Abubuwan da sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024 ta ƙunsa

...

Asalin hoton, facebook/Abba Kabir

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da ƙudurin yin gyara ga dokar da ta kafa masarautu biyar na jihar ta shekarar 2019.

A tattaunawar da ya yi da BBC, shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ya ce daga lokacin da aka amince da dokar a ranar Alhamis, "babu wani sarki mai matsayi a jihar..." kuma hakan na nufin za a buƙaci masu zaɓen sarkin Kano su gabatar wa gwamna sunayen mutanen da suke so a naɗa a matsayin sarkin Kano.

Mene ne abubuwan da dokar ta ƙunsa?

1 - Soke dokar masarautu ta 2019

An soke:

  • Dokar masarautun Kano ta 2019 (1441 A.H) wadda aka samar a ranar biyar ga watan Disamba, 2019.
  • Dokar naɗi da sauke sarakuna wadda aka yi wa gyara ta ranar 8 ga watan Disamba 2019.
  • Dokar masarautun Kano ta 2020 wadda aka yi wa gyara a ranar biyar ga watan Disamba 2019.

2 - Rushe sabbin masarautu da sarakuna biyar

...

Asalin hoton, facebook/multiple

  • An rushe dukkanin masarautu biyar da aka ƙirƙiro ƙarƙashin dokar masarautu ta Kano ta ranar biyar ga watan Disamba 2019.
  • An rushe dukkanin naɗe-naɗen da aka yi ƙarƙashin dokar masautun Kano ta ranar biyar ga watan Disamba, 2019 wadda aka soke.

3 - Mayar da masu muƙamai matsayinsu na baya

  • Duk wasu naɗe-naɗe na sarauta ko ƙarin matsayi ko sabbin muƙamai da aka samar ƙarƙashin dokar masarutun Kano ta biyar ga watan Disamba, 2019 za su koma matsayinsu na baya, kamar yadda doka ta tanada gabanin samar da dokar ta watan Disamban 2019 wadda a yanzu aka soke.

4 - Ƙarfin ikon gwamna

Gwamna zai ɗauki duk wasu matakan da suka dace wajen mayar da matsayin tsarin masarautar Kano zuwa yadda ya kasance gabanin samar da dokar masarautun jihar ta ranar biyar ga watan Disamban 2019, wadda aka soke.

5 - Ƙarfin ikon kwamishina

Kwamishinan ƙananan hukumomi zai lura da duk wasu tsare-tsaren miƙa ragama, ciki har da yadda za a yi da kadarorin masarautun da aka rushe da kuma tsarin da dokar masarautu ta ranar biyar ga watan Disamban, 2019 da aka soke ta samar.