Sadio Mane: Daga ƙwallon ƙafa a layi zuwa jigon tamaula a Afirka

Sadio Mane ne ya zura fanaretin ƙarshe domin lashe gasar Afcon ta 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sadio Mane ne ya zura fanaretin ƙarshe domin lashe gasar Afcon ta 2021
    • Marubuci, Rob Stevens
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
    • Marubuci, Charlotte Coates
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • Lokacin karatu: Minti 5

Sadio Mane ya sake jan ragamar tawagar Senegal zuwa lashe gasar Afcon, amma a wannan karon, ba lashe gasar ba ce kawai ke jan hankali.

Tsohon ɗan'wasan na Liverpool da Bayern Munich ya lashe gasar Afcon karo na biyu tare da tawagar Teranga Lions bayan doke Morocco mai masauƙin baƙi a wasan da ya haifar da taƙaddama.

Ana kusa da tashi wasa ne kocin Seegal Pape Thiaw ya buƙaci ƴan'wasansa su fice daga filin wasan baya alƙalin wasan ya ba Morocco fanareti a minti na 98 da wasan bayan ɗan'wasan baya Senegal El Hadji Malick Douf ya ja Brahim Diaz ya faɗi ƙasa.

A daidai lokacin da ƴan'wasan Senegal ke ƙoƙarin ficewa ne aka ga Mane yana ta ƙoƙarin lallaɓa su da su koma cikin fili su cigaba da taka leda tare da taimakon mai tsaron ragar ƙungiyar, Edourd Mendy.

Kimanin minti 16 bayan lamarin ne Diaz ya buga fanaretin da salon panenka, amma ya ɓaras, inda Mendy ya kama ƙwallon cikin sauƙi.

Bayan an tashi babu ci ne aka shiga ƙarin lokaci, inda Pape Gueye ya zura ƙwallon da ta zama sanadiyar samun nasarar Senegal a kan Morocco mai masaukin baƙi.

Mane, wanda ya ce wannan gasar Afcon ta ƙarshe da zai buga, ya nuna bajinta da shugabanci a lokacin da ake buƙata, musamman inda ƴan'wasan tawagar suka buƙaci ya wakilce su wajen ɗaga kofi duk da ba shi ba ne kyaftin.

Ya ce, "harkar ƙwallo ƙafa tana da muhimmanci, kuma duniya na kallonmu. Don haka bai kamata mu zama sanadiyar ɓata harkar a idon duniya ba.

"Ina tunanin da ba mu cigaba da buga wasan ba, da mun yi shirme. Kawai don alƙalin wasa ya bayar da fanareti, sai mu fita daga filin wasa? da mun yi haka, da ya zama matsala ga ƙwallon ƙafa a Afirka. Gara mu rasa wasan, maimakon a ce mun fita daga fili."

"Bai kamata a tsayar da wasan ƙwallo har minti 10 ba, amma yaya za mu yi? Amma dai mun yi abin da ya dace da muka koma wasan."

Tsohon ɗan'wasan Najeriya Daniel Amokachi ya bayyana wa BBC cewa, "Mane ya yi ƙoƙari wajen tabbatar da ƴan'wasan Senegal sun koma fili, kuma ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu.

"Ya zama jakadan ƙwallon Afirka. Mun san halayensa a filin wasa da ma a waje. Mutum ne mai kirki, kuma ya fahimci ƙwallo sosai."

Tsohon ɗan'wasan Morocco, Hassan Kachloul ya ce, "Ƙwallon ƙafar Afirka ta kusa shiga tsilla-tsilla kafin Mane ya cece mu."

Yadda ya fara ƙwallo a Senegal

Mane ya fara ƙwallo ne daga garin Bambali.

Gari da ke kudu maso yammacin Senegal, inda ya fara ƙwallo a layi a filin turɓaya, sannan yana ɗan shekara 13 ya kalla fitaccen wasan nan na ƙarshe tsakanin Liverpool da AC Milan a gasar zakarun turai ta 2005.

Daga lokacin zuwa yanzu, ya lashe gasar shi ma a ƙungiyar ta Reds, sannan ya lashe gasar Afcon sau biyu.

Mane ne ya zura bugun fanareti na ƙarshe a gasar Afcon da Senegal ta doke Masar a 2021, lamarin da ya bayyana da "lokaci mafi muhimmanci a rayuwarsa."

An saka sunansa a wani fili a birnin Sedhiou, wanda kimanin kilomita 20 daga asalin garinsu.

Yanzu mai shekara 33, Mane ya sake lashe gasar, inda za a iya cewa wataƙila ya yi ban-kwana da gasar da ƙarfinsa.

Amma Gueye ya ce ƴan'wasan tawagar za su buƙaci Mane ya canja ra'ayinsa domin ya cigaba da taka leda da tawagar aƙalla zuwa gasar ta 2027 a Kenya da Tanzania da Uganda.

Yadda yake rayuwa

Mane ya taɓa ƙwallo sau 295 a gasar Afcon ta 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mane ya taɓa ƙwallo sau 295 a gasar Afcon ta 2025
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mane, wanda yanzu yake taka leda da ƙungiyar Al-Nassr a Saudiyya, ya samu nasarori da dama, amma duk da haka bai taɓa mantawa da asalinsa ba.

Yana da ɗimbin masoya a Bambali saboda kyautarsa da ƙoƙarin da yake yi wajen ginawa da gyara asibitoci da makarantu da gina masallatai da ma tallafin da ya bayar a lokacin annobar coronavirus.

"Idan Sadio ya zo gida, yana mu'amala da kowa cikin girmamawa ba tare da girman kai ba," in ji Fode Boucar Dahaba, shugaban gasar yankin a zantawarsa da BBC.

"Bai cika so yana zama na daban a cikin al'umma ba, su kuma ƴan ƙauyen suna matuƙar ƙaunarsa."

Ƴan'uwa da dangi kuma sun bayyana shi a matsayin "wanda yake aiki domin kowa, kuma musulmin kirki."

Haka kuma ya nuna hali na daban a lokacin da yake ƙwallo a Ingila, inda da ya riƙa wanke ban-ɗakunan masallacin Toxteeth.

"Ya kasance yana aikin a ɓoye ne ba tare da an sani ba," in ji Abu Usamah Al-Tahabi, limamin masallacin Al Rahma.

"Ba shi da girman kai, ba mutum ba ne mai neman shahara."

Senegal na tsammanin ɗauki daga Mane

Ɗan'wasan tsakiya na Senegal Idrissa Gana Gueye (a gefe) ya bayyana Mane a matsayin "babban ɗan'wasa."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan'wasan tsakiya na Senegal Idrissa Gana Gueye (a gefe) ya bayyana Mane a matsayin "babban ɗan'wasa."

Mane ya buga wa Senegal wasa 120, inda ya zura ƙwallo 53.

Yana nuna ƙwarewa matuƙa a filin wasa, sannan yana da burin wakiltar ƙasarsa a gasar cin kofin duniya da za a buga a bana, inda yake fatan ƙara kafa tarihi.

Ya ɓarar da bugun fanareti a farkon wasan ƙarshe a gasar Afcon ta 2021, amma kuma ya samu nasarar zura bugun fanareti na ƙarshe, inda ƙasarsa ta lashe gasar ta hanyar doke Masar a birnin Yaounde.

Bayan kimanin ɗaya kuma ya jagorancin ƙasarsa wajen doke Masar a wasan cike-gurbi zuwa gasar cin kofin duniya da aka buga a Qatar, duk da raunin da ya ji ya hana shi buga gasar.

"Yana taimaka mana a manyan wasanni," in ji Idrissa Gana Gauye a zantawarsa da BBC.

"Babban ɗan'wasa ne, kuma yana nuna kansa a manyan wasanni."

'Za mu so ya ci gaba da buga wa Senegal ƙwallo'

Mane ɗan'wasan Senegal da ya fi zura a wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mane ɗan'wasan Senegal da ya fi zura ƙwallo a wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026

Duk da cewa Mane ba mutum ba ne mai son girma, kuma ba shi ba ne kyaftin, amma idan ya yi magana, abokan wasansa suna sauraro.

"A jawabinsa na kafin wasanmu da Masar, ya ƙarfafa mana gwiwa," in ji Pape Gueye.

"Ya yi magana sosai, ya san me zai faɗa mana domin ya ƙarfafa mana gwiwar shiga wasan da ƙarfinmu. Ya goge sosai wajen buga manyan wasanni. Yana faɗa mana mu kwantar da hankalinmu."

Mane, wanda ya yi zamani ne sosai tare da tsohon kocin tawagar, Aliou Cisse, wanda ya jagoranci tawagar ƙasar tsakanin 2015 zuwa 2024, amma kocin ƙasar na yanzu, Pape Thiaw na da burin ganin ɗan'wasan ya cigaba da wakiltar ƙasar.

"Za mu so ya cigaba da wakiltar ƙasarsa zuwa nan da wani lokaci na gaba."