Me ya faru Abba zai koma APC ya bar Kwankwaso a NNPP?

.

Asalin hoton, Kano State Government

Lokacin karatu: Minti 3

Alamu na nuna cewa duk wata jita-jita yanzu ta ƙare dangane da ko gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Kusan yanzu batun da ake ta yi ke nan a kafafen watsa labarai na jihar da ma tsakanin ƴan siyasa har ma da ma'aikatan gwamnati.

Wannan dai na zuwa ne mako biyu bayan da shugaba Tinubu ya yi wa gwamnoni gargaɗi da barazanar cewa idan ba su aiwatar da hukuncin kotun ƙolin ƙasar ba da ta yanke hukuncin jihohi su sakar wa ƙananan hukumomi mara to shi zai fara aike musu da kuɗaɗensu kai tsaye.

Yaushe Abba zai koma APC?

Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa ana sa ran gwamnan na Kano, Abba Kabiru Yusuf zai sanar da sauya sheƙar zuwa jam'iyya mai mulki a ranar Laraba lokacin taron majalisar zartarwar jihar.

Majiyar ta kuma tabbatar wa da BBC cewa kawo yanzu ba kowane ya san inda gwamnan yake ba.

Ina Kwankwaso?

Majiyar da BBC ta yi magana da ita mai ƙarfi wadda ke da alaƙa da jagoran Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan na Kano zai ci gaba da zama a jam'iyyar ta NNPP.

Sai dai kuma majiyar ta ce gwamnan zai sauya sheƙa da ma fi rinjayen ƴan majalisar dokokinsa na jam'iyyar NNPP da kuma kwamishinoni, amma kuma ban da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo wanda hakan ke nuna akwai rashin jituwa.

Shin ko an raba gari ne?

Kawo yanzu dai ba za a iya cewa an raba gari tsakanin Abba da ubangidan nasa, Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sai dai kuma alamu masu ƙarfi na nuna abubuwa guda uku kamar yadda jama'a suke ta tattaunawa:

  • Akwai yiwuwar gwamna Abba na fuskantar matsin lamba daga wani wuri da ka iya tilasta masa sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki, inda shi kuma Kwankwaso ba zai bi shi ba. Kuma za a yi hakan ba tare da an raba gari ba.
  • Wasu kuma na ganin akwai yiwuwar shiri ne na siyasa, inda masu wannan tunani ke ganin kamar Kwankwaso ya tura Abba Kabir zuwa jam'iyyar ta APC ne ya je ya karɓi jagorancinta kafin daga bisani shi kuma madugun ya bi shi.
  • Har ila yau, akwai masu hasashen cewa komai ka iya faruwa ta fuskar raba gari a siyasance tsakanin mutanen.

Martanin jam'iyyar NNPP

..

Asalin hoton, Dunguruwa/Facebook

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa ya ce gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da duk waɗanda za su bi shi zuwa jam'iyyar APC sun yi hakan ne domin raɗin kansu sannan sun yi iya yinsu wajen ganin ba su ɗauki matakin sauya sheƙar ba.

"Ina so na sanar cewa da jam'iyya ta Kano, da kasa da Jagora na Kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwasiyya da sauran jagorori duk abin da yake faruwa ba da lamuncewarmu ba ne. Hasali ma, duk abin da za mu iya mun yi don su yi hakuri kar su koma APC saboda hakkinmu da ke kansu, da kuma hakkin jama'ar Kano amma abubuwa sun ci tura," in ji Suleiman Hashin.

Sai dai kuma shugaban jam'iyyar ta NNPP a Kano ya roƙi gwamnan da ya mayar da wuƙarsa kube.

"A madadinmu gaba ki ɗaya, muna sake rokonsu da su yi wa Allah su yi wa Annabi ka da su bar wannan jam'iyyar kar su bar wannan jam'iyya su koma wadda aka yi hamayya da ita kuma talakawa da sauran masu zabe suka ka da ita."

Daga ƙarshe Suleman Hashimu ya tabbatar wa da jama'a cewa shi da wasu jiga-jigan ƴan jam'iyyar da ake ta yaɗa jita-jitar cewa su ne suka haɗa gwamna Abba da Kwankwaso ba gaskiya ba ne.

"Ina son na jawo hankalin masu yadda jita-jita cewa, musamman akwai wasu da suke hada Gwamna da Jagora Sanata Kwankwaso; musamman mataimakin gwamna, da Sanusi Surajo da Hashimu Dungurawa da Sanata Rufai Hanga, ana ganin ana zargin mu saboda ganin kusancinmu da jagora, amma mu ba mu taba hada kowa da jagora ba, amma idan wani yana da shaida sai ya fito da ita, kuma Allah ya ba su hakuri."