Ba ni da hannu a rushe sababbin masarautun Kano - Rabiu Kwankwaso
Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba shi da hannu a rushe masarautun jihar da gwamnatinsu ta yi ranar Alhamis.
Ana yi wa Kwankwaso kallon babban jagora kuma mafi ƙarfin faɗa-a-ji a ɓangaren siyasar Kwankwasiyya na jam'iyyar NNPP, wadda ke mulkin Kanon a yanzu.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rushe masarautun biyar ne bayan 'yan majalisar dokokin jihar sun rushe dokar da magabatansu suka ƙirƙira a 2019 ƙarƙashin gwamnatin Abdullahi Ganduje ta jam'iyyar APC.
Soke dokar ta sa aka tuɓe duka sarakunan jihar biyar kuma nan take gwamnan ya bayyana sunan Muhammadu Sanusi II (ko kuma Sanusi Lamido Sanusi) a matsayin sabon sarki bayan masu naɗin sarki sun zaɓe shi.
"Ni dai ga ni a Abuja, abin da ka gani ni ma shi na gani," a cewar Kwankwaso lokacin da BBC ta tambaye shi game da rushe masarautun.
Ya ƙara da cewa sai a ranar Juma'a ne yake sa ran zuwa birnin na Kano, wadda za ta iya yin daidai da ranar da Sarki Muhammadu Sanusi II zai koma kan karagar mulkin Kano.
"Zan yi magana da 'yan majalisar da shi gwamnan don mu ji yadda abubuwan suke," in ji shi.
Sai dai tun a watan Janairun da ya gabata Kwankwaso ya tabbatar da cewa babu shakka za a sake nazari kan dokar da ta kafa sabbin masarautun huɗu a Kano.
"Gaskiya yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba a taɓa zama da ni a kai ba, amma kuma na san dole za a zo a yi magana," kamar yadda ya bayyana a lokacin.
Sai dai ya faɗa wa BBC cewa da ma ba cewa ya yi a ɗauki wani mataki ba.
"Da ma ba cewa na yi a yi dama ko a yi hagu ba, cewa na yi za a duba kuma ga shi sun duba."












