari ya ce sai da matarsa ta yi wata huɗu, ba ta iya tashi, tun lokacin da likitan ya yi mata wani aikin tiyata a watan Janairun 2018.
Yadda likitan ya cire wa matata ƙoda - Kamaru
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana zargin Kekere ya shafe tsawon shekaru yana aiki a matsayin likita a birnin na Jos.
'Yan sanda sun kama likitan da ake zargi, Noah Kekere, ranar Laraba bayan wasu mazauna unguwar Nasarawa sun kai wa 'yan sanda ƙorafin cewa yana cire wa marasa lafiya ƙoda.
Sun shigar da ƙorafin ne bayan wani ɗan kasuwa mai suna Kamaru Busari ya zargi likitan da cire wa matarsa Kehinde ƙoda ta ɓangaren dama.
Ya ce Kekere ya yi wa matarsa tiyata karon farko ranar 26 ga watan Janairun 2018.
"Ya shafe kusan awa takwas yana yin aikin tare da wasu likitocin a Jos," in ji shi. "Tun daga lokacin na dinga kaiwa ina kawowa game da rashin lafiyarta. Na kashe kuɗi sosai."
Bayan sun yi masa ƙorafin rashin lafiyar a shekarar da ta gabata, sai likitan ya ce zai sake yi mata tiyata, a cewar Kamaru.
"Ba mu yarda an yi ba, saboda bayan tiyatar farko da aka yi sai da ta yi wata huɗu ba ta iya tashi, sanadin tsananin ciwo da azabar da ta yi fama da ita. Mun tsorata sosai."
Bayan haka ne kuma likitocin suka rubuta masa wasu ƙwayoyin magani da zai dinga saya a madadin aikin da aka fasa yi mata.
"Maganin farko da na saya naira 48,000 ne. Ta ɗan samu sauƙi sosai da ta sha, ganin haka sai na ce to a ci gaba da sayen maganin."
Ya ci gaba da cewa cikin mako biyu da suka wuce ne matar tasa ta yi ƙorafin cewa ta gaji da shan maganin, abin da ya sa suka yanke shawarar zuwa asibitin koyarwa na Jami'ar Jos ranar Litinin, 4 ga watan Agusta.
"Sun faɗa wa matata cewa an cire mata ƙoda ɗaya ta ɓangaren dama. Sun tabbatar da cewa ba a haka aka haife ta ba, cire mata aka yi ba da jimawa ba."
'An nemi ba mu kuɗi don mu yi shiru'
Bayan asibiti sun gano cewa an cire wa Kehinde ƙoda, likitan ya musanta batun yana mai cewa ƙila a haka aka haife ta.
"Ya ce matuƙar muna son mu tabbatar, sai mu je wani asibitin daban. Ni kuma na ce masa ya zaɓo mana asibitin da yake so mu je," a cewar Kamaru Busari.
Mijin matar ya yi zargin cewa an yi yunƙurin ba su cin hanci don su yi shiru da maganar.
Sai dai a cewar Kamaru, bai yarda da wannan tayi ba, don haka ya sake garzaya wa ofishin 'yan sanda.
Ba likita ba ne - NMA
Jim kaɗan bayan kama shi bayanai iri-iri na ci gaba da fitowa a shafukan sada zumunta game da ƙwarewar mutumin da ake zargi.
Wasu mazauna birnin Jos sun ce 'likitan' da ake zargu bai karanta fannin likitanci ba.
Shugaban ƙungiyar likitocin Najeriya ta Nigerian Medical Association (NMA) reshen jihar Filato, Dr Bapigaan William Audu, ya ce bayanan da suke da su, sun nuna cewa mutumin ba likita ba ne.
"Economics [fannin tattalin arziki] ya karanta. Binciken da muka gudanar ya nuna cewa [Noah Kekere] ba likita ba ne, kuma ba ɗan ƙungiyarmu ba ne," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Sai dai ya ce binciken cire ƙoda ko akasin haka, ba aikinsu ba ne amma ranar Talata za su wallafa cikakken rahoton binciken da suka yi a kan Mista Noah Kekere.











