Harin jirgin sama a Kaduna: 'An kashe ƴan'uwana 34'
Harin jirgin sama a Kaduna: 'An kashe ƴan'uwana 34'
Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta ce "kuskure ne" harin da wani jirginta maras matuƙi ya kai a ƙauyen Tudun biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Ana ƙiyasin cewa mutane da dama ne suka rasu sanadiyyar harin, sai dai har yanzu babu takamaiman alƙaluma daga gwamnati ko hukumomin tsaro.



