Ko tsarki da ruwan ɗumi na da amfani ga al'aura?

.

Asalin hoton, Emma Russell

    • Marubuci, Aisha Shariff Baffa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Lafiyar al'aura wani abu ne da kusan kowa ya damu da ita, sai dai ba kowa ne ke bin hanyoyin da suka dace wajen samun sahihan bayanai kan abin da ya shafi al'aurar ba.

Wannan ya sa a wasu lokutan wasu kan riƙa yin abubuwan da kan cutar da su a maimakon su amfane su, kawai saboda wasu sun yi, ba tare da neman ilimin abin yadda ya kamata ba.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da mutane da dama, musamman mata kan bi da sunan kula da al'aura ita ce yin tsarki da ruwan zafi, to amma ta yaya hakan ke amfanar al'aura?

Masana kimiyya sun ce amfani da ruwan ɗumi wajen wanke al'aura na da matuƙar muhimmanci musamman ga mata.

Dakta Yamuna Aminu Ƙani, likitar mata ce a asibitin koyarwa na Ɗan Masara da ke jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya, kuma malama a bangaren koyar da aikin likitance a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutse, ta shaida wa BBC cewa, amfani da ruwan ɗumi a yayin tsarki na da kyau da muhimmanci, musamman idan wanda zai yi amfani da ruwan na da wata lalura ko rashin jin daɗin wajen ko ciwo ko kuma miki.

Ta ce, "Idan mutum na fama da ɗaya daga cikin waɗannan matsaloli, to idan ya yi tsarki da ruwan ɗumi zai ji wajen ya saki, wato naman wajen ko jijiya ma'ana a'aurar zai ɗan shika."

Dakta Yamuna ta ce idan ciwo ne ma a al'aurar mutum na jin raɗaɗi, to amfani da ruwan zafi zai taimaka sosai wajen dusashewar ciwon da kuma rage raɗaɗi.

"Ruwan ɗumi na sa masu amfani da shi wajen tsarki jin daɗin jikinsu da kuma samun nutsuwa." in ji ta.

Ko tsarki da ruwan ɗumi na hana kamuwa da cuta?

Dakta Yamuna, ta ce a gaskiya tsarki da ruwan ɗumi ba ya hana kamuwa da cuta, amma kuma ya kan taimaka idan akwai cutar wato 'infection' a al'aurar mutum a samu sauƙin raɗaɗin ciwo.

Ta ce," Ƙwayoyin cuta irin na al'aura na son zama a wajen da ke da ɗumi da kuma damshi, don haka idan har mutum da ƙwayoyin cuta a wajen to ya kula da tsaftar wajen da amfani da ruwan ɗumin sannan kuma aje asibiti don a nemi magani."

Likitar ta ce, idan kana da ciwo a wajen ko kuma yana maka ƙaiƙayi, to ruwan ɗumin na taimakawa, musamman idan kaɗan zuba gishiri kaɗan a ciki, ana samun afuwa.

Ko tsarki da ruwan ɗumi na da alfanu ga maza?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakta Yamuna, ta ce kowa ma zai iya amfani da ruwan ɗumi wajen tsarki.

Ta ce," Ruwan ɗumi na da fa'ida sosai ko a al'aura koma ba a al'aura ba, idan aka ji ciwo a a kan yi amfani da shi wajen ɗunɗuma wajen a samu sa'ida don haka ba iya mace ne kaɗai ke amfani da ruwan ɗumin ba har mazan."

Likitar ta ce, to amma ba lallai bane amfanin ruwan ɗumin ya yi dai-dai da yadda zai yi wa mata.

Ta ce," Halittar al'aurar mace da ta namiji ba iri ɗaya bane, domin ita mace a gabanta akwai lungu, shi kuwa namji babu, don haka cutar da za ta shige lungu ta ɓoye sai ta fi illa a kan wadda ta ke fili."

" Su maza ba su fiye samun matsala a gabansu kamar mata ba, kuma da an samu matsalar ma, yawanci maza kan riga mata warkewa, saboda su basu da lungu a gabansu ba kamar mata ba, da sai an yi ta fama."

Ta ce, to amma amfanin da ruwan ɗumin zai yi a wajen tsarki duk ɗaya don daga mata har maza kowa ya yi amfani da shi zai ji daɗi ko kuma sauƙi idan akwai lalura.

Ko amfani da ruwan sanyi na rage wa mace ni'ima?

Dakta Yumuna, ta ce ba za ace ruwan sanyi na ragewa mace ni'ima ba, sai dai kawai amfani da ruwan ɗumin ya fi fa'ida.

Ta ce,"Shi ruwan ɗumi na taimakawa wajen gudanar jini a koma ina ne, kuma ni'imar jikin mace na ƙaruwa musamman idan ta yi tsarki da ruwan ɗumi."

Likitar ta ce, " Ga maza hakan ne don al'aurarsu ta shafi jijiyoyi, kuma idan aka yi amfani da ruwan ɗumi jijiyoyi za su sake jini ya gudana sai a samu kuzari don haka shi ma ruwan ɗumi zai masa fa'ida."

Sau da dama dai zaka ga wasu mata na tsarki ruwan ɗumi abin da wasu ke cewa yin hakan na ƙarawa mata ni'ima, yayin da suke cewa amfani da ruwan sanyi kuwa na ɗauke ni'ima ga mace.

To sai dai kuma likitar ta ce ba ruwan zafi sosai ake amfani da shi wajen yin tsarki ba, mai dan ɗumi wanda ba zai yi wa mutum illa ba.

Kazalika masana kimiyya ma sun ce yana da kyau bayan mutum ya yi tsarki ya dan sanya tawul mai tsafta ko toilet paper ko kuma tsumma ma kyau ya goge al'aurarsa.

Sun ce yin haka na taimkawa ƙwarai da gaske wajen tsaftace waje da hana wajen kasancewa cikin damshi, wanda wani lokaci idan damshin ya yi yawa musamman ga mata yana ja musu mtsala a gabansu.

Kuma likitoci ma kance ba a son gaban mutum ya kasance a jiƙe ko cikin damshi.