Abin da aka tattauna tsakanin Abba da Tinubu

Tinubu da Abba

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Litinin ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai wa shugaba Bola Tinubu ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke ƙara tabbatar da batun sauya sheƙarsa daga jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Kafin ganawar ta jiya, an yi ta hasashen cewa tattaunawar gwamnan da shugaba Tinubu wata kafa ce ta kammala shirye-shiryen ficewarsa daga jam'iyyar NNPP.

Siyasar Kano ta shiga ruɗani a baya bayan-nan kan batun sauya sheƙar gwamna Yusuf, wani abu da wasu jagororin NNPP, ciki har da uban jam'iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka nuna adawa a kai.

Lamarin ya janyo saɓani a cikin jam'iyyar, musamman tsakanin magoya bayan gwamnan da kuma waɗanda ke mubaya'a ga tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Kwankwaso ya assasa.

Sai dai, kakakin gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya shaida wa BBC cewa tattaunawar ta ranar Litinin ta mayar da hankali ne kan zaƙulo hanyar bunƙasa jihar, ba siyasa ba.

Ya ce sun tattauna kan halin rashin tsaro da jihar ke fama da shi a baya-bayan nan, inda ake samun wuraren da ƴanbindiga ke kai hare-hare.

"Gwamna Abba ya kuma yi amfani da damar wajen yi wa shugaban ƙasa bayani na wata mata da aka kashe da ƴaƴanta shida. Ya buƙaci shugaban ƙasa ya yi hobɓasa wajen samar da wadataccen tsaro," in ji Sanusi Bature.

'Duk mai son Kano zai so haɗin-kai tsakanin Abba da Tinubu'

Wata sanarwa da kakakin gwamnan ya fitar a safiyar Talata, ta yayyafa ruwa kan batun sauya sheƙa da mutane ke ta hasashen cewa shi ne abin da gwamnan na Kano ya tattauna da shugaban ƙasa.

"Batun sauya sheƙa abu ne na daban, ba abu ba ne da za a yi rana ɗaya ba. Ko da gwamna Abba da Tinubu sun tattauna kan haka lokaci ne zai fayyace," in ji Bature.

Ya ƙara da cewa duk mai son cigaban jihar Kano zai so ganin haɗin kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihar, ganin cewa jam'iyyar adawa ce.

"Abin farin ciki ne cewa gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da mu domin ganin yadda za a haɗa gwiwa wajen ciyar da Kano gaba," in ji shi.

Ya ce batun sauya sheƙar gwamnan dai magana ce ta lokaci, wanda a cewarsa dama ana cewa lokaci ne alƙali.

"Duk tattaunawar da ake yi, da ta fili da ta ɓoye da kuma masu gutsuri-soma ke ta faɗa, duka idan lokaci ya yi aka zo gaɓa komai zai fito fili," in ji mai magana da yawun gwamnan na Kano.

Batun sauya sheƙar ya janyo ruɗani a Kano

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Batun sauya sheƙar gwamnan na Kano, Abba Kabir Yusuf dai na ci gaba da ta da yamutsi a siyasar jihar.

Ko a watan Disambar shekara ta 2025, shugabancin jam'iyyar ta NNPP a jihar Kano da kuma na ƙasa sun yi fatali da batun sauya sheƙar gwamnan, inda suka ce ba sa tare da shi kan haka.

Sanarwar da jam'iyyar ta fitar a lokacin, ta ce "Muna sane da abubuwan da ke faruwa a jihar Kano kan cewa wasu mutane na son sauya sheƙa zuwa APC, ba ma goyon bayan haka," kamar yadda shugaban jam'iyyar Hashim Dungurawa ya bayyana.

Ya ce babu wani ɗan jam'iyyar da ke goyon bayan lamarin, har ma da uban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

An ambato Kwankwaso na faɗa a lokacin a wani bidiyon da ya karaɗe shafukan sadarwa cewa bai yi mamakin zargin son sauya sheƙar ba, inda ya ce ƴan siyasar da ke son barin jam'iyyar su duba tarihi su gani.

Sai dai a wani ɓangaren kuma, tsagin gwamnan ya sanar da dakatar da Dongurawa daga shugabancin jam'iyyar, kafin uwar jam'iyyar ta dakatar da shugabancin jam'iyyar baki ɗaya a jihar Kano.

A wani abu da ya ƙara tayar da ƙura, akwai wani taron rabon tallafin kayan aiki da gwamnan ya yi a Kano, inda yawanci waɗanda suke tare da Kwankwaso ba su halarta ba, sannan shugaban NNPP tsagin gwamnan ne ya halarta.