Majalisar Kano ta rushe masarautu biyar na jihar

Abba Kabir da Aminu Ado Bayero

Asalin hoton, Kano State Government

Bayanan hoto, Sarkin Kano Aminu Ado kenan suke gaisawa da Gwamnan Kano Abba Kabir ranar Litinin yayin taron 'yan majalisar ƙungiyar Ecowas

Majalisar dokoki ta jihar Kano a arewacin Najeriya ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sababbin masarautu a 2019.

Hakan na nufin cewa an koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.

Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi ranar Alhamis.

Sabon matakin da majalisar ta ɗauka ya nuna cewar sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da Ƙaraye, da Gaya, da Rano duk sun rasa kujerunsu.

Idan har Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a kan sabuwar dokar hakan zai ba shi damar naɗa sabon sarki a masarautar Kano.

"Wannan doka ta bai wa gwamna iko, tun da an dawo da masarauta guda ɗaya, ya tuntuɓi masu zaɓen sarki su ba shi sunan wanda zai zama sarkin Kano," kamar yadda Shugaban Masu Rinjaye na majalisar Kano Lawan Hussaini Dala ya yi bayani

"Yanzu babu sarki ko ɗaya a Kano," in ji shi.

'Yan majalisar kuma sun gabatar da sabuwar dokar da za ta ƙirƙiri sabbin sarakuna masu daraja ta biyu.

"A gobe [Juma'a] za mu yi wa dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu karatun farko insha Allahu," a cewarsa.

Sauya gwamnati a Kano

Sanusi Lamido Sanusi

Asalin hoton, Facebook/Sanusi Lamido Sanusi

Bayanan hoto, Gwamnatin Kano ta tuɓe Muhammadu Sanusi II daga sarautar sarkin Kano a watan Maris na 2020
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Muhawara ta kaure kan makomar masarautar Kano da kuma sabbin masarautun da aka ƙirƙiro ne bayan nasarar jam'iyyar NNPP a zaɓen gwamnan jihar na 2023.

Jam'iyyar NNPP tana ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda a lokacin mulkinsa ne aka naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin na Kano.

A farkon wannan shekarar Sanata Kwankwaso ya tabbatarwa manema labarai cewa za a sake nazari a kan masarautun Kano.

"Gaskiya yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba a taɓa zama da ni a kai ba, amma kuma na san dole za a zo a yi magana," in ji Kwankwaso.

A watan Maris ɗin shekarar 2020 ne gwamnatin jihar Kano ta bakin sakataren gwamnati, Alhaji Usman Alhaji, ta sanar da cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga kujerarsa.

Wannan dai wani mataki ne da ya raba kan al'ummar jihar Kano, wasu sun goyi bayan cire sarkin wasu kuma suka nuna adawarsu da shi.

Kazalika masu sharhi sun yi zargin tsamin dangantaka da ke tsakani Kwankwaso da Ganduje ita ta shafi Sarki Muhammadu Sanusi II, tun da Kwankwaso ne ya naɗa shi bayan rasuwar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Sai dai a lokacin sanarwar gwamnatin Kano ta bayyana dalilai irinsu: sukar manufofin gwamnatin Kano, da rashin biyayya ga gwamnatin da kuma kare mutuncin jihar da dai wasu ƙarin dalilai.