Da gaske Kwankwaso ya ce zai amince ya zama mataimakin Peter Obi a 2027?

Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi

Asalin hoton, Social Media

Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayar fitar wani bidiyo da aka ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, yana hira da ƴanjarida a jihar kafafen sada zumunta da ma jaridun Najeriya suka fara rawaito cewa tsohon gwamnan ya amince ya zama mataimakin Peter Obi a takarar shugaban ƙasa ta 2027.

A 2023 Peter Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne da ke kudancin ƙasar, ya yi takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party (LP), bayan da ya fice daga jam'iyyar PDP inda ya yi wa Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP mataimakin ɗantakara a 2019.

Shi ma Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP a 2023, inda ya zo na huɗu a bayan Tinubu na APC, da Atiku, da Obi.

Tun a ranar Alhamis da ta gabata a naɗi hirar amma sai a ƙarshen mako lamarin ya fara jan hankali, inda ma'abaota shafukan sada zumunta suka dinga bayyana ra'ayoyi daban-daban.

Jam'iyyar Labour ta bakin sakatarenta na ƙasa, Umar Farouk, ta faɗa wa BBC cewa tana maraba da kalaman na Kwankwaso.

Yanzu tambayar da jama'a ke yi ita ce da gaske Kwankwaso ya faɗi hakan?

Me Kwankwaso ya ce a bidiyon?

A cikin bidiyon mai tsawon kusan awa biyu, an tambayi Rabi'u Kwankwaso kan ko zai karɓi muƙami a gwamnatin APC ƙarƙashin Tinubu. Tsohon sanatan na Kano ta Tsakiya ya ce ba zai karɓa ba duk da tayin da aka yi masa "a birnin Paris".

Ya ci gaba da bayani har ya zo wurin da yake maganar tattaunawa da sauran jam'iyyu, ciki har da LP ta Peter Obi.

"Na ce ni ba ni da matsala amma a kawo "criteria" [dalilin da zai sa na ajiye takara ta]," in ji shi. "Ba mu ne ba mu da ilimi ba ƴan Arewa? Ba mu ne kowa ya raina ba? Ni yayansa ne a siyasa.

"Kuma duk abin da aka ɗauko a saka a "criteria" [mizani] da ilimi. Ni ba sa'ana ba ne. Ni ina da PhD a "civil engineering" [harkokin gine-gine]. Riƙe muƙamai ba a fi ni ba. Ƙwazo na irin aikin da muka yi ma ba iri ɗaya ba ne a jiharsa da jihata.

"Na ce mene ne mizanin da zan yi masa mataimaki? Hankali dai ake amfani da shi ko? Kuma wannan jam'iyyar ai gina ta muke yi a hankali ko. Ba irin PDP ba ce da muka haɗu muka gina ta, ko kuma APC da kawai mutum zai shigo ya yi mata taka haye.

"Saboda haka mu muna nan muna jira, kuma a shirye muke mu tattauna da kowa. Amma duk abin da za a yi a yi shiri na gaskiya. Kada a zo a faɗa min ƙarya."

Muna maraba da kalaman Kwankwaso - LP

Da ma an sha tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Obi tun kafin zaɓen 2023, amma suka kasa cim ma matsaya game da yin haɗaka domin tunkarar APC mai mulki.

A wannan karon, Sakataren LP na Ƙasa Umar Farouk ya ce suna maraba da kalaman, waɗanda ya bayyana a matsayin ci gaba a siyasar Najeriya.

"Da ma irin wannan rashin haɗin kai ne ke sakawa a rasa ɓangaren hamayya mai ƙarfi a siyasar Najeriya," a cewarsa.

"Idan ire-iren su Kwankwaso suka sassauta burinsu muna da ƙwarin gwiwar za a samu ci gaba a ƙasar. Shi ma Obin ya ce ai zai iya yi wa wani mataimaki."

Ganin cewa ba a rubuce ya miƙa wa LP buƙatyarsa ba, anya ba za a ce sun yi azarɓaɓi ba kuwa? Sai sakataren ya ba da amsa da cewa:

"Ai ba maganar azarɓaɓi, ba sai ya rubuto ba tun da dai ya faɗa da bakinsa. Indai ana son ci gaban ƙasar nan ne muna yi masa maraba, kuma ɗantakarar shugaban ƙasarmu a shirye yake ya yi aiki da shi."

Ba a fahimci maganganun Kwankwaso ba - Buba Galadima

Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar NNPP kuma makusantan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ba a fahimci kalaman Kwankwaso ba musamman waɗanda ba sa jin harshen Hausa sosai.

"Da mutum yana jin Hausa ai zai fahimci ma an ƙasƙantar da Peter Obi ne. Babu wannan magana. Shaci faɗi ne kawai. Mu ba mu shiga siyasa domin kanmu ba. Mun shiga siyasa ne domin taimaka wa talakawan Najeriya."

Sai dai kuma Buba Galadima ya amince da cewa "suna yin maganganu ne domin su nuna wa ƴan adawa cewa ƙofarsu a buɗe take tunda dai ba zaman gaba ake yi ba."

Me ya sa ake son Kwankwaso ya zama mataimaki ga ƴantakara?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Baya ga Peter Obi, masu bin harkokin siyasa sun sha nuna sha'awar Kwankwaso ya haɗa kai da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, kuma an gansu tare bayan zaɓen 2023.

Kasancewarsa tsohon gwamna, tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai, tsohon sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta Tsakiya, Rabi'u Kwankwaso ya kafa kansa a matsayin jagora na siyasa a Najeriya.

Wannan ta sa ya yi takara a dukkan manyan jam'iyyun; ya zama gwamna a wa'adinsa na farko ƙarƙashin PDP, sannan ya kammala wa'adi na biyu ƙarƙashin APC kuma ya ci zaɓen sanata a APC ɗin, kafin daga baya ya yi takarar shugaban ƙasa a NNPP.

"Ko da a ce sun haɗu [Kwankwaso da Peter Obi] in dai ba su shiga lungu da saƙo sun tallata manufofinsu ba to baza su yi wani tasiri ba," in ji Farfesa Kamilu Fagge, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero da ke jihar ta Kano.

Ya ƙara da cewa "sannan sai sun haɗa ƙaƙƙarfar tawaga da za ta iya ja da jam'iyya mai mulki, saboda APC na da ƙarfin mulki."

Masanin ya bayar da misali da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya shafe lokaci mai tsawo yana yi takara kuma yana samun ƙuri'u "amma bai iya cin zaɓen ba sai da ya nemo wani daga kudanci suka haɗa hannu".