Me ya sa wasu mata ke cinye mabiyiya bayan sun haihu?

A woman with her new-born baby

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Mabiyiya abu ne da akan jefar bayan an haihu, to amma me ya sa wasu ke son cin ɗanyar mabiyiyar ɗan'adam?

Mabiyiya wata jakka ce da ke taimaka wa ɗan tayi ya rayu a cikin mahaifa, amma da zarar ta fito bayan haihuwa, to ta gama aikinta. Daga nan akan jefar ko a binne ta - to amma ba kowa ba ne ke jaefarwa ko binnewa.

Wasu mutanen na cewa sinadaran gina jiki da uwa take tura wa ɗan tayi ta hanyar mabiyiya a tsawon watanni a cikin mahaifa, suna nan jibge a cikin mabiyiya, saboda haka bai kamata a ɓarnatar da su ba.

Sun yi amannar cewa ɗanyar mabiyiya na ƙunshe da duk abubuwan amfani da uwa ke buƙata yayin da take ƙoƙarin gyagijewa daga wahalhalun goyon ciki da kuma shiga batun shayar da jariri.

Wasu matan kan so su sha mabiyiyar idan aka markaɗa ta tare da ƴaƴan itatuwa, ƴan awanni bayan haihuwa. Wasu kuma sun fi son su busar da ita su yi garin ta daga nan sai a mayar da ita kamar ƙwayoyin magani ta yadda za su riƙa sha.

Sun yi amannar cewa mabiyiyar za ta bai wa uwa ƙarfi da haɓɓaka samar da ruwan nono da kuma kare mata daga shiga damuwar bayan haihuwa.

Charlie Poulter, daga yankin Reading a ƙasar Ingila, ta yi amannar cewa cakuda wani ɓangare na mabiyiya da ruwan kayan iatce ya sa ta samu ƙarfi bayan naƙuda da ta yi.

Ta ce "Na sha shi da sauri, saboda ba na son ma na tsaya wani tunane-tunane.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Lokacin na gama naƙuda ke nan, mutane na zagaye da ni.

"Na yi tunanin cewa in dai har za ta hana ni shiga damuwar bayan haihuwa da kuma samar min ƙarfi, to zan daure na sha," in ji Charlie.

Abubuwan da suka sanya wannan matar cin mabiyiyar a bayyane suke.

Ta shafe watanni 18 tana samun shawarwarin ƙwararru kan tsananin damuwa har zuwa lokacin da ta samu juna-biyu, shi ya sa ta damu matuƙa kan yadda za ta kauce wa faɗawa cikin cutar damuwa bayan haihuwa.

"A baya ban taɓa jin labarin maganin da ake hadawa da mabiyiya ba amma daga baya na ji an ce yana taimakawa wajen kawar da damuwa.

"Na ci alwashin yin duk abin da zan yi, kuma mijina ya ce min ko ma mene ne ba za ta cutar da ke ba."

Ta ce kuma ba ta faɗa cikin cutar damuwar bayan haihuwa ba, kuma "na rantse mabiyiyar ce ta hana."

Ɗan'adam ba ya cikin halittun da aka san suna yawan cin mabiyiya bayan haihuwa.

Baya ga halittun ruwa da kuma wasu hallitun na gida, sauran halittu masu shayarwa sukan cinye mabiyiya bayan haihuwa - wataƙila domin ƙarfafa danƙon alaƙa da ƴaƴansu..

Akan yi amfani da mabiyiya wajen haɗa wasu magungunan ƴan ƙasar China, inda suka yi amannar cewa yana taimakawa wajen gyagijewar maijego, sai dai batun cin mabiyiya ɗabi'a ce ta ƙasashen Turawan yamma wadda ba kowa ne ya amince da ita ba.

Cin mabiyiya 'ba ya ƙara lafiya'

A woman playing with her baby

Asalin hoton, Getty Images

Babu wani bayani na kimiyya da ya gasgata cewa cin mabiyiya bayan haihuwa zai iya kare mata daga cutar damuwa da akan samu bayan ahihuwa ko kuma ƙara musu ƙarfi, kamar yadda wani bincike a Amurka ya nuna.

Iƙirarin da ake yi na cewa mabiyiya na ƙunshe da sinadarai da ke ƙara wa mata lafiya sun sanya mutane da dama na son gwadawa.

Sai dai nazarin da jami'ar Northwestern ta yi bai nuna cewa akwai irin wannan amfani da ake ikirari ba.

Ita kuwa kwalejin koyar da aikin ungozoma ta Royal College of Midwives ta ce ya kamata a bar mata da zaɓin su.

Masu bincike sun ce cin mabiyiya na ƙara samun karɓuwa tsakanin mutane, sai dai sun danganta hakan da yawan yayata bayanin a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta.

Wata maƙala da aka wallafa a Mujallar lafiya mata ta yi nazari kan bayanai 10 da aka wallafa kan cin mabiyiya.

Sai dai masanan sun ce babu wani bincike da ya tabbatar da cewa cin mabiyiya ɗanya ko dafaffa ko kuma ta sigar ƙwayan magani yana da amfani ga lafiya.

Sai dai bayanin ya ce babu wani nazari ko cin mabiyiyar na da illa.

Ita dai mabiyiya wata rariya ce da kan tace da kuma zuƙe sinadarai da za su iya cutar da ɗantayi.

Saboda haka masana sun ce akwai yiwuwar za a iya samu sauran ƙwayoyi masu cutarwa a jikin mabiyiyar bayan haihuwa.

Jagorar masu binciken, Cynthia Coyle, ta jami'ar Northwestern University ta ce: "Abin da muke so a sani shi ne ya kamata mata masu cin mabiyiya su yi hattara da irin abin da suke ci a lokacin da suke ɗauke da ciki da kuma lokacin renon jarirai, kada su riƙa cin abin da babu wata hujja da ta tabbatar da amfaninsa ko kuma hatsarin da yake da shi gare su da kuma jariransu.

"Babu dokoki kan yadda ake ake sarrafawa da kuma ajiye mabiyiyar, kuma babu takamaiman bayani kan yadda za a ci ko sha.

"Mata ba su san abin da suke cusawa a cikinsu ba."

Louise Silverton ta kwalejin horas da ungozoma ta Royal College of Midwives ta ce ya zuwa yanzu babu isassun bayanai da za su yi amfani da su domin bai wa mata shawara kan batun cin mabiyiya.