Cutuka bakwai da suka fi kwantar da ƴan Najeriya a asibiti

Cutuka

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya, NARD, ta ce akwai wasu cutuka waɗanda su ne kan gaba wajen kisan ƴan ƙasar.

Ƴan Najeriya dai na fama da matsaloli na lafiya iri-iri da ke janyo mace-mace ƙari a kan rashin ingantaccen tsarin lafiya a ƙasar mai yawan al'umma fiye da miliyan biyu.

A shekarar 2024 kimanin likitoci 4,000 ne suka bar ƙasar zuwa ƙasashen waje bisa dalilin ƙarancin albashi da rashin kayan aiki.

A shafinta na X, ƙungiyar ta lissafa manyan cutuka guda bakwai da ta ce su ne suka fi addabar ƴan ƙasar.

Maleriya

Ƙungiyar ta NARD ta ce kusan dukkan ƴan Najeriya na fuskantar zazzaɓin maleriya wani lokacin ba ma sau ɗaya ba a shekara.

Alƙaluma daga hukumar lafiya ta duniya, WHO a 2023 sun nuna cewa kaso 40 na yawan masu fama da cutar maleriya na duniya.

Ƙididdigar hukumar ta WHO ta kuma nuna cewa yawan mutanen da maleriya ke kashewa a Najeriya sun kai kaso 46 na waɗanda cutar ke kashewa a faɗin duniya.

Ciwon suga (Diabetes)

Ƙungiyar ta NARD a shafin nata na X ta ce kaso 14.9 na marasa lafiya da ake kwantarwa a asibitocin Najeriya masu fama da larurar ciwon suga ko Diabetes Malitus.

Alƙaluman hukumar lafiya ta duniya, WHO sun nuna cewa kaso 4.3 na ƴan Najeriya na fama da cutar suga, duk da wasu rahotanni sun nuna masu cutar sun kai kaso 5.7 zuwa 11.

Ƙungiyar masu cutar Suga ta Najeriya ta ce matasan ƙasar kimanin miliyan uku ne ke fama da cutar ta Suga a faɗin ƙasar.

Yayin bikin ranar masu cutar suga a Najeriya a 2024, shugaban ƙungiyar masu fama da cutar na Najeriyar, Dr Ejiofor Ugwu ya ce ƴan Najeriya 30,000 zuwa 40,000 ne ke mutuwa a kowace shekara sakamakon cutar suga.

Hawan jini da Bugun jini

Ƙungiyar ta likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya, NARD ta ce cuta ta uku da ke kwantar da ƴan ƙasar ita ce ta hawan jini wadda take kwantar da kaso 9.2 na marasa lafiya a asibitoci.

Cuta mai alaƙa da hawan jini ita ce ta bugun jini wato stroke wadda ƙungiyar ta ce kaso 7.8 na waɗanda ke kwanciya a asibiti.

Tsayawar zuciya

Ƙungiyar ta NARD ta ce kaso 9.2 na waɗanda ake kwantarwa a asibitocin Najeriya na kwanciyar ne sakamakon gazawar aikin da zuciyarsu ke yi.

Tsayawar zuciya na daga cikin manyan matsalolin kiwon lafiya a Najeriya inda masu cutar suka kai kaso 5.8 zuwa 15.5 na yawan ƴan ƙasar da ke fama da cutuka.

Matsalar ƙoda

Kaso 11.8 na marasa lafiya da ake kwantarwa a asibitocin Najeriya na fama da cutar ƙoda ne musamman waɗanda ƙodar ke daina aiki.

Alƙaluma daga hukumomin lafiya da dama na Najeriya sun nuna cewa matsalar ƙoda ta kasance babbar matsalar kiwon lafiya a ƙasar, inda take kama kaso 1.6 zuwa 26 na ƴan ƙasar.

Larurar hawan jini ce babbar matsalar da ke haddasa illa ga ƙoda, inda kuma ake fara wankin ƙodar bayan watanni uku da kamuwa da cutar, kuma idan da ƙarar kwana mutum zai mutum jim kaɗan bayan nan.

Tarin fuka

Dangane kuma da cutar tarin fuka,ƙungiyar ta ce kaso 7.0 na waɗanda asibitocin Najeriya ke kwantarwa sun kasance masu fama da tarin faka.

Tarin fuka na ɗaya daga cikin manyan matsalolin lafiya a Najeriya,inda a 2023 ƙasar ta samu masu ɗauke da cutar fiye da 371,000.

Duk da cewa Najeriya ta yi nasarar magance ta da kaso 93 amma har yanzu ƙasar na fama da cutar inda tarin fukar ke ci gaba da kama mutane da dama.

Ƙarancin garkuwar jiki

Cutar Sepsis a Turance wadda ke haddasa ƙarancin gaskuwar jiki ga wanda ya kamu da ita na ɗaya daga cikin cutukan da ke kwantar da ƴan Najeriya a asibiti.

Ƙungiyar NARD ta ce cutar ce ke tilasta kwantar da kaso 6.0 na marasa lafiyar da ake kwantarwa a asibitocin ƙasar.

Cutar Sepsis na faruwa ne lokacin da garkuwar jiki ta mayar da martani ga ƙwayar cuta, inda alamun cutar kan farawa da zazzaɓi mai tsanani da bugawar zuciya da matsalar numfashi da ruɗewa.

Me ya kamata jama'a su yi?

Likitoci na yawan bai wa marasa lafiya shawarar cewa su mayar da hankali kan yadda suke rayuwarsu kamar abinci da motsa jiki waɗanda suka ce na taimakawa sosai wajen rage kaifin cutuka koda kuwa mutum ya gada.

To sai dai kuma a lokacin da mutum ya samu ɗaya daga cikin waɗannan cutuka, likitoci na shawartar masu cutar da su garzaya asibiti domin ganin likita.

Da dama dai jama'a kan zauna a gida su ƙi zuwa asibiti walau dai sakamakon rashin kuɗin zuwa asibitin ko kuma saboda al'adar ƙin asibiti, har zuwa lokacin da cutar za ta ci ƙarfinsu.