Dalilan da suka sa matan China ba sa son haihuwa

Asalin hoton, Getty Images
"Ba na son ƴaƴa da yawa,’’ in ji Gloria, wata matar aure da ke da shekara 30.
Ta ce ta yi lissafin cewa hakan zai saka ta kashe kuɗi sama da $2,400 a wata bayaga sauran abubuwa da za ta buƙata na sayawa jariri a China.
"Zai kai kusan $436 a kowace rana kamar sayan abinci. $291 na kai yaro makaranta, $145 na kula da jariri, sai kuma akalla $1, 456 na sauran buƙatun makaranta.”
Gloria na aiki ne a matsayin malamar wucin gadi a wata makaranta da ke lardin Guangdong a kudancin China.
Mafi ƙanƙantar albashi da masu aiki a kamfanoni masu zaman kansu ke samu a ƙasar ya kai kusan yuan 6,000.
Kasancewa ita kaɗai ce a iyalinsu, saboda tsarin ƙasar China na ɗa tilo, ta ce tana son mayar da hankali kan biyan bashi da kuma adana kuɗi don taimaka wa iyayenta da suka fara tsufa.
Raguwar al’umma
China dai na fama da matsalar raguwar al’umma a karon farko cikin shekaru 60.
Sabbin alƙaluma sun nuna cewa yawancin mata a ƙasar na son su mallaki ɗa guda ɗaya ko kuma babu kwata-kwata.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Alƙaluman matan China da ba sa da yara ya tashi daga kashi 6 a 2015 zuwa kashi 10 a 2020, a cewar wani binciken da cibiyar kula da al’umma da kuma ci gaba na ƙasar ta gudanar a baya-bayan nan.
Binciken ya kuma nuna cewa matan ƙasar masu shekarun haihuwa ba sa da buƙatar samun ɗa, inda alƙaluman mata masu son yara ya ragu da kashi 1.64 a 2021, idan aka kwatanta da 1.76 a 2017.
Yayin da sauran ƙasashen Asiya kamar Singapore da Japan da Kudancin Korea, su ma suna da buƙatar haihuwar yara biyu kaɗai, yawancin matan sun ce yara biyu kaɗai suke so. Sai dai, ba haka batun yake ba a China.
"A China ba wai masu haihuwar ne suka yi ƙaranci ba, a’a, waɗanda ke buƙatar haihuwan ne ya ragu,’’ in ji Dakta Shuang Chen, mataimakin farfesa a fannin tsare-tsare na rayuwar ɗan adam a kwalejin harkokin tattalin arziki da kimiyyar siyasa da ke birnin Landan.
A dai-dai lokacin da China ke shirin gudanar da wasu tarukan siyasa – waɗanda ke da muhimmanci ga ƙasar – masu bayar da shawara kan harkokin siyasa, sun gabatar da takardu daban-daban na son bunƙasa yawan masu haihuwa.
Shawarwarin da suka bayar sun háɗa da taimaka wa matan da basu da aure yin ƙwayaye da rage kuɗin makaranta da na takardu daga makarantar firamare har zuwa kwaleji.
Har ila yau, akwai kuma shawara da suka bayar na bai wa yaran da aka haifa ba tare da aure ba kulawa kamar kowa.
A China, yaran da aka haifa ba tare da iyayensu sun yi aure ba, suna fuskantar wahalhalu wajen samun rajistar da ta dace na samun ilimi da lafiya da kuma na kyakkyawar rayuwa. Yawancin lokuta kuɗin suna tsadar gaske.
Wahalar rainon yaro'

Asalin hoton, Getty Images
Tsadar rayuwa wajen rainon yara, na cikin dalilai da suka sa matan China basa son haihuwa.
A China, da zarar an haifi yaro, daga lokacin iyayensa za su fara fafutukar ganin sun kai shi makaranta mai kyau da sayan gidaje kusa da sanannun makarantu a larduna da kuma ɗaukar malamai su zo har gida don koyar da yaransu.
"Bana son kawo sabuwar rayuwa cikin wannan muhalli mai cike da wahalhalu,’’ in ji Mia, wata ɗaliba mai shekara 22 da ke karatu a wata kwaleji.
An haife ta ne a wani ƙaramin gari da ke arewacin China, inda yawancin karatunta na makaranta ya ta’allaka kan jarabawa.
Ta zana babbar jarabawa na shiga kwaleji a ƙasar, wanda aka fi sani da Gaokao, inda daga nan ta wuce zuwa wata babbar jami’a a Beijing. Ta ce a yawan lokuta, tana jin kanta a gajiye.
Ta ce ko da waɗanda suka gama makaranta, suna jajircewa wajen ganin an dama da su tsakanin waɗanda ke da halin zuwa karat ƙasashen waje.
"Dukkan wannan ƙarin abubuwa na tallafi na ilimi na buƙatar kuɗi,’’ in ji Mia, wadda ke ganin bata tsammanin samun kuɗaɗe da yawa da za ta iya rainon yara a nan gaba.
"Idan ba zan iya bai wa yaro irin wannan kulawa ba, to me ya sa zan haifi yaro?”
Babu sauƙi a wajen aiki

Asalin hoton, Getty Images
Yawancin matan da BBC ta tattauna da su, sun bayyana irin mummunan tasiri da tsarin aikinsu yake musu, wanda hakan na cikin dalilai da ta sa suka zaɓi zama ba tare da yara ba.
A wajen gwaji na ɗaukar aiki, matan sun bayyana cewa ana tambayarsu cewa ko suna da niyyar samun haihuwa a cikin shekaru masu zuwa. Sun ce idan suka mayar da martani da cewa suna son haihuwa, to za su rasa damar samun aikin, ko kuma damar da suke da ita ta samun ƙarin matsayi za ta ragu.
"Samun sauƙi a wajen aiki da kuma na rayuwar yau da kullum, na cikin abubuwan da yawancin mata a manyan makarantun China suka nanata cewa ya sa basa son haihuwa,’’ in ji Dakta Yun Zhou, mataimakiyar farfesa a fannin nazarin rayuwar ɗan adam a jami’ar Michigan, a tattaunawarsa da BBC.
"A wajensu, aiki shi ne cimma buƙatar ƙashin-kai,’’ in ji ta. “ A cikin tsarin aiki da ke ciki da musgunawa, yana da matukar wahala a yi zaɓi tsakanin tsarin aiki da kuma na son samun haihuwa."
'Na fuskanci cin zarafi a intanet lokacin da na ce bana son haihuwa'
Kamar sauran matasa waɗanda ke son bayyana wani abu kan rayuwarsu a kan kafafen sada zumunnta, Mia ta naɗi wani bidiyo, inda ta ke bayyana abin da ya sa bata son haihuwa da kuma wallafa shi a kan intanet.
Sai dai, ta cika da mamaki kan irin zagin da ta sha a wajen mutane.
Yawanci sun zargeta da yin son kai. Wasu kuma sun ce bata san abin da ta ke yi ba saboda har yanzu ita karama ce mai shekaru ashirin da ‘yan kai.
"Baki da damar faɗar haka. Bari um ga ko za ki ce hakan idan kika kai shekaru 40,’’ in ji wani a martanin da ya mayar.
"Na saka $10,000 cewar za ki yi da na sani," in ji wani.
Martanin wasu har ya zarce kan haka, inda suka kira ta da ‘yar ƙasar waje da ke son cusawa mutane ra’ayin kada su haihu.
Gwamnatin China ta bullo da tsarin yara uku ga kowane iyali a watan Mayun 2021, a wani martani kan kiɗayar 2020, da ta nuna cewa mata a China sun haifi yara miliyan 12 a shekarar, mafi karanci da aka samu tun 1961.
A shekarun baya-bayan nan, gwamnatin ƙasar ta ɓullo da tsare-tsare da dama domin karfafawa ƙarin mutane na cewa su haifi yara.
Sai dai, duba da ƙarancin haihuwa a ƙasar, a wajen wasu, duk matar da ta ce bata son haihuwa, tana durkusar da kasar ne.
"Ra’ayi na ne na kashin kaina. Ban da’awa kan batun waɗanda basa son haihuwa. Ina girmama mutanen da ke sony ara,’’ in ji Mia.
'Na sha gwagwarmaya mai zafi'
Kalubalantar tsare-tsaren iyali musamman ma kan haihuwa, na da matukar wahala.

Asalin hoton, Getty Images
"Na sha gwagwarmaya," in ji Yuan Xueping. Mai shekara 34, wadda aka haifa da kuma ta tashi a ƙauye, wajen da aka ɗorawa yaron da mace za ta haifa musamman ma idan ɗa namiji alhakin tafiyar da sunan iyalin yadda ya dace, wanda kuma ke da matuƙar wahala mace ta ce ba ta son haihuwa.
Miss Yuan da yayarta basu samu damar zuwa kwaleji ba, duk da cewa tana cikin ɗalibai na ukun farko masu ƙoƙari a makarantarsu. Iyayenta sun biya wa ƙaninta kaɗai kuɗi don ci gaba da karatunsa.
"Iyaye na suna yawan cewa: 'Mene ne ribar yarinya na zuwa kwaleji? Yanzu ko anjima, za ki iya yin aure tare da zama a cikin gida don kula da yaranki," in ji Ms Yuan.
Lokacin da aka saki yayarta, inda aka bar ta da ɗawainiyar kula da yaranta biyu, hakan ya sa ta ƙara cire batun haihuwa a ranta.
"Ba ni da ra’ayin aure a yanzu,’’ in ji ta, bayan barin mahaifarta da zuwa birni, inda a yanzu ta ke zaman kanta.
"Ina karatuna da kuma fita yawon shaƙatawa tare da ƙawayena a duk lokacin da nake so. Ina jin daɗin yin komai a yanzu."











