Yadda wani mutum ya cinna wa kansa wuta a jihar Filato

.

Asalin hoton, Nigerian Police

Rahotanni a Najeriya na cewa wani mutum da ake zargin ya cinna wa kansa wuta ya mutu, jim kaɗan bayan an garzaya da shi asibiti.

Lamarin dai ya afku ne a birnin Jos na jihar Filato inda wasu shaidu suka ce mutumin mai suna Muhammad Ibrahim mai kimanin fiye da shekaru talatin ya cinna wa kansa wuta ne bayan wata rashin jituwa da ya samu tsakaninsa da mahaifinsa da ƴan uwansa.

Wani Malam Hassan Umar wanda yake sana'a a kusa da wurin da lamarin ya faru a Unguwar Zaria Crescent cikin wani lambu a birnin Jos, ya shaida wa BBC cewa sun hangi Muhammad Ibrahim wanda magidanci ne da ƴaƴa biyu yana shan wani abu a galan.

A cewarsa, daga baya sai suka ga wuta ta kama sai suka nemi ruwa ba su samu ba, suka samu ruwan leda shi ma ya ƙi kashe wutar, sai dai a kwata suka yi amfani da shi suka kashe wutar, ko da suka kashe wutar ta riga ta ƙona shi.

BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun 'yan sanda na Filato ASP Ubah Gabriel, domin jin ƙarin bayani kan lamarin, sai dai ya aiko mana da rubutaccen saƙo cewa har yanzu suna kan tattara bayanai don haka zai nemi mu.

Haka ma bayan mun tuntuɓi ɗan uwan mutumin ya ce mu yi haƙuri ba zai iya magana ba, amma ya shaida mana cewa yayansa mutum ne mai zuciya da kafiya.

Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani game da abin da ya sa ya ƙona kansa sai dai wata majiya ta tabbatar wa BBC da cewa lamarin yana da nasaba taƙaddama tsakaninsa da mahaifinsa inda magidancin ya yi zargin mahaifin da cewa ya hanashi samun nasara a rayuwa.

Rikicin dai yayi ƙamari ne bayan a daren Laraba rigima ta kaure da mahaifin har ma wasu bayanai ke cewa ya lakaɗawa mahaifin nasa duka, lamarin da yayi sanadiyar karyewar mahaifin a hannu.

Hakan ya sa 'yan uwansa suka lakaɗama masa dukan tsiya a cewar majiyarmu.